Sashe 91
A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.. Yana yin parking Gwani ya sauka daga motar, kusan lokaci ɗaya da Lulu. Suna fita kuwa ya datse ƙofar. Didi ta tura ta tura ta ƙi buɗuwa. Se ta juya ta kalle shi daidai lokacin da ya zuba mata waɗannan idanun nasa. Ya kashe mata ido guda ɗaya yana cije gefen lips ɗinsa na ƙasa. Kawai se ta juya tana bin Lulu da ta yi gaba da kallo, zuciyarta kamar za ta buga dan takaici. Sun fi minti 2 a haka ba tare da kowannensu yace komai ba. Jikinta a sanyaye ta juya ta kalle shi kamar za ta fashe da kuka tace
"Don Allah ka buɗe min.." Se a lokacin sannan ya ɗan yamutsa fuska yace
"Fita za ki yi?" Da sauri ta jinjina kai tana fatan ya buɗe matan ta fita. Numfashi ya sauke sannan ya soma faɗin
"Ohk.. Idan ki na so na buɗe miki se kin yadda daga nan babu inda inda za ki wuce se kitchen ki dafa min Coffee. Daga haka se ki tafi sashen Mommahn. Idan kuma ba haka ba mu kwana cikin motar nan." Ya ƙare yana ɗaga hannunsa. Shiru ta yi tana kallansa bayan ta gama jin bayaninsa. Fisabillahi kwana nawa ne ba ta kai masa Coffee ɗin ba? Ba se ya bari ta huta ba. Wai ma shi duk me ye ya chanja shi haka ne?
"Toh ai ba a sashen nake ba.." Ta faɗa kamar za ta yi kuka. Tsayawa ya yi yana kallanta yanda ta yi ɗin nan ba ƙaramin kyau ta masa ba. Karo na farko ya cigaba da biyewa zuciyarsa da ke tunzura shi ya yi ta shigewa yarinyar, se kuma daga baya ya zo yana tuhumar kansa. Kai a yanzu ma fa kwana 2n nan da suka yi ba ya ganinta sosai se yake jin wani abu ne kama da kewa na kama shi. Haka nan yake tsintar kansa da son ganinta, abu se ka ce asiri.
"Oh.. ya yi. Da ma ban miki dole ba ai.. Gyara zama ki shirya kwana cikin motar nan." Ya ƙarasa maganar yana kwantar da kujerar da yake kai. Da sauri tace
"A'ah zan kawo maka." Buɗe idanunsa da ya fara rufewa ya yi yace yana ƙunshe dariyarsa.
"Oh kin amince?" Se ta jinjina kai tana ɗauke kai. Ɗaga kafaɗa ya yi kamar irin be damun nan ba, ya yin da yana saka hannu ya buɗe ƙofar ya saki wani miskilin murmushi yana sake cije lips ɗinsa. Kamar ta fasa ihu haka take ji, haka ta bi bayansa zuwa sashen nasu da yanzu ba a ciki suke zaune shi da Gwani ba. Sun koma ainahin sashen Bad Man. Kai tsaye hanyar kitchen ta yi dan yin sauri ta gama abin da za ta yi. Ya yi saurin riƙo hannunta yana faɗin
"Saurin na meye ne? Mu je na nuna miki wani abu." Ya yi maganar ba tare da ya bata damar musu ko ƙwace hannunta ba. A haka suka ƙarasa ɗakin.
"Mu je mana.." Ya yi maganar irin ransa a ɗan haɗe ɗin nan dan kar ma ta kawo wani abun a ranta.
"Yau da rashin kirki ya tashi kenan." Ta faɗa ƙasa ƙasa tana shiga cikin ɗakin. Kusan a tare suka shiga, se dai shi ya dakata yana shiga ya saka key a jikin ƙofar sannan ya jefa cikin aljihun wandonsa. Da sauri ta juyo ta kalle shi, kamar za ta yi kuka tace
"Ka ce fa Coffee zan kawo maka.. Kar Mommah ta neme ni."
"Se me? Ki na wajen mijinki." Ya yi maganar cikin basarwa yana ƙarasawa cikin ɗakin. Binsa ta yi da kallo ta girgiza kai tace
"Ni dai don Allah.."
"Shhhh...." Ya faɗa bayan ya ɗora hannunsa a kan bakinsa. Ya juya ya ƙarasa cikin ɗakin. Kai tsaye soma rage kayan jikinsa ya yi kamar wanda ke shirin yin wanka. Lura da ko damuwa da wanzuwarta a wajen be yi ba, dan kuwa cigaba ya yi da ƙoƙarin cire kayan shi ya sanyata saurin juyawa ƙirjinta na dukan uku uku. Ya sake yin wata miskilar dariya ƙasa ƙasa yana ƙarasa abin da yake yi. Toilet ya faɗa ya watsa ruwa, ya fito. Rigar bacci ya saka, irin me buɗaɗɗen gaban nan. Se ya saka igiyar rigar ya ɗaureta kafin ya feshe jikinsa da turarukansa masu mugun daɗin shaƙa. Har lokacin tana tsaye ta rasa abin yi. Tun bayan shigarsa wankan da ta duba mukullin ba ta gani ba. Se ta sake tsayawa tana jiran fitowarsa dan ta sake roƙarsa. Ta buɗe baki da niyyar yin magana yace
"Ki kwantar da hankalinki.. Ki zo ki kwanta kawai.. Yau a nan za ki kwana." Ya faɗa lokacin da ya soma takowa zuwa inda take. Girgiza kai ta yi daidai lokacin da ƙwalla ta taru a idanunta tace
"Don Allah kar ka min haka.. ka bar ni na tafi ka ji?"
"Na ƙi." Ya yi maganar lokacin da ya iso dab da ita. Hannu ya ɗora a kan hijab ɗinta daidai lokacin da ta soma ja baya lokaci ɗaya kuma tana danne hijab ɗin jikinta.
"Ki yi shirin kwanciya.. Ko ki cire wannan hijabin ko ni na cire." Ya yi maganar yana kafeta da idanunsa.
"Don Allah.." Ta faɗa tana girgiza kai.
"Ba ki yadda ba kenan?" Ya yi maganar yana sake matsawa kusa da ita da niyyar saka hannu ya cire mata hijabin. Se ta yi saurin saka nata hannun ta soma yaye hijabin. Ya yi dariya ƙasa ƙasa, tabbas wannan tsoron nata na ɗaya daga cikin abubuwan da ke burge shi a tattare da ita. Kamar ba za ta cire ba, se dai ta runtse idanunta kawai ta cire. Ya karɓa yana jefa shi gefe.
"Je ki kwanta.." Ya yi maganar yana nuna mata kan gado. Ganin alamar za ta sake yin magana ne ya sanya shi katseta da faɗin
"Kar ki min musu." Se ta haɗiye maganar ta ƙarasa kan gadon kawai ta kwanta. Ta runtse idanunta tana curewa waje ɗaya kamar kayan wanki. Ji take kamar ta fashe da kuka, ko kuma ta yi ihu ko ze fahimceta tun da dai ya ƙi jin roƙon da take masa. Ya ɗan shafa sumar kansa yana sauke ajiyar zuciya. Bayan shuɗewar wasu mintuna se ya ƙarasa kan gadon ya zauna. Yana lura da yanda take sake jan bargo tana rufe jikinta. Ya yi ƙwafa yana murmushi. Ya kai wajen minti 5 da zama ba tare da ya yi yunƙurin yin komai ba kafin a hankali ya kai hannunsa ya yaye bargon gaba ɗaya. Abin da ya ba shi mamaki shi ne har ta fara baccinta cikin kwanciyar hankali. Ya yi murmushi lokaci ɗaya yana lumshe idanunsa sanda zuciyarsa ta ɗan buga kaɗan. Be ɓata lokaci ba wajen maidata cikin jikinsa ya kwantar a kan ƙirjinsa da ke a buɗe. Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da bugun zuciyarsa ya ƙaru. A hankali ya kai hannunsa kan hular da ke kanta ya zameta. Nan take dogon baƙin gashinta da ke tufke da ribbom ta bayyana, babu abin da take se sheƙi da wani daddaɗan ƙamshi. Ƙamshin da ya tilasta masa lumshe idanunsa. Se ya shagala da son cigaba da shaƙar ƙamshin, dan haka ya ɗora hancinsa kan gashin nata yana shaƙar ƙamshin da ke fitowa daga jikinsa. Sake rungumeta ya yi sosai tamkar wanda za a ƙwacewa ita. Cikin bacci ta ji ta kamar ba a kwance ba, hakan ne ya sanyata soma ƙoƙarin buɗe idanunta da sauri. Se ta ji ta ƙam ƙam a jikinsa, yana kuma cigaba da shaƙar ƙamshin da ke fita daga kanta. Ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske, ba ta san lokacin da ta buɗe baki a tsorace ta saki ƙara ba, dan ba ma ta fahimci a inda take ba. Cikin sakannin da ba su wuce 3 ba, ya yi amfani da bakinsa wajen lalubo nata ya haɗe su waje guda. Se a lokacin ta fahimci lallai shi ne, shi ɗin ne dai yau ma ya maimaita abin da ya yi rannan. Cikin lokaci ƙanƙani wata irin kasala ta rufe shi, bugun zuciyarsa ya ƙaru fiye da na ɗazu. Be san yanda aka yi ba, ba kuma ta tsammata ba, bayan ƙoƙarin ƙwace bakinta da ta yi daga cikin nasa, se salon nasa ya chanja ma gaba ɗaya. Cikin ƙanƙanin lokaci wani irin tsoro ya ziyarci Didi. Da dai ta ga duk ƙoƙarin da take a banza kawai se ta cigaba da kukanta cike da tsoro. Ƙarar da wayar Bad Man ta yi ita ce ta dawo da shi hayyacinsa. Ya ja Didin ya rungume cikin jikinsa yana komawa gefe har lokacin bugun zuciyarsa be saitu ba. Ya lumshe idanunsa kafin ya buɗe yana mamakin wanda ya kira shi a wannan lokacin. Hannunsa ya kai ya ɗauki wayar ya duba me kiran.
"Mommah!" Ya faɗa da kasalalliyar muryarsa. Dab da za ta tsinke ya ɗaga yana maida dubansa kan Didi da jikinta ke rawa tana kuma so ta miƙe daga jikinsa. Se dai duk da yanda jikinta ke rawa hakan be hanata sake ƙoƙarin miƙewa ba, dan gani take kamar idan ya ajje wayar ze dawo ne ya ƙarasa abin da ya yi niyya.
"Ka na ina?" Mommah ta tambaya muryarta babu wasa, dan tabbas so take ta tabbatar da Areef ɗin yana son Didin sosai kafin ta ba shi ita gaba ɗaya. Kamar yanda ya garasu a farkon auren haka take so shi ma ta wana shi, ta saita shi, ta yanda ze fahimci ba komai kake samu a lokacin da kake so ba. Duk da yanda ta lura yanzun akwai soyayyar Didi cikin idanun Areef ɗin amma so take bayan wannan kuma su yi amfani da hakan wajen ceto shi daga mummunar ɗabi'ar shaye shaye da yake. Har yanzu kuma ba ta yi wa Daddy magana a kan masu tsaron Areef lokacin da yana ƙasar waje ba. Dan so take idan Allah Ya yadda komai ya daidaita se ta sanar da shi dan ka da hankalinsa ya tashi. Se da ya ɗan lumshe idanunsa sannan ya buɗe yace muryarsa a cunkushe
"Ina gida.."
"Ina Afrah?" Ta tambaya kai tsaye. Se da ya fara kallan Didi da ya sake rungumowa sannan yace kamar me magana shi ɗaya.