← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 122

Sashe 106

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

... A ɓangaren Bad Man kuwa hannunsa ɗauke da wani ƙaramin towel da ke ɗore a kan jiƙaƙƙiyar sumar kansa ya fito, sanye da boxer. Gaba ɗaya gargasar da ke kwance a jikinsa dukka a jiƙe suke se ka ce wanda ya bar ruwan da kansa dan jin daɗi kawai. Kai tsaye wajen mudubi ya wuce dan gyara kansa. Ƙamshin da ya soma shiga cikin hancinsa shi ne ya sanya shi zame towel ɗin da ke kansa ya ɗaga kai ya kalli cikin ɗakin. A kan gadon ya hangeta zaune ita ma kamar Lulu cikin wannan atamfar da mayafi. Lumshe idanunsa ya yi yana ɗan murmushi, wato be san abin nasa har ya kai haka ba, kenan har ta fara masa gizo? Ya tambayi kansa. Kamar ze share se kuma ya ajje towel ɗin gefen mudubin ya shiga takowa zuwa kan gadon. Takunsa da ta ji shi ne ya sanyata yin firgigit ta dawo daga tunanin da ta tafi. Daidai lokacin da ya ƙaraso ta ɗaga dara daran brown eyes ɗinta ta kalle shi. Se suka faɗa cikin nasa kyawawan matsakaitan idanun. Ita janye nata ta yi da sauri tana gyara zamanta a kan gadon. Ba ta ankara ba se jin motsinsa ta yi a gabanta durƙushe. Ɗaga idanu ta yi da niyyar kallan fuskarsa se idanunta suka sauka a ƙaƙƙarfan jikinsa da babu riga, se wannan baƙar gargasar da ta cika ƙirjinsa da kuma hannayensa. Farar ƙafarsa kawai ake iya gani saboda durƙuson da ya yi. Se inda ke a buɗe daga wajen ƙafarsa ya haɗe da jikinsa da babu riga. Cikin matuƙar tsoro da firgici zuciyarta ta buga. Kenan tumɓur yake? Ta tambayi kanta dan ita dai ba ta ga alamar akwai kaya a jikinsa ba. Ba ta yi aune ba se jin hannunsa ta yi kan hannunta. Ai ba ta san lokacin da ta yi wani tsalle ba tana sakin ƙara a gigice lokaci ɗaya tana runtse idanunta cike da tsoro. Cike da tabbatarwa da kansa lallai da gaske ita ɗin ce ba gizo take masa ba, tare kuma da mamakin abin da ya tsoratata ya miƙe da sauri ya yi amfani da hannunsa wajen riƙota ya dawo da ita baya. Sake runtse idanunta ta yi tana cigaba da ihunta jikinta na wani irin karkarwa lokaci ɗaya kuma tana ƙoƙarin fuzge hannunta. Ganin dai ta ƙi nutsuwa ne ya sanya shi janta da ƙarfi kawai ya haɗe bakinsu waje ɗaya. Abin da ya dakatar da ƙarar da ke fita daga sanyayyiyar muryarta kenan. Hakan ne kuma ya ba su damar zubewa a kan gadon har lokacin yana riƙe da ita a hannunsa, bakinta kuma na cikin nasa..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO79*

___ Ya ɗauki wajen minti 1 yana kissing lips nata kafin a hankali ya sake shi yana shafa jiƙaƙƙiyar sumar kansa lokaci ɗaya yana lumshe idanunsa. Wato duk sanda ya sumbaceta jinsa yake wani daban, wani irin taushi ne da bakin kamar wadda ke amfani da wani abun da ze sanya shi laushi. Da hannunsa ya sake yin amfani wajen riƙo fuskarta yana ɗagota dan ta kalle shi, lokaci ɗaya yana furta

"Me ya faru?" Ya faɗa yana jin yanda har lokacin jikinta ke rawa, ta kuma ƙi buɗe idanunta da ta runtse sosai. Kawai se ya jata ya mannata a ƙirjinsa cike da mamaki. Sosai bugun numfashinta ya cigaba da fita da sauri da sauri. Hakan ne ya sanya shi sake yi mata kyakykyawar runguma cike da fatan hakan ya dawo mata da nutsuwarta, ta kuma sanar da shi abin da ya faru. Shiru yanzun ma ba tace komai ba. Se ya yi shiru be sake cewa komai ba yana jin yanda take cigaba da sauke numfashi. A hankali kuma se bugun zuciyarta ya soma saituwa. Se a lokacin ne ta ɗan soma buɗe idanunta. Ta sauke ajiyar zuciya lokacin da ta lura da boxer ɗin da ke jikinsa, lokaci ɗaya tana taune laɓɓanta na ƙasa cikin baki. Ta lumshe idanunta tana sake sauke ajiyar zuciya. A hankali ya soma ɗago da kanta, ya tsayar da shi a saitin fuskarsa yana kallanta.

"Me ya tsorataki haka?" Ya faɗa yana lalubo ƙwayar idanunta da yake fatan ta shiga cikin tasa. Girgiza kai ta yi ba tare da ta ɗaga kai ta kalle shi ba. Se dai da ta ga babu mafita kawai ta ɗaga idanunta ta kalle shi, dan idan ta cigaba da kallansa se dai ta yi ta kallan jikinsa da ke a buɗe babu riga. Wanda duk ta kwashe danshin da ke jikin nasa a jikinta. Duk da be wani yarda ba, amma kuma tun da ta nutsu hankalinsa ya kwanta. Dan haka se ya zameta daga jikinsa, ya zaunar da ita kan gadon kafin yace a nutse.

"Ina fatan ganinki da na yi yana nufin kin amince kin dawo ɗakinki?" Ya ƙare yana murmushi cike da fatan abin da yake tunani ya kasance haka ɗin ne. Jinjina kai ta yi, dan fatanta ya bar wajen ko ta samu bugun zuciyarta ya koma daidai. Lumshe idanunsa ya yi kafin ya buɗe. Kamar ba ze ce komai ba, se kuma yace

"Kenan hakan na nufin kin amince ki na sona?" Ya tambaya yana kallanta. Se ta girgiza kai idanunta a kan fuskarsa. Wani irin bugawa da zuciyarsa ta yi shi ne ya sanya shi saurin dafe saitinta. Ya ƙurawa Didi idanunsa da suka ƙanƙance. Da muryarsa da ita kanta ta sauya yace

"Ki na nufin ba kya sona?" Ya tambaya cike da tsoro. Irin kallan da ta ga ya mata, da kuma ganin yanda cikin ƙanƙanin lokaci gaba ɗaya ya sauya, idanunsa kansu sun sauya kamar ba nasa ba, ya sanya ba ta san lokacin da ta yi saurin sake girgiza kai ba, daidai lokacin da ƙirjinta ya buga, ta kuma kaucewa idanunsa da ke kanta. Runtse idanunsa ya yi yana jin yanda bugun zuciyarsa ke tsananta. Murmushi ya yi irin murnushin yaƙen nan da ake cewa ya fi kuka ciwo. Ya sake zuba mata idanunsa kafin ya soma faɗin

"Shi kenan.. Zan cigaba da zama da ke har zuwa ƙarshen numfashina. Ko da kuwa ba kya sona tun da har kin amince za ki cigaba da zama da ni, kuma ni ina sonki." Wallahi ba ta san lokacin da ta ɗaga jajayen idanunta da suka cika taff da ƙwalla ta kalle shi ba. Ba ta taɓa tunanin abin da ze fito daga bakinsa ba kenan. Wani irin tausayinsa ya kamata. Se ta kasa ɗauke idanunta daga kansa. Jin ƙwallar na neman saukowa kan fuskarta ne ya sanyata saurin janye idanunta tana saka hannu ta ɗauketa. Se a lokacin sannan Bad Man ya miƙe, duk da yanda zuciyarsa ke cigaba da masa wani irin zafi hakan be hana shi faɗin

"Ki na buƙatar wani abu ne?" I zuwa lokacin barin hawayen ta yi ya sauka a kan kuncinta. Lallai ya yi chanjawar da ba ta taɓa tunani ba. Har ta nuna ba ta son shi a gaban idanunsa amma ya cigaba da nuna mata kulawa?

"Uhmmm?" Ya yi maganar yana ɗan leƙa fuskarta. Saurin saka hannu ta yi ta goge hawayen tana ɗaga kanta. Cikin rashin fahimta yace

"Kuka kike yi? Me ya saka ki kuka?" Ya tambaya cike da fatan ta ba shi amsa. Murmushi ta ƙaƙalo ta wanzar a kan fuskarta. Ta ɗan ja ajiyar zuciya kafin ta soma faɗin

"Ba kuka nake ba.. Ba na kuma buƙatar komai." Ƙura mata idanu ya yi kamar me son gano wani abu daga kan fuskarta. Ya ɗan sauke numfashi kafin yace

"Ban yadda ba.. Ki faɗa min idan wani abu ke damunki.." Sake girgiza kai ta yi cike da fatan ya ƙyale zancen a nan, ba se ya zurfafa bincike ba. Se kuwa ta ji yace

"Shi kenan.. amma idan na sake ganinki ki na kuka toh tabbas se kin sanar da ni abin da ke damunki." Ɗaga kai ta yi ta sake kallansa yau ɗin a karo na barkatai. Wato ko wacce magana ya yi da kalar sinƙin mamakin da ze sanyata ciki. Shi ma tsayawa ya yi yana kallanta, cikin zuciyarsa yana mamakin yanda yau ɗin ba ta jin kunyar kallansa ko kaɗan. Se kuma kunya ta kamata ta yi saurin saukar da idanunta cikin basarwa. Ya ɗan fesar da iska daga bakinsa yana fatan damuwar da yake ji yanzun ta ragu tun da dai yana tare da Didin. Komawa ya yi gaban mudubin, shiryawar da be yi ta a nutse ba kenan, kawai ya saka kaya ya feshe jikinsa da turarukansa masu ƙamshi.

Ganin da ta yi yana gyara gadon ne ya sanya ta miƙewa daga inda take zaune. Ta ƙarasa, ba tare da tace komai ba ta kama tattausan bedsheet ɗin ta shiga gyarawa cike da ƙwarewa. Be lura da tahowarta ba se ganinta kawai ta yi ta soma gyarawar. Se ya miƙe hadda wani sauke numfashi irin wanda ya sha aikin wahalar nan, dan da ma karanbani ne kawai ya sanya shi gyara gadon ba don ya iya ba. Tass tass haka ta gyara gadon. Se a lokacin ta saka hannu ta ɗauki ɗaya daga cikin pillown da ke kan gadon tana shirin wucewa ta jiyo muryarsa yana faɗin

"Ina za ki je?" Dakatawa ta yi tana sake riƙe pillown sosai kamar wanda za a ƙwace.

"Bacci nake ji." Ta faɗa tana ɗan rufe idanunta da ke ɗauke da bacci sosai.

"A ina za ki kwanta ne?" Ya tambaya cike da mamaki yana kallanta. Kujerar da taso daga kanta ta nuna tana ɗan cuno baki. Ya bi kujerar da kallo kafin ya maido da dubansa kanta yana jinjina kai.

"Lallai!" Ya faɗa a kan laɓɓansa. Soma takawa ya yi zuwa inda take. Lura da hakan ya sanyata sake riƙe pillown da kyau. Hannu ya saka ya riƙo pillown. Se ta ɗaga kai da sauri ta kalle shi. Narai narai ta yi da fuska ganin da gaske karɓa ze yi. Tace kamar za ta yi kuka

"Don Allah kwanciya fa zan yi." Be ce komai ba ya karɓe pillown, dan ya fahimci manufarta. Ajje pillown ya yi kan gadon kafin ya dawo da dubansa kanta yace

"Za ki kwanta kan gadon ne ko na kai ki da kaina?" Kallan gadon ta yi kafin ta ɗauke kai tace
Chapter 106 · 0% Book details