← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 122

Sashe 55

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Har yanzu?" Ta sake tambaya tana cigaba da kallansa. Se kawai ya sauke ajiyar zuciya, jin da ya yi babu hanyar fita. A hankali yace

"Ba ta jin daɗi ne shi ya sa ba ta fito ba tun ɗazun."

"Subhanallahi.. Haba Affan.. Yanzu ɗiyar tawa ba ta da lafiyar da har ta hanata fitowa shi ne ba ka faɗa min ba ina nan a zaune. Bari na duba gaskiya idan zazzaɓin ne se dai mu sake zuwa asibiti." Ta faɗa lokacin da ta gama miƙewa a kan ƙafafunta.

"Ummeey ai tana samun sauƙi ma.." Gwani ya faɗa dan gudun ka da Ummeeyn tace za ta dubata. Duk da ba ta taɓa shiga ɗakin ba tun bayan aurensu. Amma a yanda ta damu da Lulun ya san sarai za ta iya shiga ɗakin.

Tun da aka yi bikinsu Gwanin Ummeey za ta iya cewa ba ta sake shiga ɗakin ba se yau ɗin. A nutse ta yaye labulen ɗakin ta shiga. Gwani kam kasa motsawa ya yi daga inda yake. Se cigaba da tsayawa da ya yi a wajen kamar wanda aka dasa.

Yanda ta ganota lulluɓe cikin bargo ya sanyata sake fahimtar da gasken zazzaɓin ne ya sake rufeta. Dan haka da sauri ta ƙarasa tana faɗin

"Afaaf.." Ƙirjinta ne ya buga lokacin da ta ji kamar muryar Ummeey cikin ɗakin. Sake maimaita sunanta da Ummeyn ta yi ne ya sanyata sake tabbatar da lallai Ummeeyn ce. Hannu Ummeey ta saka ta ɗan ɗage bargon ta wajen fuskarta. Hakan ya bata damar ganin idanunta da suke a kumbure.

"Ya salaam.. Sannu.." Ta faɗa cikin tausayawa. Ba ta iya buɗe baki tace komai ba saboda yanda dabara ta ƙare mata. Ta kasa buɗe idanunta dan ba ta san da wanne ido za ta kalli Ummeeyn ba. Saboda ji take kamar ko ba ta faɗa mata ba tana kallan idanunta za ta fahimci abin da ya faru. Lura da idanunta biyu ya sanya Ummeey matsawa kusa da ita ta yi amfani da hannunta wajen ɗagota.

"Ai ba a zauna a gida haka ba lafiya ba." Ummeey ta faɗa tana ƙarasa ɗago Lulu da ta kaasa ko yunƙuri ballantana ta ƙwaci kanta. Zuwa lokacin gaba ɗaya jikinta ya gama yin mugun tsami. Dan haka ba ta san lokacin da ta saki ƙaramar ƙara ba lokacin da Ummeeyn ta ida zaunar da ita a kan gadon. Ba tare da Ummeey ta fahimci wani abun ba tace

"Daure ki tashi ki shirya mu je asibiti.. Ai ba a zauna haka ba." Ta ƙare tana sake taimaka mata dan ta miƙe. Se dai zuwa lokacin ta ɗan tsaya tana karantar Lulun. Sam ta rasa me za tace. Ta kasa buɗe baki tacewa Ummeeyn ta barta lafiyarta ƙalau. Se a lokacin sannan ta buɗe idanunta, se dai har lokacin ta gaza furta komai. Ta kuma kasa ɗaga ido ta kalli Ummeeyn. Taimaka mata Ummeey ta yi suka soma tafiya dan ita a niyyarta a maidata asibiti su ƙara dubata. Lokaci ɗaya kuma tana sake karantar Lulun. Se dai ko tafiyar second 10 ba su yi ba Ummeey ta dakata. Ta ɗan sauke ajiyar zuciya sannan ta komar da Lulun ta zaunar da ita a kan gadon. Idanun Lulu a runtse suke gaba ɗaya tun lokacin da suka fara tafiya. Har kuma yanzun ba ta buɗe su ba. Ba tare da Ummeey tace komai ba ta fita daga ɗakin. A inda ta bar Gwani a nan ta same shi. Ba tare da ta kalle shi ba tace

"Juyo min ruwan zafin da ke kan wuta ka kawo min.." Daga haka ta juya ciki. Be fahimci ta gane abin da ya faru ba ne. Dan haka kai tsaye wajen wutar ya nufa kamar yanda ta umarta ya juyo cikin bokiti ya kai mata har cikin banɗaki. Be jira wani abu ba ya fice daga ɗakin. Se da ta shiga banɗakin ta haɗa ruwa sannan ta fito. A nutse ta kalli Lulu tace

"Maza tashi ki je ga ruwa can na haɗa miki ki yi tsuguno ciki.. Idan ya huce akwai wani a gefe se ki chanja da shi sannan ki yi wanka In Sha Allah za ki ji daɗin jikinki.." Ɗaga idanunta Lulu ta yi ta saci kallan Ummeeyn. Ƙirjinta ya buga da ƙarfi. Kar dai ta san abin da ya faru. Ita kam idan haka ne ta shiga 3 ta lalace.

"Tashi kin ji?" Ummeey ta katse mata tunanin da faɗin hakan. Wai duk dan idan Ummeeyn ba ta fahimci komai ba kar ta gane. Hakan ne ya sanyata aro duk wani jarumta ta miƙe cike da ƙarfin hali ta wuce banɗakin. Ummeey ta yi murmushi lokacin da Lulun ta shige banɗakin a fili ta furta

"Allah sarki!!" Daga haka ta cigaba da zama cikin ɗakin.

Kamar yanda Ummeey ta umarceta hakan kuwa ta yi. Cikin ƙanƙanin lokaci ta ji jikinta ya yi mata daɗi kamar ba shi ne ɗazun take jinsa kamar ba nata ba. Ta ɗauki mintuna masu yawa a ciki kafin ta fito sanye da hijab ɗinta. Har lokacin kanta na ƙasa ta ƙarasa ta zauna a kan gadon. Riga Ummeey ta miƙa mata mara nauyi tace

"Saka wannan se ki kwanta ki samu ki yi bacci.." Ji take kamar ta ɗora mata da bayani a kai, se dai ko babu komai ita ɗin sirikarta ce. Kuma a yanda take ta sum sum da kai ta san ba ta so kowa ya san abin da ya faru. Dan haka ita ma Ummeeyn se ta basar kawai cikin hikima dai ta cigaba da yi mata magana.

"Ya kike jin jikin naki?" Ummeey ta tambaya dan ita har zuwa yanzun tana ɗaukar Lulun ne a matsayin ɗiyarta. Wata irin kunya da takaici su ne suka taru suka mata dirar mikiya. Ta kasa ko da ɗaga ido ne ta kalli Ummeeyn. Idanunta na kawo ƙwalla tace a sanyaye

"Alhamdulillah.."

"Toh madallah.. ki cigaba da yanda na faɗa miki har zuwa lokacin da jikinki ze koma daidai." Sam Ummeey ba ta damu da yanda Lulun ke cigaba da ƙunshe kai ba kamar ba ita ba. Ta cigaba da mata magana cikin hikima. Ba Ummeey ce ta bar ɗakin ba se da ta tabbatar Lulun ta kwanta har ta soma bacci sannan ta fito. A ƙofar ɗakinta ta samu Gwani. Tana neman waje za ta zauna tace

"Ka samu ka siyo mata wani abun da za ta ci idan ta tashi.. Yau ɗin wainar gero zan yi. Na kuma san ba lallai ta mata daɗi ba."

"Toh Ummeey.." Ya ƙare yana miƙewa. So yake ya tambayi Ummeeyn se dai yau ɗin wata irin kunyarta yake ji kamar wata sirikarsa. Se dai ya maaze kawai yace

"Ba sai an je asibitin ba Ummeey?"

"Ehh ba se an je ba.." Ummeey ta ba shi amsa ita ma ba tare da ta kalle shi ba, saboda yanda ta ga yau ɗin yana ta wani mammazewa, yana ƙin kallanta idan ze yi magana kamar ba shi ba. Ita dariya ma yake bata. Se dai kawai ta riƙe abarta. Be sake cewa komai ba ya fice daga gidan.

... Ƙarasowa Baba Atine ta yi cikin ɗakin hannunta ɗauke da waya. Ta zauna a kan wani ƙaramin tuntu dake ƙasan gadon tace

"Barka da wannan lokaci Rankiyadaɗe.."

"Kai Baba.. na ce miki ba na so." Didi ta faɗa tana tura baki.

"To ya za a yi.. Se dai ki yi haƙuri 'yata.. ko ban faɗa ba wani lokacin ki bar ni na faɗa wani lokacin ko dan kar na dinga manta matsayinki.." Ita dai sam Didi ba ta san irin wannan zancen. Dan haka dan ta kawar da zancen ya sanyata faɗin

"Ina Mommah?"

"Kin ga ma yanzu ita ce ta aiko ni.. Tace ki kira Ummanki ku gaisa." Wani irin farin ciki ne ya ziyarci Didi jin abin da Baba Atinen ta faɗa. Cikin farin cikin da ya bayyana har cikin muryarta tace

"Toh Baba.." Miƙa mata wayar Baba Atine ta yi tana jin daɗin yanda ta ga tana murmushi. Dan babu ƙarya tana so ta ga Didin ta yi farin ciki ta sanadiyyarta. Karɓar wayar ta yi ta loda number Ammi. Cikin ƙanƙanin lokaci se ga number ta fito an yi saving nata da 'Ammin Afrah' Babu ɓata lokaci ta kira number tana karawa a kunnenta. Cike da kewar juna kamar ko yaushe suka shiga gaisawa bayan Ammi ta ɗaga wayar. Kamar ko yaushe se suka shiga hirar yaushe gamo. Cikin haka ne Didi tace

"Ammi makaranta fa?" ta faɗa a sanyaye dan tabbas tana kewar makarantar. Dan za ta iya cewa bayan kewar er uwatta ɗan uwanta da kuma iyayenta kewar makarantar ce za ta biyo baya.

"Ki kwantar da hankalinki.. yanzu kam dai babu zancen makaranta Didi.. Zuwa gaba dai idan Allah ya yi za ku cigaba se ki ga da kansu su mazajen naku sun sama muku makarantar kun cigaba." A sanyaye tace

"To Ammi.."

"Ina Little..?" Didi ta tambaya cike da kewarsa.

"Sun fita da Abbanku. Ina so ma a kawo shi wajenki ya ganki kafin mu je ganin Gwaggo.."

"Kai Ammi barin garin za ki yi?"

"Ki ji min ja'ira.. Aou kar na je ganin Gwaggon?" Tura baki Didi ta yi tace

"A'ah Ammi.. Amma don Allah kar ki tafi da Little.. A kawo min shi nan ya kwana har zuwa lokacin da za ki dawo. Don Allah Ammi kar ki ce a'ah.." Shiru Ammi ta yi bayan ta gama jin abin da Didin ta faɗa. Tabbas ta san daga Didin har Little sun yi kewar junansu. Dan kuwa tun bikin ba su sake ganin junansu ba. Ga shi kuma ya je wajen Lulu ya kwana, ko babu komai ita ma idan ya je wajenta ya kwana za ta ji daɗi. Dan haka Ammi ta amsa da

"Shi kenan.. In Sha Allah ze zo.."

MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO54*

Not edited..
Chapter 55 · 0% Book details