← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 122

Sashe 103

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni ma ban sani ba." Ta ƙare tana goge ƙwallar da ta soma sauka a kan fuskarta. Runtse idanunsa ya yi, har ga Allah ba ya son kukan nan ko kaɗan. Duk se yanzu ze rasa nutsuwarsa. Ba ya son ya ganta cikin damuwa, musamman ma kuma a irin yanayin nan da ya kasance ba ita ɗaya ba ce. Gaba ɗaya manta a inda suke ya yi dan kukan nata duk ya ruɗa shi. Ya saka hannunsa da sauri ya riƙota, janta ya yi cikin jikinsa ya rungume cikin rarrashi yace

"Kar ki yi kukan nan please.." Ya faɗa kamar me raɗa. Sauke ajiyar zuciya ta yi tana ƙoƙarin hana mara dalilin ƙwallar cigaba da zubowa. Daidai lokacin da Iftihal ta shigo. Wani irin turus ta yi ta ja ta tsaya ƙirjinta na bugawa. Ta kasa ko da ƙwaƙwaƙwƙwaran motsi ne. A daidai lokacin Lulu ta lura da tsayuwarta a wajen. Cikin lokaci ƙanƙani fushin da Gwani ya soma samun nasarar sauke shi, Iftihal ta taso da shi. Cikin ƙanƙanin lokaci fuskarta ta sake haɗewa kamar hadarin da ya kusa bada ruwa. Wani killer smile Lulu ta saki kafin a hankali ta ɗaga hannayenta ta zagaya da su jikin Gwani ta rungume shi. Buɗe idanunsa ya yi cike da mamakin abin da ya ji Lulun ta yi. Da gaske ita ɗin ce? Da gaske hakan ne ke faruwa? Be ida tunanin ba se ji ya yi ta sake rungume shi sosai kamar wadda za a ƙwacewa shi hadda wani komawa ta lafe a jikinsa tana lumshe idanunta. Duk da yanda kalmar da take haɗawa cikin ƙwaƙwalwarta zuciyarta na hanata. Tana kuma daƙirewa tana ji kamar ba za ta iya fitowa daga bakinta ba. Hakan be hanata yin watsi da komai ba, ta aro wata irin jarumta a hankali ta furta

"Ina..son..ka." Ta yi maganar a rarrabe, yanda ta san dole ko da bakinta kake kalla ka san abin da ta faɗa. Kafin ya gama dawowa daga wancan shock ɗin se ga wanda ya fi kowanne. Wanda ya sanya ya soma ƙaryata duk abin da ya faru ɗazu. Ya soma tunanin lallai ire-iren mafarkan da yake yi ne yau ma yake sake yin kalarsu. Se dai ya rasa dalilin da ya sanya wannan ɗin ya fita daban. Yake ji kamar gasken ne. Wata irin ƙara da Iftihal ta saki tana fashewa da kuka ita ce ta dawo da shi hayyacinsa. Abin da kuma ya tabbatar masa da lallai ba mafarki yake yi ba. A hankali ya shiga sassauta riƙon da shi da ita suka yi wa juna. Se dai me? Se ji ya yi ta sake riƙe shi gam. Yau kam mamaki ya kusa kashe Gwani. Se dai farin cikin da yake ciki Allah kaɗai ya san yawansa. Ta gabansu Iftihal ta zo ta wuce cikin ɗakin Mommah a zuciye tana cigaba da ƙaramin kukanta. Be iya ganin fuskar wace ce ba. Se kawai ya basar ya maida dubansa kan Lulu ya shiga lalubo fuskarta da har lokacin take kwance a jikinsa. A daidai lokacin Lulu ta sake shi, se ta shiga ƙoƙarin miƙewa daga jikin nasa. Tana idawa kuwa ya yi caraf ya riƙo hannunta. Kasa ɗaga ido ta yi ta kalle shi dan tabbas wannan kalmar da ta faɗa ta mata nauyi. Ba ta san za ta iya faɗinta a irin wannan lokacin ba, se sanda ta ga Iftihal a gabanta. Ba ta san zuciyarta za ta bata haɗin kai har ta furta ba se da ta soma faɗa. Ta kuma kasa dakatawa, kowacce gaɓa ta jikinta kuma ta yi na'am da hakan. Wani irin murmushin farin ciki ke tashi a kyakkyawar fuskar Gwani. Ya ma rasa me ze ce? Me ze yi? Shin da gaske ne abin da ta faɗa? Ashe kenan da gaske kishinsa ya gani cikin idanunta ranar nan? Da gaske ta fara sonsa ɗin kamar yanda ta faɗa? Cikin ƙarfin hali ya tattara wannan maganar..

"Da gaske ki na sona Afaaf..?" Ya tambaya cike da fatan amsar da za ta fito daga cikin bakinta ta kasance daidai da abin da ta faɗa ɗin. Maimakon ta ji tana son ƙaryatawa ko da ba za ta iya faɗa masa kai tsaye ba. Se ba ta ji hakan ba. Se kasa ɗaga ido da ta yi ta kalle shi. Ta kalli hannunta da ke cikin nasa tana ji kamar ta janye kama yanda ta saba, se ta kasa hakan. Se dai kuma da gasken so take ya saketa ko ta samu ta guje masa, ballantana ta cigaba da tuna abin da ya faru a wajen nan.

"Ki faɗa min don Allah.." A karo na biyu ya sake faɗar hakan. Ba za ta iya kallansa tace da gasken take ba, ba kuma za ta iya cewa ba da gaske take ba. Dan haka kawai se ta zame hannunta da sauri cikin azama ta shige cikin ɗakin Mommah. Binta ya yi da kallo yana sake jin wata nutsuwa da farin ciki na kama shi. Lallai idan dai har hakan ta tabbata babu abin da ze yi se dai ya godewa Allah. Lumshe idanunsa ya yi yana ɗora hannunsa a kan sumar kansa da ke a buɗe ya shafa, har lokacin murmushi ya ƙi barin fuskarsa. Ya fi minti 3 a wajen kafin ya ja ƙafafunsa ya wuce sashensu.

.. Hannunta ɗauke da akwati ta fito daga cikin ɗakin idanunta sun yi jajir alamar ta sha kuka ta ƙoshi. Da sauri Mommah ta ƙarasa tana faɗin

"Subhanallahi Ifti me ya faru?" Ta yi maganar tana riƙo akwatin. Ɗauke kai Iftihal ta yi tace

"Gida zan tafi.." Da mamaki Mommah tace

"Gida kuma?"

"Ehh.." Ta bata amsa tana sake riƙo akwatinta. Girgiza kai Mommah ta yi kafin tace

"A'ah me ya faru? Ba se gobe za mu wuce gidan gaba ɗaya ba?" Da sauri Iftihal ta girgiza kai tana faɗin

"A'ah Mommah yau zan tafi.. Don Allah yau zan tafi." Ta faɗa tana ji kamar ta yi kuka, dan ita kaɗai ta san me take ji, ba ze yiwu ta cigaba da zama a cikin gidan nan ba, dan ta ga alama Lulu na da niyyar tarwatsa mata zuciya..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO78*

___Kallanta sosai Mommah ta yi kafin tace

"Ko dai wani abun ya faru ne ban sani ba?" Sake girgiza kai ta yi kafin tace

"Ba komai."

"Toh maza koma ki zauna.. kin san dai ba ze yiwu na barki ke ɗaya ki tafi ba."

"Mommah don Allah.."

"Ki koma na ce Iftihal.." Mommah ta katseta da faɗin hakan. Idanunta da suka cika da ƙwalla ta runtse tana juyawa ta koma cikin ɗakin. Mommah ta bi ta da kallo cike da mamakin dalilin da ya sa take so ta tafin.

... Ya kasa dena farin ciki tun da ya fito daga cikin ɗakin. Hatta fuskarsa kaɗai idan ka kalla za ka tabbatar da lallai yana cikin farin ciki. A haka ya shiga cikin ɗakin Bad Man ɗin. Baƙon abu ne irin haka a wajen Bad Man, ya ga fuskar Gwanin ɗauke da annuri babu wani dalili. Ya riga ya saba ganin fuskarsan nan mara annuri wadda take a haka kusan ko yaushe, kasancewar hakan a halittarsa ne. Dan haka a mamakance yace

"Bro me ya faru ne? Na ga kamar ka na cikin farin ciki." Se a lokacin Gwani ya saki murmushi. Ya juyo gaba ɗaya yana kallan Bad Man yace

"Tabbas yau ina cikin farin ciki.. Afaaf ta furta tana sona.."

"Woww!! Amma na tayaka murna ɗan uwa."

"Na gode." In ji Gwani. Hannu Gwani ya ɗora a kan kafaɗar Bad Man yace a nutse

"Ka kwantar da hankalinka in Sha Allah wannan ranar na nan zuwa. Ka cigaba da addu'a, ka kuma cigaba da kulawa da ita. Gefe guda kuma ka cigaba da istigfari." Ya fahimci abin da yake nufi, hakan ne ya sanya shi ɗan yin murmushin yaƙe kafin ya jinjina kai yana ajje numfashi.

.. Washegari kamar yanda Mommah ta alƙawarta, gaba ɗaya suka shirya zuwa gidan Sarki (Baba Abdullahi). Gaba ɗaya suka tafi har da Lulu da Didi. Baƙin ciki da ɓacin rai kamar su kashe Iftihal, saboda ganin har da Lulu a tafiyar. Abin da ta yi jiya tabbas ya matuƙar tsaya mata. Har yanzu take jin kamar shakka shakkar kallan inda Gwani yake. Se dai duk da haka ta maze tana ɗan satar kallansa. Ita gaba ɗaya zama gidan ma be mata amfani ba. Tun da dama ta zauna ne dan ta samu ko da shaƙuwa ce ta shiga tsakaninta da Gwanin. Se dai ba ta ga alamar hakan za ta faru ba.

Tarba ta musamman suka samu a gidan Sarkin. Irin tarbar da Mommah da Yaya Amina ba su taɓa tsammata ba. Ranar sun ga en uwa, sun ga dangi. Sun ga waɗanda ba su sani ba. Sun ga kuma waɗanda suka sani. Kowa farin ciki yake da zuwansu cikin gidan. Waɗanda suka san abin da ya faru na sake ɗibewa Samira albarka, ana binta da addu'ar Allah Ya saka musu. Ranar se ta kasance wata ta daban a rayuwarsu. Sun yi farin ciki ainun, haka kuma sun yi kuka. Se dai duk da haka farin cikin ranar ya fi yawa.

.. "Kun ba ni dama, kun amince na maida kowaccenku ɗakin mijinta?" Mommah ta faɗa tana kallansu cike da fatan amsar da za ta fito daga bakinsu ta kasance "Eh" ce. Shiru ne ya wanzu a cikin ɗakin babu wanda yace komai. Zuwa can Didi tace

"Idan dai har kin ga hakan ya dace Mommah ki yi. Duk abin da kika yanke mu masu biyayya ne a kai, saboda mun ɗauke ki ne tamkar Ammi. Dan haka kawai ki ba mu umarni. Dan mun san ba za ki yanke abin da ze cutar da mu ba." Girgiza kai Mommah ta yi tana ji tana sake ƙaunar Didin. Wato hankalin yarinyar na burgeta. Idan ta yi wani abun se ka ɗauka wata babba ce me shekaru. Nan kuwa hankalinta ne ya fi shekarunta yawa.
Chapter 103 · 0% Book details