← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 122

Sashe 87

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba kya buƙatar komai?" Ɗan jim ta yi kafin ta jinjina kai tana ji kamar ta yi ficewarta. Se ta kasa yin hakan, kawai ta cigaba da zama. Idan ta tuhumi kanta dalilinta na yin hakan, se ta kawo uzurin yau ɗin Gwanin abun tausayi ne sosai, shi ya sa ta zauna saboda kuma yace mata ta zauna. Sosai kuma hakan ya taimaka masa, dan babu ƙarya Lulun ta zame masa sanyin idaniya, musamman a yau ɗin da ya sake gasgata hakan. Abu ɗaya ne ya rage, shi ne sauyawar halin Lulun gaba ɗaya, duk da cikin ikon Allah a hankali a hankali take chanjawa, dan yanzu an samu kaso me yawa ya ragu daga cikin halayenta.

A ɗaya ɓangaren kuwa da sallama ta shiga ɗakin ɗauke a bakinta. A Zuciyarta tana fatan Allah ya sa ya yi bacci, ko kuma dai ma kar ta same shi cikin ɗakin gaba ɗaya. Se dai addu'arta ba ta karɓu ba, dan kuwa samunsa ta yi kishingiɗe a kan gadon, ya ɗora kansa a kan hannunsa idanunsa a lumshe kamar me bacci. Se dai ba baccin yake ba, tunanin abubuwan da suka dinga faruwa kamar a mafarki ɗazun yake yi. Ya kasa dena tunanin, duk kuwa da abin da ya sha ɗazun amma har yanzu be manta abin da ya faru ba. Sallamar da ta sake yi ne ya sanya shi buɗe idanunsa da suka fi kama da na wanda ya tashi daga bacci. A hankali ta cigaba da takawa zuwa cikin ɗakin, kai tsaye ta ƙarasa inda ta saba ajewa ta ajiye sannan ta juyo. Kamar ta fice daga ɗakin ba tare da tace masa komai ba, se kuma ta ga rashin dacewar hakan, dan haka cikin siririyar muryarta tace

"Barka da wannan lokaci.." Se a lokacin sannan ya miƙe zaune. Maimakon ya ji kamar a da yana son shareta ko kuma sake mata gargaɗin kar ta sake shigo masa ɗaki, se ya ji yau ɗin ba haka ba ne. Ta wani ɓangaren ma kamar jin daɗin zuwanta ya yi. Ya ɗan sauke numfashi a gajiye sannan yace

"Barka." Ko a iya sautin muyarsa ya isa a fahimci yanayin da yake ciki a halin yanzu. Dan ita kanta Didi se da ta ɗaga kai ta kalle shi saboda yanda ta ji muryarsa ta sauya. Abin da dai ba ta sani shi ne, ko baccin da ya yi ne ya sanya muryarsa sauyawa ko kuma har yanzu a kan al'amarin da ya faru ɗazu ne?.

"Duk da dai ka ce na dena shiga harkarka amma da ka ɗauki Qur'an ka karanta.." Be san dalilin da ya sa yanzu idan ta yi makamanciyar maganar nan yake jin haushin hakan ba. Ya ɗan ja ƙaramin tsaki yana miƙewa tsaye a hankali. Ba ta yi tunanin ma ze tanka mata ba, se jin cunkushashshiyar muryarsa ta yi yace

"Kamar na ce ki bar min wannan maganar koh?" Ya yi maganar yana kafeta da idanunsa. Se ta yi saurin kauda kai tana ɓata fuska. Ƙasa-ƙasa ta furta

"Ai dai gwara na kama kaina.. kafin ka shuka min rashin kirkinka.." Sarai ya ji abin da ta faɗa, dan tun da ta fara maganar yake kallan bakinta dan fahimtar abin da ta faɗa. Ya ja ƙwafa yana cigaba da kallanta, ba tare da ya bari ta ankara ba ya ɗan soma rage tazarar da ke tsakaninsu. Ita dai tun da ta kawo abincin ta kuma gaida shi babu abin da ya rage mata. Dan haka ta ɗaga ƙafa da niyyar takawa dan ficewa daga ɗakin, ba tare da ta lura ba se jin hannunsa ta yi a kan hannunta, kafin ta yi ƙoƙarin yin komai ya jata gaba ɗaya zuwa jikinsa.

"Me kika ce?" Ya faɗa yana kafeta da lumsassun idanunsa. Ba ta san lokacin da jikinta ya kama rawa ba, musamman yanda ba ta yi tsammani ba. Se ta rasa ma abin da za ta ce. Ita burinta ɗaya ya ɗauke waɗannan idanun nasa daga kanta, idanun da suke sakawa ta ji tsoronsa ya kamata.

"Me kika ce..?" Ya faɗa yana riƙe hannunta sosai.

"Ni ba abin da na ce.."

"Kin faɗa.." Ya katseta da faɗin hakan yana sake janta cikin jikinsa. Da sauri ta girgiza kai tuna abin da ya faru rannan. Tsoron kar a sake maimaita abin da ya faru ya sanyata faɗin

"Allah ba da kai nake ba.. Don Allah ka yi haƙuri." Har ga Allah ta ba shi dariya, amma be yi ba ya maaze, ya sake tamke fuska. Yanayin yanda tsoro ya bayyana a kan fuskarta ba ƙaramin kyau ta yi ba. Se ya ji tamkar kar ya saketa, su cigaba da kasancewa a haka.

"Ashe mara kunyar ƙarya ce.." Ya faɗa yana sakinta, dan yau ɗin kusan duk hankalinsa na kan abin da ya faru ne ɗazun. Ba ta jira ta sake cewa komai ba, ko ya ce wani abu ba ta fice daga ɗakin kamar za ta yi tuntuɓe. Sam ba ma ta lura da waye a palour ba, Lulu ta koma ko ba ta koma ba duk ba ta lura ba. Ita dai burinta kawai ta ganta a sashen Mommah.

Komawa ya yi ya zauna a kan gadon, ya lumshe idanunsa tunani barkatai na zuwa masa cikin ƙwaƙwalwa. Se dai waɗanda suka fi tasiri su ne tambayar da ke ta masa yawo cikin kwanya.
"Shin me ke damunsa ne? Me ye ya sa yanzu yake kasa controlling kansa ne idan yarinyar na gabansa? Duk me ye hakan?" Ya tambayi kansa hannunsa cikin kwantacciyar sumar kansa.

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO71*

___Ba ta daɗe da shiga ɗakin ba Lulu ta shigo ɗakin ita ma. Ta bi Didi da kallo tana mamakin yanda ta ganta.

"Ya na ganki kamar a zabure?"

"A zabure kuma?" Didi ta faɗa tana harararta. Se ta yi dariya tana faɗin

"Ehh yasin. Kamar wadda ta wa sarki ƙarya." Dariya ita ma Didin ta yi. Ta saka hannu ta janyo hannun Lulu tace

"Wai ni kam ki na kallan kanki a mudubi kuwa Lulu?"

"Na shiga 3 me na yi?" Lulu ta faɗa tana waro ido waje.

"Dillah kyau kika yi fa.. Kin ga har da ƙiba ma fa duk kin yi wallahi, kamar ba ke ba. Ke idan Ammi ta ganki ma ba za ta gane ki ba." Dariya Lulu ta yi jin ta ƙare zancen nata da barkwanci ya sa ta fahimci da wasa take. Tace

"Didina."

"Lulun Gwani." Buɗe baki Lulu ta yi tana kallan Didin. Se ta fuzge hannunta tana faɗin

"Allah ba na son kalar haka Didi.. Ni ba na so."

"Iyee.." Didi ta faɗa tana kallanta. Ita dai ba ta ga alamar har yanzu Lulun na cigaba da takun saƙa da Gwani ba, ba kuma ta ga alamun tsanar nan tasa da ta yi ba. Se dai abin da ba ta sani ba yanzun ta fara son shi ne ko kuwa a'ah? Se dai ba ta so ta gwada tambayarta kuma ta zo ta ɓaro wani aikin. Shi ya sa ta yi maganar nan ko za ta fahimci wani abun. Ba ta ankara ba se ganin Lulun ta yi ta fice daga ɗakin. Ta bita da kallo tana murmushi.

"A dai juri zuwa rafi.." Daga haka ita ma ta miƙe ta fice daga ɗakin zuwa palour. A nan suka sami Mommah, suka sake gaisawa. Ta kalli Baba Atine da shigowarta kenan tace

"Kin gama komai?"

"Ehh Hajiya.." Maida dubanta kansu Mommah ta yi tace

"Ya kamata ku je ku huta haka nan.. Ta kai muku abinci ku tabbatar kun ci sannan ku kwanta se da safe." A tare suka miƙe, Baba Atine ma ta miƙe dan musu rakiya zuwa ɗakin duk da a cikin palourn Mommahn yake.

"Se da safe Mommah.." Didi ta faɗa.

"Se da safe." Ita ma Lulu ta faɗa a hankali saboda rashin sabo a tsakaninta da Mommahn.

"Allah Ya tashe mu lafiya Yarana.." Ta yi maganar tana murmushi. Kai tsaye bin bayan Baba Atinen suka yi zuwa cikin ɗakin, ya yin da Mommah kuma ta miƙe ta faɗa ɗakinta.

.. Washegari da safe, fitowar Mommah daga cikin ɗakinta kenan suka yi sallama cikin ɗakin. Ta amsa sallamar tana kallan en biyunta da ta kwana tana musu addu'a a kan Allah Ya kare mata su. Se ta ƙaraso cikin ɗakin daidai lokacin da su ma suka ƙaraso. Dukkansu zamewa suka yi suka zauna a ƙasa. Mommah ta yi murmushi daidai lokacin da take amsa barka da safiyar da suka mata.

"Kun tashi lafiya?" Ta tambaya cikin kulawa.

"Alhamdulillah.." Gwani ya amsa da hakan, ya yin da Bad Man ya amsa da

"Ehh Mommah."

"Bari na ɗan amsa waya." Bad Ya faɗa yana miƙewa. Se duk suka bi shi da kallo, Gwani har yanzu ganin abin yake kamar a mafarki. Se kawai ya jinjina kai yana sake kaɗaita Allah a cikin zuciyarsa. Maganar Mommah ita ce ta katse masa tunani lokacin da take faɗin

"Don Allah ka din ga saka min ido sosai a kan Areef.. Ban san waye babba cikinku ba, amma haka nan zuciyata ke ba ni kai ne babba.. Dan haka ga ɗan uwanka nan ina fata za ka taya ni kula da tarbiyyarsa, duk wani abu da za ka gani be dace ba a wajensa ka yi ƙoƙarin hana shi ko tunasar da shi. Kai ne za ku din ga kasancewa tare shi ya sa nake faɗa maka haka." Jinjina kai Gwani ya yi kafin yace

"In Sha Allah Mommah.."

"Ku wuce sashen Daddy.. Za mu taho yanzun." Da "toh" ya amsa yana miƙewa ya fice daga ɗakin. Ta bi shi da kallo wannan farin cikin da ya kasa barinta na cigaba da ratsata. Kafin ta fita se da ta sake tura Baba Atine ta duba mata su Lulu. Nan take shaida mata bacci suke yi, se ta umarceta da ta ƙyale su kawai. Ita kuma ta wuce zuwa sashen Daddyn.
Chapter 87 · 0% Book details