← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 122

Sashe 60

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

___Juyawa ta yi a hankali ta kalli Little da ke ta kalla kallansa. Se kuma ta dawo da kanta kamar za ta sake cewa wani abu se kuma ta kama bakinta. Dan ba ta san yau ɗin me ya taka ba. A nutse ta sake ƙanƙame abin da ke hannunta sannan ta soma takawa. Se kuma ta ɗan dakata saboda yanda ya yi bake bake a bakin ƙofar. Se da ya watsa mata wani kallo sannan ya juya ya koma ciki. Se a lokacin ta taka ta shige ɗin sum sum ta isa inda ta saba ajiye wa a da. Ta ajiye sannan ta juyo dan ficewa daga ɗakin. Se dai har ga Allah tana jin tsoro kar ta je ta sake yin laifi. Dan haka a hankali ta ɗan saci kallansa. Kamar be san da zaman wata halittar cikin ɗakin ba. Dan kuwa cigaba da abin da yake yi ya yi. Daidai lokacin da ta kalle shi ɗin ya ɗaga ido ya watsa mata wani kallo da ya fi kama da na gargaɗi. Se ta yi saurin kauda kanta tana jin bugun zuciyarta na ƙaruwa. Kawai se ta nemi waje ta zauna a sukwane tana ji kamar ta fasa ihu. Ƙwafa shi kam ya yi a ransa yana sake saƙa yanda ze barta ta cigaba da zama cikin ɗakin har zuwa wani lokaci. Ko ba komai ya san ba za ta sake rashin kirkin da ta tsiro da shi ba. Se da ya ida ɓalle maɓallan rigar gaba ɗaya ya zamana tana jikinsa ne be kai ga cireta ba sannan ya nemi waje ya zauna. Hannu ya kai ya ɗauki coffee ɗin ba tare da ya kalleta ba ya soma sha yana danna wayarsa har da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Har bayan shuɗewar wasu mintuna yana cigaba da shan abinsa hankali kwance. Da alama ma ya manta da zamanta cikin ɗakin. Sake satar kallansa ta yi. Ji take kamar ta tashi ta yi tafiyarta. Musamman saboda Little da ta bari a waje shi ɗaya. Lura da ba ya ganinta ne ya sanyata soma miƙewa cike da takatsantsan. Daidai lokacin da aka soma ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin. Dakatawa ya yi da abin da yake yi. Ya juya ya kalli ƙofar cike da mamakin wanda ke knocking ɗin. Se ya ajje cup ɗin ya miƙe zuwa wajen ƙofar ya buɗe. Se kawai ya tsaya yana kallan Little ɗin da shi ne yake ƙwanƙwasawa. Waye wannan ɗin? Ya tambayi kansa.

"Didina ta shigo?" Little ya yi maganar kamar ze fashe da kuka.

"Didi.." ya maimaita sunan a kan laɓɓansa fuskarsa na cigaba da nuna mamakin da ya ke ciki.

"Waye hakan?" Ya tambaya yana kallan Little.

"Didina.." ya sake maimaita sunan kawai. Da sauri ta sake miƙewa jiyo muryar da ta yi. Se kawai ta ƙaraso bakin ƙofar tana kallan Little ɗin. Daidai lokacin da ya ɗaga kai ya kalleta se kawai ya tafi da gudu ya rungumeta. Hannu ta saka ta rungume shi tana murmushi. A hankali ya kalli Bad Man sannan ya ɗaga kai ya kalli Didi kamar me raɗa yace

"Uncle?" Se da ta saci kallan Bad Man ɗin sannan kawai ta jinjina kai tana ƙaƙalo murmushi a kan fuskarta. Sakin hannunta Little ya yi ya tafi wajen Bad Man yace yana murmushi

"Uncle ina kwana?"

"Uncle.." ya sake maimaita sunan a kan laɓɓansa idanunsa a kan Little. Ya ɗan taɓe baki sannan yace

"Ka na lafiya?" Ya yi maganar yana wucesu. Daidai yana shirin giftata ta yi ƙarfin halin faɗin

"Don Allah mu tafi?" Dakatawa ya yi ba tare da ya kalleta ba. Se kuma a hankali ya ɗaga kai ya kalleta.

"Da wa ya zaunar da ke?" Ya yi maganar cikin basarwa. Ba ta san lokacin da ta ɗaga idanunta ta kalle shi ba, cike da mamakin furucinsa. Se kuma ta yi saurin ɗauke kanta saboda yanda ta ji waɗannan idanunsa masu madaidaitan girma sun mata wani irin nauyi. A take ta ji wani irin ɓacin rai da kuma takaici sun haɗar mata. Ji ta yi kamar ta fashe da kuka saboda haushi. "Lallai ma mutumin nan, yau na sake tabbatarwa ba shi da kirki ko kaɗan." Ta faɗi hakan a cikin ranta. A fili kuma se ta kama hannun Little da sauri ta ja shi suka fice daga ɗakin. Ko da suka koma ɗaki ma duk se ta kasa sukuni, maganar da ya faɗa mata ɗin tana ta dawo mata.

"Didi wai nan gidan kika dawo?" Tambayar Little ta katse mata tunanin da take yi. Se ta dawo da dubanta kansa. Ta ƙaƙalo murmushi tace

"Ehh.."

"Daga yanzu wancan ne Uncle koh?" Ya sake tambaya yana murmushi. Ji take kamar tace masa a'ah saboda haushin da take ji. Se dai ta san halin Little ɗin, idan ta faɗi hakan shi kenan ta zauna masa a kai.

"Ehh shi ne.."

"Tohm.." ya faɗa yana murmushi. Ta ɗauki mintuna masu yawa kafin ta iya mantawa da abin da Bad Man ɗin ya mata. Ta dawo da hankalinta kan Little suka cigaba da hirarsu.

.. "Sannu da hutawa Ummeey.."

"Yawwah sannu ka dai.. ka dawo?"

"Eh Ummeey.. Abeey na ciki kuwa?" Gwani ya tambaya yana kallan ƙofar ɗakin Abeey.

"A'ah ya fita kam babu jimawa.."

"Ohk.."

"Wai ni kam ba daga kasuwa kake ba ne?" Se da ya kai hannunsa ya ɗan shafa kansa kafin ya girgiza kai

"A'ah Ummeey ba daga nan nake ba."

"Oh ni 'yasu.. Wai Affan me kake so ka zama ne? Kai ba ga kasuwar ba, kai ba ga zama ka kula da er mutane ba?" Shiru ya yi kamar ba ze yi magana ba se kuma ya ɗan gyara zama kafin yace

"Ki yi haƙuri Ummeey.. Amma ba wani abun ba ne. Kawai dai akwai wani dalili da yake saka ni fitar. Amma In Sha Allah ya zo ƙarshe. Kasuwa kuma Ummeey yanzu ina da damar bawa wani riƙo ya riƙe min ba lallai se na je ba." Jinjina kai Ummeeey ta yi sannan tace

"Duk da haka dai Affan.. Ya kamata ka din ga zuwa ɗin kullum."

"Shi kenan Ummeeey In Sha Allah.." ya faɗa da murmushi a kan fuskarsa.

"Toh Allah ya yadda."

"Ameen" ya amsa da hakan yana cigaba da zama a wajen. Bayan shuɗewar wasu mintuna ya sake satar kallan ɗakinsa. Se kuma ya maida dubansa kan Ummeeey yace

"Ummeeey bari na je."

"Toh madallah.." Ummeeey ta faɗa. Ba tare da ya sake cewa komai ba ya miƙe a nutse ya wuce ɗakin. Da sallama ya shiga ɗakin a hankali. Idanunsa a kan gadon da yake da tabbacin tana kai. Aikuwa ilai tana kai ɗin se dai saɓanin yanda yake tunanin ze ganta a kwance se ya ganta zaune kan gadon kamar wadda aka yi wa dole. Ya riga ya fuskanci taɓarar da take ji da ita yanzu dan haka ba tare da ya ce da ita uffan ba ya saka hannu ya ɗauki wayarsa cike da fatan ta yi wayar kamar yanda ya bar mata wayar dan ta yi kira. Kai tsaye call logs ya shiga. Da alama ta manta ba ta yi deleting contact ɗin ba bayan ta gama. Ya yi murmushi har ransa yana jin daɗin hakan. Dan ko babu komai ya san za ta rage damuwa kaso me yawa daga cikin wadda take ciki.

"Ki na lafiya?" Ya tambaya yana kallanta. Sarai ta ji maganar tasa. Se dai ba tace komai ba se ɗauke kai da ta yi tana ji kamar ta tashi ta masa duka saboda wannan tambayar da ya yi mata. Ya san tabbas ta ji shi, ya kuma san har yanzu haushin nasa take ji shi ya sa ta nuna kamar ma ba ta san da wanzuwarsa cikin ɗakin ba. Jinjina kai ya yi yana cije lips ɗinsa gami da murmushin gefen baki dukka lokaci guda. A hankali ya shiga takawa zuwa wajen gadon. Duk da ta ji motsinsa hakan be sanyata juyowa ba. Dan ta riga ta san idan ya gama surutunsa ba ta tanka shi ba ze fice ne ya ƙyaleta. Se dai kafin ta yi aune se jinsa ta yi a kan gadon. Ta juya da sauri ta kalle shi, se ganinsa ɗin kuwa ta yi kan gadon.

"Damm!!" Ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske.

"Na shiga 3.." ta faɗa a kan laɓɓanta tana cigaba da kallansa. Ba tare da yace komai ba ya soma matsawa inda take. Ba ta san lokacin da ta yi baya ba muryarta har ta soma rawa tace

"Wai me ye haka ne kam?" Ta faɗa lokacin da wata ƙwalla ta ida tarar mata cikin idanu. Ƙiris take jira ta zubo. Cikin basarwa yace yana kafeta da idanunsa

"Ina so ne na duba ko lafiyar taki ƙalau, tun da kin ƙi ba ni amsa." Ya yi maganar still yana ƙara matsawa kusa da ita. Dab yake da haɗe tazarar dake tsakaninsu. Ba ta san lokacin da ta yi wani baya ba da sauri. Tana shirin sauka ya sanya hannunsa ya riƙota da sauri, ya yo baya da ita ya zamana ta faɗo kansa. Kawai se ta fashe da kuka. Cikin ƙarfin hali ta sanya hannunta ta riƙo na shi hannun tana girgiza kai ta soma faɗin

"Don girman Allah ka yi haƙuri ka ƙyale ni. Wallahi Allah lafiyata ƙalau.. Ka ƙyale ni don Allah.." ta faɗa hannunta riƙe da na shi da ta ƙi saki tun ɗazun. Be san sanda wata dariya mara sauti ta ƙwace masa ba. Wato duk tsiwarta matsoraciya ce ta ƙin ƙarawa. Gaba ɗaya ta rikirkice, jikinta na wani irin karkarwa kamar wadda ake shirin yankawa.

"Ban yadda ba.." ya sake faɗa yana ƙoƙarin zame hannunsa. Duk wani ƙarfinta ta saka ta sake riƙo hannun nasa da ƙyar ta iya buɗe baki tace
Chapter 60 · 0% Book details