← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 122

Sashe 58

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai Didi. Ni fa Allah Didina ta gaske nake son gani" Ta faɗa tana cuno baki. Sun kwashe fiye da awa 2 suna wayar. Sun yi hirar yaushe gamo, sun kuma taɓo Bad Man. Inda Lulu ke bawa Didi labarin abin da ya faru a Restaurant ɗin nan. Da kuma gaskiyar da ta bayyana. Ta kuma sanar da ita yanda a da take zargin Bad Man se daga baya ta gane ashe ba shi ba ne. Ba ƙaramin tashin hankali Didi ta shiga ba jin labarin da Lulun ta bata. Se dai ta gefe guda kuma ta ji wani sanyi jin da ta yi ba Bad Man ɗin ba ne ya yi wa Lulun hakan. Se kuma a lokacin ne ta iya fahimtar abin da ya kawo Bad Man gidansu. Wato ya ɗauka ita ce Lulu. Ashe ƙaddarar aurensu ke kiransa. Se ta sauke ajiyar zuciya lokacin da Lulu ta gama bata haƙuri a kan ɓoye matan da ta yi tun ranar da suka je Restaurant ɗin saboda ta ga Ɗidin ta ji haushi.

"Don Allah ki yi haƙuri Didina.. Ba na son ɗaga miki hankali ne.. Kuma ban san ma haka ne ze biyo baya ba shi yasa.. Amma ki yi haƙuri kin ji Masoyiyatah.."

"Ki je can ki nemi Masoyiyarki ba dai ni ba.." Didi ta sake faɗa.

"Haba mana Didi na baki haƙuri fa don Allah.." ta faɗa a shagwaɓe. Da ƙyar ta samu ta shawo kan Didin ta haƙura.

"Wai ya na ji kamar muryarki ta sauya ta koma ta masu hankali.."

"Kai Didi da ba ni da shi.?" Ta ƙare tana waro idanunta. Se kuma ta yi shiru ta yi jin abin da Didin ta faɗa. Toh ko dai ta gane abin da ya faru tsakaninta da Gwani duk da ba ta faɗa mata ba? Idan kuwa haka ne daga yanzu ba za ta sake kiran kowa ba balle ma a ganeta.

"Ni dai ban ce ba.." Didi ta faɗa tana dariya. Sun ɗan ƙara mintuna suna wayar kafin daga bisani suka yi sallama cike da farin ciki, suna ji kamar kar su dena wayar. Ko kuma su dawwama suna yin wayar tun da dai yanzu ba sa kusa.

.. A palourn baƙin Daddy aka sauki Abba da ke riƙe da hannun Little.

"Abba wai nan ne gidan Didin?" Little ya faɗa yana kallan Abba. Jinjina kai Abba ya yi yace

"Nemi waje ka zauna.. Yanzu za ka ga Didin taku.." Babu musu Little ya haye kan kujerar ya zauna yana jejjefa ƙafarsa. Duk ya matsu ya ga Didin. Bayan wajen minti 10 se ga Daddy ya shigo cikin ɗakin, sanye cikin wasu manyan kaya en ubansu. Malam kayan nan sun gaji da haɗuwa, ga shi kuma sun haɗu da kyakykyawan dattijon da kuɗi da kuma ilimi suka samu wajen zama. Cikin takun nan nasa da ke kama da na masu jinin sarauta. Ko kuma ma in ce sarki da kansa ya ƙaraso cikin ɗakin. Kai tsaye ya nemi waje ya zauna. Hannu ya miƙawa Abba da murmushi kan fuskarsa daidai lokacin da yake faɗin

"Haji Muhammad.." Gaisawa suka yi Abba na faɗin

"Barka da shigowa Yallaɓai.."

"Yawwah an zo lafiya?"

"Alhamdulillah.." Abba ya amsa da hakan.

"Ina kwana?" Little ya faɗa yana kallan Daddy. Mika masa hannu Daddy ya yi ya riƙo shi ya hau da shi kan cinyarsa yace

"Lafiya ƙalau.. Me ye sunanka?"

"Little.."

"Areef dai koh?" Abba ya faɗa yana Mallam. Little da murmushi kan fuskarsa. Se ya jinjina kai shi ma yana murmushi.

"A'ah ka ce yarona ne ma sosai ashe.." Daddy ya ƙare maganar yana gyarawa Little ɗin zama. Shi kam Daddy har yanzu halin Alhaji Matawallen burge shi yake yi. Yanda yake tafi da rayuwarsa babu hayaniya. Babu laifi sun ɗan taɓa hira kafin Daddyn ya masa sallama ya fice daga ɗakin.

"Abba Didi.." Little ya faɗa yana riƙo hannun Abba. Daidai lokacin da Didi ta yi sallama cikin ɗakin cike da zumuɗin son ganin Abbanta da kuma Little. Aikuwa tun kafin ta ida shigowa Little ya tafi a guje ya rungumeta. Ita ma rungume shin ta yi sosai tana jin wata shahararriyar kewarsa. Ji take kamar ta yi kuka.

"Didinmu.." ya faɗa kamar yanda wani lokacin suke kiranta da hakan.

"Littlena.." Ita ma ta faɗa muryarta na ɗan rawa. Sun kai wajen minti 1 a haka sannan ta miƙe hannunta riƙe da na shi suka koma wajen Abban. Cike da farin cikin ganin Abban ta gaishe shi. Shi ma ƙwarai da gaske ya ji daɗin ganinta, dan haka suka ɗan shiga taɓa hira duk da sama sama ce musamman da Abba yace ba daɗewa ze yi ba. Aikuwa be daɗe ɗin bs bayan wasu mintuna ya miƙe. A nutse ya sake kallan Didi yace

"Babu dai wata matsala koh?"

"Eh Abba.." Ta ba shi amsa tana wasa da hannun Little.

"Toh shi kenan.. Allah Ya ƙara haɗa kan ku, Ya bayar da zaman lafiya.."

"Ameen." Little ya amsa da hakan, duk da ba fahimtar abin da ake faɗa ya yi ba. Dukkansu se suka yi dariya. Daga nan Abba ya fice daga ɗakin bayan sun sake yin sallama ta bayar da saƙon gaisuwarta wajen Ammi. Ta sauke ajiyar zuciya lokacin da Abban ya fice, tana ji tamkar ta baiwa zuciyata haɗin kai ko ta samu ta fashe da kuka dan ta ji sauƙin abin da take ji. Se dai ta din ga mammazewa kawai. Bayan wasu mintuna ta miƙe hannunta riƙe da na Little suka fito daga ɗakin zuwa nasu sashen..

.. Kamar waɗanda suka shekara a tare haka suka gaisa duk da ba wani annuri a kan fuskar kowanne. Se dai da yake halin ne a haka ya sa ko a cikinsu babu wansa ya damu da hakan.

"Ya ƙoƙari? Allah Ya saka da alkhairi.." Gwani ya faɗa lokacin da ya mke gyara zamansa a kan kujerar me zaman banza. Be amsa ba Bad Man har se da ya tayar da motar suka fara tafiya saman mota sannan yace

"Ameen.." Waqa Bad Man ya kunna kamar kodayaushe ya ƙure volume. A haka ya cigaba da driving cikin kwanciyar hankali. Ɗan runtse idanunsa Gwani ya yi saboda yanda yake jin kiɗan na hawar masa kai kamar me. So yake ya yi magana se dai ba ya so ya wuce gona da iri. Amma kuma yana da kyau ya yi maganar. Dan kuwa a irin wannan lokacin ba ma su sa tabbacin za su sauka daga cikin motar sa ransu ko kuma za su mutu? Idan kuma suka mutu suna jin waƙa fa? Se dai kuma ba ya so a ce ya zaƙe da yawa haka. Amma duk da haka gwara ya magantu. Se da ya sauke ɗan numfashi kaɗan kafin yace

"Idan babu damuwa ka ɗan sauke mana waƙar nan mana.." Kallansa Bad Man ya juyo ya yi. Be saba jin umarni daga wajen wani ba idan ban da Daddy. Ciki kuwa har da Mom. Dan kuwa ko ita idan ta tashi saka shi abu se ta haɗa da rarrashi da roƙo. Daddy ne kaɗai ke ba shi umarni kai tsaye ya aikata. Se ga shi Gwanin na ce masa ya yi kaza. Kamar ya share shi, se dai ya rasa dalilin da yasa yake mugun ganin girman Gwanin tun farkon haɗuwarsu. Se ya ɗan yi irin murmushin nan na saman baki kafin ya cigaba da driving. Kamar be ji abin da Gwani ya faɗa ba, se kuma ya kai hannunsa a hankali ya rage volume ɗin waƙar sosai yanda ma ba a yi ji.

"Na gode." Gwani ya faɗa yana ɗan ƙaramin murmushin nan nasa da ya fi kama da na yaƙe. Be ce komai ba Bad Man ban da cigaba da driving da ya yi har zuwa lokacin da suka isa wani police station. Tare suka sauka suna shiga ciki. Bayan kusan awa 1 zuwa da rabi se ga su sun fito tare da wasu en sanda mata da maza su biyar. Motar su daban suka yi. Bad Man da Gwani suna cikin motar Bad Man. Ya yin da su kuma en sandan suke cikin tasu daban. Wadda idan ka ganta ba za ka taɓa cewa en sanda ne a cikinta ba. Daga can baya kuma wata motar na binsu wadda ita kuma na za ka ce tare suke ba.

.. "Malam ya za ka shigo mana gida haka ba tare da an maka iso ba? Me kake nufi da hakan?" Wani ƙaton saurayi ya faɗa yana kallan mutumin da ya shigo cikin gidan kai tsaye haka nan. Se da ya gyara tsayuwarsa sannan yace

"Amma dai la bari ka ji me ya kawo ni koh? Toh ba wajenka na zo ba.. na zo wajen Ladi ne.." Shiru saurayin ya yi ya kalle ma shi sama da ƙasa kafin yace

"Ta san da zuwanka..?"

"Wai Gaddi hayaniyar me nake ji ne? Me ke faruwa?" Ladi dake fitowa daga cikin ɗakin nan nata ta faɗa tana gyara zaman ɗankwalin kanta da shi da babu duk ɗaya. Dan kuwa duk uban tulin attachment ɗin dake kanta ya fito tun daga sama har ƙasa. Sanye take cikin wata riga ta roba irin me kama jikin nan. Se skirt da ta saka wanda ya kamata gam kamar za ta fashe.

"Wannan mutumin ne ya shigo babu izini mana.." Wanda aka kira da Gaddi ya faɗa yana hararar mutumin. Maida dubanta kan mutumin Ladi ta yi ta kalle shi na tsawon sakanni kafin ta maida idanunta kan Gaddi tace bayan ta jefa masa harara

"Bash shi mana.. Be faɗa maka mun yi da shi ze zo ba ne?" Ta ƙare maganar tana ida fitowa daga cikin ɗakin. Jikintan nan na rawa kamar ba jikinta ba. Ita a lallai dole se ta ja ra'ayin koma wane ne.

"Aou toh ai se ya yi magana.." Gaddi ya faɗa yana soma barin wajen. Se ta kai hannu ta daki kafaɗarsa daidai lokacin da take furta

"Toh yi haƙuri sarkin mita." Mutumin ya bi su da kallo kafin ya jinjina kai.

"Mu je koh?" Ta faɗa tana sakin wani shu'umin murmushi.

"Ina dai ke ce Ladin ban yi ɓatan kai ba?" Da sauri ta girgiza kai
Chapter 58 · 0% Book details