Sashe 75
A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.. Tun da ta ga Daddyn cikin ɗakin se ta sake wani narkewa ita a lallai dole dan ya san ta ji jiki fa. Ya kalli yaron da ba a daɗe da dawo da shi ba bayan duba shi da aka yi aka tabbatar lafiyarsa ƙalau.
"Bacci yake yi ne?" Ya ƙare yana kallanta.
"Ehh.. Ai gwara ya huta bawan Allah.. Ya wahalar da kansa ya wahalar da ni.." Ta ƙare tana yaƙe haƙora. Kallan cute fuskar yaron Daddy ya yi kamin yace
"Bawan Allah.. Sannu.. Yaron da Sa'adah ta haifa ya koma." Ya ƙarasa maganar yana kallanta. Kamar da gaske ta ɗaga kai da sauri tana faɗin
"Inna lillahi.. Ita ma ta haihu ne?" Daddy ya jinjina kai yana neman waje ya zauna.
"Wayyo.. Allah sarki.. Allah Ya ji ƙansa, Ya sa me ceto ne."
"Ameen Ya rabbi." Daddy ya faɗa. Cikin zuciyarsa yana mamakin yanda Mom ɗin ta nuna damuwa sosai, duk wannan uban kishin nata. Ko da yake ai magana ake ta mutuwa, ya san dole ta saduda, komai abinka kuma ka tausayawa Mommahn musamman idan ka ga halin da take ciki.
Duk da yanda ta ga yanayin da Daddyn ke ciki hakan be hanata tambayarsa inda wayarta take ba wai za ta kira Aunt Makiyy. Ba tare da yace komai ba ya miƙa mata wayar yana ficewa daga ɗakin. Se da ta tabbatar ya fita sannan ta danno number Maimunan ta kira. Tun da ta soma ringing se ta shiga dube_dube saboda tsaro kar ta je a shigo ba tare da ta lura ba.
"Yawwah Hajiya ga mu tare da Muttaƙa." Maimuna ta faɗa daga can ɓangaren.
"Ba shi wayar.." Mom ta faɗa tana kallan cikin ɗakin da take. Babu musu Maimuna ta miƙa masa wayar.
"Hello.." Ya faɗa da muryarsa da tafi kama da ta en shaye_shaye. Ba tare da Mom ta amsa ba ta soma faɗin
"Ku san yanda za ku yi da wannan jaririn.. Ban iyakance muku abin da za ku masa ba.. ni dai kun gama min nawa aikin idan kuka salwantar da rayuwarsa, ba na son sake ganinsa har ƙarshen rayuwata. Ka tura min Account number ɗinka da zarar kun gama aikin za ka ji ni.."
✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO65*
___"An gama Hajjaju." Ya faɗa yana jinjina kai. Ba ta sake cewa komai ba ta katse wayar. Maimuna ta kalli Muttaƙa tace.
"Ya za mu yi yanzun?" Shiru ya yi na tsawon sakanni kamar me nazari, har se da Maimuna tace
"Ko dai kawai mu je mu jefar da shi salin alin tun kafin ya tona mana asiri, dan ka ga fa yanzu ya soma kuka." Ɗaga idanunsa Muttaƙa ya yi ya watsa mata wani kallo da ya fi kama da harara.
"Kee!! Duk fa tantirancina ina tsoron Allah.. Wallahi ba zan iya jefar da wannan ɗan tahalikin ba, wa ya san me ze same shi idan mun watsar da shi.?" Ya ƙare da wannan muryar tasa. Buɗe baki Maimuna ta yi tana kallan Muttaƙa, cike da mamakin furucinsa.
"Amma ka san ba za ka iya ba ka karɓi wannan aikin?" Ta tambaya still dai tana kallansa.
"Ke kin san tun da na karɓa zan yi ne.. Kawai dai abin da kika ce ne ba zan iya ba. Tun da dai ba ta ce ga abin da za a masa ba, toh ni dai yanda na yanke kawai mu kai shi gidan marayu.. Duk abin da ya faru da shi laifinsu ne ba nawa ba.." Ya ƙare yana ɗaga hannayensa sama.
"Gidan marayu kuma? Me kenan?" Maimuna ta tambaya.
"Ke kar ki ɗaga min murya mana. Waye ze san gidan marayu aka kai shi? A rana sau nawa ake kawo yara? Daga zarar mun kai shi fa shi kenan an manta da babinsa."
"Ina jin tsoro gaskiya."
"Ke dallah can.. Tsoro kuma?" Muttaƙa ya faɗa yana harararta.
"Idan kuma garin hakan aka kama mu fa? Ta ya ya zamu fidda kanmu?" Shiru ya yi hannunsa a gefen fuskarsa yana bubbugawa, kafin can yace
"Ɗauko shi mu tafi.." ya yi maganar yana yin gaba. Ba tace komai ba ta ƙarasa ta ɗauki jaririn da zuwa yanzun kuka yake yi. Se ta shiga rarrashinsa saboda ya samu ya yi shiru ko dan kar ya ɗaga musu hankali su kasa abin da suke niyyar aikatawa. A lokacin da suka fita daga gidan magrib ta yi, dan haka kafin su isa inda Muttaƙan ya ja su duhu ya sake yi sosai. Ajiye motar ya yi a can nesa da wani ƙaton gini da ya fi kama da gidan marayu. Hannu ya saka ya karɓi yaron da ke hannun Maimuna yace
"Bari ki ga abin da za a yi.." Be jira tace komai ba ya fice daga cikin motar. Cike da takatsantsan da kuma lura haka ya ƙarasa har ƙofar gidan marayun nan. Ya yi gefe inda ya san ba za a gan shi ba, duk da lokacin ma kowa hankalinsa na kan abin da yake yi ne. Se da ya duba gabas da yamma, kudu da arewa, ya tabbatar babu me kallansa sannan ya ajje jaririn. Ba tare da ya kalli inda ya ajje shi ba da sauri ya koma cikin motar. Babu ɓata lokaci ya figi motar suka bar wajen. Daga nan Maimuna ba ta wuce ko ina ba se asibiti, a nan take sanarwa da Mom an gama da jaririn nan. Ba ta damu da inda suka kai shi ba, dan ta san halin Muttaƙa ba raga masa ze yi ba duk kuwa da jariri ne. Ita dai kawai ta tura masa uban kuɗi cikin account ɗinsa. Aikuwa ya yi ta godiya. Ita kam ji take kamar ta haɗa duk abin da ta mallaka ta bawa Maimuna da Muttaƙa, dan ko babu komai sun sakata cikin farin cikin da har abada ba ta tunanin za ta fita daga cikinsa. A ranar Yaya da Aunt Makiyy suka iso asibitin. Kowacce wajen er uwatta ta nufa. Yaya se da ta yi ƙwalla da ta ga halin da er uwatta ke ciki, da kuma jin labarin abin da ta haifa ma ya koma. Aunt Makiyy kam farin ciki kamar ta yi mene, musamman da ta ga Babyn yayar tata kamar shi ya yi kansa dan kyau. Ta dinga koɗa shi kamar za ta cinye shi. Daga farko kamar Mom ba za ta faɗawa Aunt Makiyy yanda aka yi aka samu jaririn ba, se dai daga baya da ta yi tunanin wace ce Makiyyan, kuma da ma babu ɓoye ɓoye tsakaninsu, se ta sanar mata da abin da ya faru. Sosai mamaki da kuma tsoro suka kamata, waɗanda suka gaza ɓoyuwa a kan fuskarta. Tace a tsorace
"Ba kya tsoron a gano gaskiya?"
"Ki ji banza.. Ta ya ya za a gano? Waye ze gano? Kin ga ki kwantar da hankalinki.. Ka da ma ki sake ki saka wannan abun a ranki.. Ni ce na haifi yaron nan ba wata ba. Dan haka ki ma manta da mun yi maganar nan." Mom ta faɗa tana kallan Aunt Makiyy. Ita dai kam mamaki sun kasa barinta tace wani abun. Se kuma can daga baya sannan tace
"Wallahi Yaya tsoronki ya shige ni.. Haka kika iya shirya makirci ban sani ba?" Jin yanda ta koɗata ne ya sanyata yin murmushi tana wani kallan gefe da gefe tana hura hanci.
"Ki na wasa da ni."
A ranar aka sallami Mom, ya yin da Mommah se da ta yi sati sannan aka sallameta bayan ta sha kuka bayan farkawarta. Se dai daga ƙarshe ta fawwalawa Allah komai ta rungumi ƙaddararta hannu biyu. A ranar da aka sallameta ne ranar ya kama sunan ɗan gidan Mom. Yaron da ya ci sunan Areef. Ba ƙaramin hamshaƙin suna aka gabatar ba a ranar. Sunan ɗan gata. Mom ji take babu ya ita, ta yi shiga kala kala, ana wani babbasarwa, ita a lallai dole me haihuwa. Bayan wasu satika haka nan kawai Mom ta kasa sakewa da Maimuna tun bayan abin da ya faru. Duk da Maimunan ba ta taɓa nuna mata wani abu da ze sa ta tsargu ta ga cewar ko za ta iya tona mata asiri ba. Amma ita dai haka nan ta kasa sukuni. Dan haka rana ɗaya aka wayi gari za ta sallami Maimuna. A ranar ta gama aikinta, ta zo da niyyar fita daga ɗakin Mom ta kirata. Se ta dawo ta nemi waje ta zauna, ta kalli Areef da ke gefe yana bacci cikin kwanciyar hankali ta sakar masa murmushi tana kama kumatunsa ta ja kaɗan.
"Ga ni Hajiya." Ta faɗa tana kallan Mom. Se da Mom ta sauke ajiyar zuciya kamin ta ɗauko wata babbar leda ta ajje a gabanta tace
"Ki ɗauki wannan naki ne Maimuna.. kuɗi ne.. ki tafi garinku.. Na gode da kulawarki da kuma taimakonki gare ni.. Allah Ya saka da alkhairi." Da mugun mamaki Maimuna ke kallan Mom ƙirjinta na bugawa, kafin da ƙyar ta yi ƙarfin halin faɗin
"Hajiya me na miki? Me na aikata miki? Wani abun aka ce na miki?" Girgiza kai Mom ta yi da sauri tana faɗin
"A'ah fa Maimuna ba ki min komai ba wallahi.. Yanzun ne kawai ba na buƙatar er aiki, kin san ma ke ba a matsayin er aiki na ɗauke ki ba. Kawai dai na fi so ki koma garinku ki je ki ɗan huta ke ma. Wannan kuɗin ze ishe ki ki yi duk abubuwan da kike buƙata.. Amma don Allah ki yi haƙuri na sallameki, kuma wallahi ba dan komai ba, dan kuwa alkhairinki gare ni yawa gare shi."
"Ki taimaka min don girman Allah Hajiya.. kar ki kore ni.. Ki faɗa min idan wani abu na miki in gyara amma ni dai kar ki kore ni don Allah." Ajiyar zuciya Mom ta sauke sannan tace