← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 122

Sashe 37

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sorry Dad.. but honestly i.." Ɗaga masa hannu Daddy ya yi ransa a ɓace da wannan hali na Areef ɗin, taurin kansa na ba shi ciwon kai.

"Umarni nake ba ka.. Idan kuma ba za ka yi ba ne let me know.." Iska ya fesar daga bakinsa yana miƙewa a kan ƙafafunsa, ya ɗan tsaya na tsawon sakanni sannan ya fice daga ɗakin a fusace. Binsa Daddy ya yi da kallo yana komawa ya zauna shi ma hannunsa a kansa yana girgiza kai. Ya san Areef ɗin na da taurin kai, se dai komai taurin kansa ko da ya nuna fushi a kan abin da Daddyn ya saka shi to fa ze yi ɗin. Janyo wayarsa ya yi ya shiga message ya turawa Bad Man ɗin addrees kamar yanda ya buƙaci a tura masa.

.. Ko komawa ɗaki be yi ba ya wuce inda motarsa take. Ya hau ya figeta da wani irin gudu kamar ze tashi sama. Ransa a mugun ɓace yake driving ɗin. Idan ba dan Daddy Daddy ba ne da babu wanda ya isaya dinga saka shi abin da be yi niyya ba, ballantana kuma a kai ga zuwa ɗauko yarinyar nan daga wani waje kamar wani Drivernta. A harabar asibitin ya yi parking motarsa har lokacin fuskarsa babu yabo babu fallasa. Ya shafe wajen minti 5 zaune a cikin motar ba tare da ya yi yunƙurin aikata komai ba. Se dai kuma fahimtar da ya yi ko da ze shekara ne a wajen idan dai har be je ba ba za ta san ya zo ba ballantana ta zo su tafi. Ya ja tsaki yana jin wani irin haushi na cika shi. Me ya sa Daddyn ze masa haka? Ganin dai yana cigaba da ɓatawa kansa lokaci ne ya sanya shi fitowa daga cikin motar, cikin haɗaɗɗen takun nan nasa ya soma takawa zuwa ciki angry face ɗinsan nan a haɗe musamman da ransa ke a ɓace.

.. Ganin Didi da ta yi gaba ɗaya ya sanyata kasa yin musu a kan duk abin da ta sakata yi. Abincin haka ta zauna ta ci da taimakon Didi, haka maganin ma ta sha dukka da taimakon Didin. Sosai suke hirar yaushe gamo duk da jefi jefi suke yinta. Se dai sun kasa yin shiru, haka suka dinga biye wa Little dake ya surutunsa kamar yanda suka saba. Se suke jin yau ɗin ta daban, suke jinsu kamar a gidansu. Abubuwa da dama yau ɗin ta tuna musu, dan haka se ta kasance rana ta musamman a wajensu. Ummeey da Gwani tare suka shigo ɗakin a yanzu haka. Cike da fatan da suke yi kuwa se suka ga Lulun zaune tana kallan Little har da su dariya kamar ba ita ce mara lafiyar ba. Har ran Ummeey hakan ya yi mata daɗi sosai. Gwani ya ɗan yi murmushi yana sauke ajiyar zuciya, ko babu komai yanzu kam ze iya fita ya je ya samu Abbati su yi magana.
Kamar an ce ta juya se kuwa ta hange shi tsaye a bakin ɗakin yana kallan ciki. Ɗan rufe idanunta ta yi ta buɗe su a kan shi dan sake tabbatarwa kanta fuskar da take gani, ta ɗan runtse idanunta na tsawon sakanni sannan ta buɗe still dai a kansa. Ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske lokacin da ta ida shaida fuskar, cikin sauri kuma ta ɗaga hannunta ta shiga nuna shi se dai kuma ta gaza furta komai. Didi, Ummeey har ma da Gwani gaba ɗaya bin inda take kalla suka yi da kallo cikin sauri. Bad Man na tsaye hannayensa duka biyun cikin aljihunsa. Didi dake kan gado ta yi saurin saukowa daga kan gadon cike da mamakin ganinsa cikin asibitin. Yayin da Gwani ya sake maida dubansa kan Lulu da har lokacin ba ta dena nuna Bad Man ɗin ba, kuma ba tace komai ba. Tsantsar mamakin da na gani a kan fuskar Ummeey shi ne ya sanya ni kallan fuskar tata daidai lokacin da ta miƙe tsaye tana kallan Bad Man.
Daidai lokacin da shi kuma ya soma takowa zuwa cikin ɗakin Lulu ta yi ƙarfin halin kallan Gwani tace

"Shi ne..!!" Sanda wasu kyawawan hawaye suka zubo a kan kuncinta. Maida dubansa kan Bad Man Gwani ya yi bayan ya ji abin da Lulu ta faɗa, daidai lokacin da shi ma Bad Man ɗin ya saukar da idanunsa a kan Gwani. Kamar wanda aka dakatar se shi ma ya dakata yana kallan Gwanin. Kamar wasu zakaru haka suka shiga kallan kallo kowanne da abin da ke cikin ransa..

Toh Alhamdulillah! Daga haka zance se Allah ya kai mu bayan Sallah. Allah ya sa mu shiga watan Ramadan a sa'a, ya sa mu yi ibada karɓaɓɓiya, ya sa muna daga cikin bayinsa 'yantattu. Ameen ya rabbi.

MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO43*

___ Cikin en sakannin da basu wuce 5 ba Bad Man ya ɗauke idanunsa daga kan Gwani ya maida su zuwa cikin ɗakin, daidai lokacin da Lulu ta sake kallan Gwani da idanunta da lokaci ɗaya suka ciko da ƙwalla. Haɗa idanun da suka yi ne ya sanya ta sake faɗin

"Shi ne.."

Rashin fahimtar abin da take nufi ya sanya shi soma takawa zuwa cikin ɗakin har lokacin be ɗauke idanunsa daga kanta ba, kamar yanda ita ma ba ta ɗauke nata idanun daga kansa ba. A nutse ya ɗan ranƙwafa saitinta ba tare da yace komai ba ya ɗan karkatar da kansa yana sanya idanunsa cikin nata.

"Na cikin hoton nan.." shi ne abin da ta furta lokacin da ta zame ƙwayar idanunta daga cikin nasa. Tana ida faɗa ya miƙe a kan ƙafafunsa ya juya yana kallan Bad Man da ya maida wayarsa cikin aljihu sannan ya soma cigaba da takawa zuwa cikin ɗakin. Sake juyawa Gwani ya yi ya kalleta, fahimtar abin da yake nufi ya sanya ta jinjina kai cike da tabbatarwa. Haka nan kawai take jin wani irin sanyi na ratsata, se dai kuma ta kasa fahimtar dalilinsa na zuwa cikin ɗakin da take kwance. Didi da ta fahimci lallai tabbas Bad Man ne, ta kuma san babu abin da ze kawo shi nan ɗin idan ba ɗaukarta ya zo yi ba kamar yanda Mommah ta faɗa mata. Hakan ne ya sanya ta miƙewa da sauri cikin zuciyarta tana jin babu daɗi kwata kwata, yayin da take Allah Allah su fita daga cikin ɗakin kafin ya nuna musu halinsa na rashin kirki. A ɗan ɗarare ta kalli Ummeey da zuwa lokacin ta koma inda ta tashi ta zauna a sanyaye. Kamar yanda ta ji sunan a bakin Little tace

"Ummeey bari mu tafi.." ta faɗa tana wani yaƙe, haka nan kawai take jin bugun zuciya. Da mamaki Ummeey ta kalleta bayan ta kalli Bad tace

"Mijinki ne?" Satar kallan shi ta yi lokacin da ya watsa mata idanunsa dan ya tabbatar da ta gan shi kafin ya fita. Se ta ɗauke kanta tana ƙaƙalo wani murmushi lokaci ɗaya tana jinjina kai a sanyaye. Kallan Bad Man Ummeey ta yi daidai lokacin da yace

"Ina yini..?" Ya faɗa kamar ba shi ba..

"Ikon Allah.." Ummeey ta faɗa fuskarta na nuna zallar mamaki. Ba ta iya amsawa ba se da ta juya ta kalli Didi, Lulu har ma da Gwani sannan ta dawo da dubanta kan Bad Man tace

"Lafiya ƙalau.." Shi be ma ji ta ba dan yana gama yin gaisuwar ya fice daga ɗakin saboda ya riga ya tabbatar wadda ya zo dominta ɗin ta gan shi. Se a lokacin sannan Gwani ya ƙaraso yana kallan Ummeey yace

"Ummeey bari na ɗan fita.." Da "toh" ta amsa masa, shi kuma ya fice daga ɗakin. Dama tunanin yanda ze yi maganar a gaban Ummeey yake yi, ba ya so ko kaɗan ta ji maganar. Yanzu kuwa da Bad ɗin ya fita se ya ji har cikin ransa hakan ya masa. A gaggauce Didi ta yi wa Lulu sallama, duk da tarin tambayoyin da suke yawo a ƙwaƙwalwar Lulun amma yanda Didin ke sauri ya sanya ta adana su. Har cikin ranta ba ta ji daɗin tafiyar tata ba, se dai sanar da ita da Didin ta yi za su din ga waya ya sanya ta jin sanyi a ranta. Hankalinta gaba ɗaya ya rabu gida da yawa, tunaninta gaba ɗaya ya cukurkuɗe. Kawai se ta kwantar da kanta ta ɗan lumshe idanunta cike da tunani barkatai.

... Hango shi da ta yi yana dab da ƙarasawa inda motarsa take ya sanya ta ɗaga ƙafa, se dai duk ƙwaƙwar mutum ba ze iya fahimtar hakan ba. A daidai tana dab da ƙarasawa se ta hangi Gwani ya riga ta ƙarasawa inda yake. Da matuƙar mamaki ta kalle shi daidai lokacin da ya ƙarasa inda Bad Man ɗin yake. Se kawai ta dakata a inda take tana cigaba da kallansu.

A nutse ya ɗaga kai ya kalli me ƙarfin halin da yake ƙoƙarin riƙe ƙofar da ze buɗe dan shiga cikin motarsa.

"Assalamu Alaika.." Gwani ya faɗa fuskarsa babu yabo babu fallasa yana kallan Bad Man irin kallan nan na ido cikin ido. Dakatawa Bad Man ya yi shi ma yana kallan Gwani cike da mamakin waye shi? Me ya kawo shi wajensa?. Irin kallan da yake masa ya fi kama da na wanda ya kama wani me laifi ko kuma wanda ya kama wani da ya aikata aikin saɓo. Samsam be ga ya masa kama da me neman taimako ba, dan kuwa daga yanayin halittarsa har kayan dake jikinsa ba su yi nuni da wanda ke cikin wahala ba. Se dai shigar tasa da ta fito da ainahin kamalarsa, da kuma yanda kallo ɗaya mutum ze masa ya fahimci Malamin Addini ne. Dab da dab suke, kowanne na ma ɗan uwansa kallan tuhuma.
Chapter 37 · 0% Book details