← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 122

Sashe 94

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ni kaina.. Kawai na bari ne su shigo ɗin. Allah Ya kawo su lafiya." Mommah ba ta iya sake furta komai ba saboda tsananin mamaki. Dan ita dai tun da ta ji alamar mutanen da suka zo daga gidan sarki suke jikinta ya yi sanyi, haka kawai ta kuma shiga tsintar kanta cikin bugun zuciya. Kawai se ta yi shiru ta baza ido dan ganin su waye za su shigo. A nutse, cikin kuma dattako da kuma sarautar da ke yawo a cikin jininsa ya shigo cikin ɗakin tare da fadawa. Se da ya nemi waje ya zauna kafin ya bawa fadawan umarni da su fice daga ɗakin. Tun da suka shigo Mommah ke kallansu. Da sauri Daddy ya miƙe cike da mamaki ya furta

"Yallaɓai.." Ya yi maganar cike da maɗaukakin mamakin ganin Sarkin a cikin palournsa ba tare da wani dalili ba. Kafin ya ida tunani se ga Yaya Amina ta shigo cikin ɗakin, bayanta wasu mata ne guda 5. A'ah mamaki fa na neman kashe Mommah. Ta kuma kasa gane me ke faruwa. Me ye haɗin Yaya Aminar da waɗannan mutanen.

"Duk ku zauna.." Sarki ya yi umarni da hakan da muryarsa me kauri da kuma wani irin kwarjini a cikinta. Babu musu duk suka nemi waje suka zauna. Idanun Mommah gaba ɗaya yana kan Yaya Amina ne, dan ƙarin bayani kawai take jira. Kamar kuma ta san me take nufi, se ta kalli Mommah tace

"Sa'adah Baba Abdullahi ne.." Shiru ta yi na en wasu sakanni kafin can tace

"Wanne Baba Abdullahin?" Ta faɗa cike da maɗaukakin mamaki, kasancewar Baba Abdullahi dai ɗaya ta sani a rayuwarta. Ita kuma yanzu wanda take gani zaune a nan ba ta shaida fuskarsa ba ballantana har ta kawo cewar shi ne Baba Abdullahi. Se dai ko dan kaɗe-kaɗen da ta ji ya sa ta yi tunanin yana da alaƙa da sarauta.

"Baba Abdullahi dai namu Sa'adah.." Maida dubanta kansa Sa'adah ta yi cike da mamaki tana kallansa. Idan dai har ba ta yi kuskure ba se yanzu ta fahimci wannan ɗin Sarki ne wanda suka sani, se dai ba su taɓa ganinsa a zahiri ba se yanzu da yake zaune ga shi ga su. Shi ne kuma Yaya Amina ke faɗa mata Baba Abdullahi ne? A hankali Mommah ta ƙarasa ta zube a gaban Sarkin tana faɗin

"Baba Abdullahi."

"Na'am Sa'adatu.." Kawai se Mommah ta fashe da kuka. Kamar wadda aka wankewa ƙwaƙwalwa, ko kuma wadda aka zuba mata sabon tunani haka ta ji. Baba Abdullahi? Baba Abdullahi shi ne Sarkin garin nan, sun san shi suna kuma ganinsa amma ba su taɓa tunanin komai ba. Wannan wane irin abu ne?

.. Mommah da Yaya Amina sun kasance 'ya'ya ne ga yayan Baba Abdullahi, wato tsohon Sarki Abdulrazaq kafin Allah Ya karɓi rayuwarsa. Lokacin da yana raye shi ne Sarki. Ya kasance yana da mata biyu. Mahaifiyarsu Mommah 'ya'yanta biyu Sa'adah da kuma Amina. Ya yin da ɗayar ke da 'ya ɗaya Ramla. Lokacin da suke a matan Sarki ba ƙaramin kishi ake bugawa ba, dan ita Samira wani kalar jahilin kishi take da Mahaifiyarsu Mommah, musamman lokacin da take da 'ya'ya biyu ita kuma tana da ɗaya. Se dai ashe tsananin kishin da ze kaita ga saɓawa mahalicci yana nan zuwa, shi ne lokacin da Mahaifiyarsu Mommah ta haifi maza en biyu waɗanda suka ci suna Hassan da kuma Hussaini. A lokacin ne Samira ta kusa ƙaramin hauka, daga lokacin ne kuma tunaninta ya chanja, dan ba ƙarya hankalinta ya tashi saboda ganin magadan Sarki Abdulrazaq sun zo. Dan haka se ta fara shiga bokaye. Ta din ga bin bokaye dan su mata maganin damuwarta. (Wa iya zubillah) Abu na farko da suka fara fuskanta shi ne wata matsananciyar rashin lafiya da babarsu Mommah ta soma yinta, wadda kwata kwata aka rasa gane kanta. Babu kuma daɗewa Allah Ya karɓi ranta. Mutuwar da ta girgiza gidan sarautar gaba ɗaya, ban da mutum ɗaya da tafi kowa farin ciki da hakan. Ko banza ta gama da matar, hankalinta ze kwanta tun da dai yanzu babu fargabar kar ta je ta sake haifar namiji. Daga nan kuma se hankalinta ya koma kan En biyun. Sati 1 da mutuwar Mahaifiyarsu Mommah Hussaini ma ya rasu. Nan take gidan Sarkin ya sake rikicewa. Haka dai suka haƙura. Tun daga wannan lokacin se hankalin Samira ya koma kansu Mommah da kuma Hassan. Dan ita ta ɗauka ma har Hassan ɗin za a gama mata da shi. Se dai a nan bokan nata ke faɗa mata dole se dai su fara gamawa da mutum ɗaya kafin su koma kan ɗayan. Ita gaba ɗaya kishin nata ma ba a kan namiji ne kaɗai ba, dan duk da ta san namiji ne kaɗai ze iya yin sarauta, amma kishi ya rufe mata idanu, dan sam ta ƙi jinin ta buɗe idanunta ta ga su Mommahn. Hakan ne ya sa ta je aka mata aikin da za a raba su Mommahn da ɗan uwan nasu daga dangin mahaifinsu gaba ɗaya. Dan tun da an kasa gamawa da Hassan ɗin gwara kawai a kaɗa su can wani wajen su je su ƙarata. Dan tana tsoro ka da ta barsu su rayu cikin gidan kuma nan gaba Sarki ya bar duniyar a zo a ce shi ze gaje shi. Ana cikin hakan ne kuma Sarki suka yi hatsari a kan hanyarsu ta dawowa daga wata gaisuwar Abokin Sarkin. Kuma a hatsarin ne Abban nasu ya rasu. Mutuwar da ta fi kowacce mutuwa girgiza kafatanin gidan. Bayan mutuwarsa ne kuma babu daɗewa aikin Samira ya fara aiki. Sam su Mommah se suka kasa zaman gidan, musamman da ya kasance kowa na gidan ya juya musu baya. Babu be raga musu, daga ƙarshe ma se ya kasance babu me bi ta kansu gaba ɗaya. Su kansu ji suke kamar ana kaɗa su. Kamar kaɗa su ake da su bar gidan. Ga shi ko Baba Abdullahi wajen sati kenan be neme su ba. Ko ya manta da suna gidan ne? Ba su sani ba. Se dai su ma cikin ƙanƙanin lokaci wata irin tsanar gidan ta addabe su. Ana cikin haka ne kawai suka saɓi jiki suka bar gidan, kasancewar ta saka an ɗauke hankalin kowa daga kansu ya sa babu wanda ya neme su. Se dai inda Allah Ya taimake su se suka yi dangin mahaifiyarsu. Gwaggo ita ce ta riƙe su su ukun. Dan da ma tun mutuwar er uwatta ta so ɗaukarsu. Tun daga lokacin se ya kasance sun manta da wasu en uwan Babansu kwata kwata. Yanda ka san an goge musu wani abun haka suka manta da su kwata kwata. Gwaggo ce ta riƙe Hassan ta cigaba da kula da shi. Se dai da yake shi ma ba me tsawon rai ba ne ba a daɗe ba ya rasu. Haka dai Gwaggo ta cigaba da riƙe su kamar ita ce ta haife su. Tun tana musu zancen dangin mahaifinsu har ta gaji ta watsar, musamman da ta ga ko lokacin da za su dawo wajenta da zama babu wanda ya kawo su, su kaɗai suka zo. Daga nan dai rayuwarsu ta cigaba da tafiya.

A can ɓangaren kuma Baba Abdullahi da ya hau kan kujerar Sarkin shi ne ya auri Samira bayan mutuwar Sarki Abdulrazaq. Daga nan ta cigaba da zuba rayuwarta. Gaba ɗaya dai ta mantar da su rayuwarsu Mommah. Babu kuma wanda ya sake tunawa da su har zuwa shuɗewar waɗannan shekarun. Se a cikin satin can da Allah Ya karɓi ranta, ba tare da ta nemi yafiyar ɗumbin laifukan da ta aikatawa en adam ba. Se dai kafin ta mutun se ta din ga tonawa kanta asiri a kan abubuwan da ta aikata. Babu wanda be yi mamaki ba a duk waɗanda suka ji lokacin da take waɗannan sumbatun. Haka dai ta tafi a banza, bayan wata irin mutuwar wulaƙanci da ta yi. A lokacin ne asirinta ya soma warwarewa a hankali, dan kuwa cikin ƙanƙanin lokaci mutane da dama suka fara tunawa da 'ya'yan Sarki Abdulrazaq. Musamman ma Baba Abdullahi da hankalinsa ya tashi a lokacin saboda buɗe ido da ya yi ya ga babu Sa'adatu, babu Amina kuma babu Hassan. Ga kuma maganganun da Samira ta din ga faɗa kafin ta mutu. Sosai hankalinsa ya sake tashi, ko bacci ba ya iya yi a cikin kwanakin. Ya kasa sukuni saboda tunanin kamar be riƙewa ɗan uwansa amana ba.
Chapter 94 · 0% Book details