← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 122

Sashe 7

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A bar min ita anan idan babu damuwa. Ga mukullin sashenta nan se ku shiga ku duba.." Mommah ta faɗa da murmushin dai. Karɓa Aunty Maryam ta yi, suka fito daga sashen Mommahn zuwa na kusa da nata. Wanda aka ce musu shi ne na Didi. Tun kafin a shiga parlour ma kaɗai abin kallo ne, ballantana kuma bayan an shiga. Komai na ciki abin kallo ne, dan kuwa ya ƙayatu matuƙa gaya. Komai a kintse, a gyare, a kuma nutse, babu hayaniya, se zallar kyau me tafiya da zuciya. Suka kuwa kashe kwarkwatar idanunsa sannan suka fito cike da santin gidan. Zuwa lokacin Mami kawai bin kowa take da idanu, dan kuwa mamaki ya kusa kasheta. A ina Abba ya samo wannan ɗin? Ashe dama Abban yafi son Didi bata taɓa sani ba se yau? Ya aka yi Didin ta samu wannan shahararren me kuɗin? A ina kuma Lulu ta samu faƙiri haka, talaka mara arziƙi?. Ɗakin Mommah suka koma inda babu ɓata lokaci suka yi sallama da ita, sannan suka yi da Didi. Kukan da sautinsa ya dena fita ta fashe da shi sanda zasu tafi ɗin. Haka tana komai suka tafi suka barta ba dan suma sun so ba. A yanzun ma bayan sun fito Mami kasa dena bin gidan ta yi da kallo, ko tamfatsetsen ƙatuwar harabar gidan ma kaɗai abar kallo ce ballantana kuma a kai ga ɗakin Didi, daga nan kuma aje ga ɗakin Mommah. Komai na gidan ya haɗu, komai na gidan haɗaɗɗe ne cikin tsari.

Tashi Mommah ta yi ta koma kusa da Didi a hankali ta saka hannunta ta riƙota tace

"Ki dena kukan haka nan kin ji? Ka da kanki ya yi ciwo.." Mommahn ta faɗa a nutse. Didi ba ta iya cewa komai ba, se maida kukan da ta fara ƙoƙarin yi duk da bata tunanin yiwuwar hakan. Ganin haka ne ya sanya Mommah kai hannu ta ɗan yaye mayafin da aka rufe fuskar Didi da shi, wanda hakan ya bawa kyakkyawar farar fuskarta damar fitowa, wadda ta yi jajir, kamar yanda idanunta ma suka yi.

"Tabarakallah Masha Allah.." Shi ne abin da Mommah ta faɗa tana sakin murmushi sanda idanunta suka sauka a kan fuskar Didi. Jin ta dena kukan se sheshsheƙa da take yi ya sanyata miƙewa tana faɗin

"Bari na samo miki ruwa.." ta faɗa tana wucewa. Ita dai Didi ba tace komai ba se cigaba da zama da ta yi a wajen.

.."A kira Yaya.. Na ji yana zancen ze siyo kayan ɗaki, da sauran abubuwan da ake buƙata a gidan amarya.. Toh wallahi ya bar shi ba se ya siyo ba. A ina za a saka kayan? Shin anya kuwa ma Yaya ya san wanda ya aurawa Lulu kuwa? Ta yaya ma za a ɗauki yarinya kamar Lulu a kaita wannan gidan da yafi kama da gidan marasa galihu?"

"Ke Sadiya ki kiyayi abin da bakinki ze furta. Dan tsabar sanin da na yiwa wanda na aurawa Afaaf, ni da kaina na yi masa tayin aurenta.. Kin ga me ya rage kenan?" Abba ya faɗa ransa a ɓace da halin Mamin da yafi kama da na Lulu kamar ita ta haifeta. Dama ƙarfin hali ne kawai take yi, dan tun fitowarsu daga gidan Alhaji Matawalle ta kasa cewa uffan, se da suka dawo gida sannan ta tuna inda suka baro Lulu kana ta samu ɗan ƙwarin gwuiwar yin magana.

.. Da sallama ya shigo cikin gidan, cike da fatan ze samu babu kowa a gidan. Addu'ar tasa kuwa ta karɓu dan kuwa Ummeey kaɗai ya samu zaune cikin ɗakin kan dadduma da carbi a hannunta. Sallamar tasa ta amsa fuskarta ɗauke da murmushi. Se ya ƙaraso ya zauna yana faɗin

"Barka da wannan lokaci Ummeey.."

"Yawwah barka dai.."

"Ka kuwa ci abinci?" Ummeey ta tambaya cike da kulawa. Jinjina kai ya yi fuskarsa ɗauke da ƙayataccen murmushi, dan ba kaɗan ba yana jin daɗin kulawar Ummeeyn a gare shi.

"Ehh na ci Ummeey.."

"Toh hidima duk ta hana ni sanin halin da kake ciki.. Ko da yake, yanzu ma wannan aikin yana ƙoƙarin tashi daga kaina zuwa kan ɗiyata.."

"Ɗiyarki?" Ya tambaya dan shi har ga Allah be fahimci abin da take nufi ba.

"Ka ji min yaro.. Aou toh ko se na fito ɓalo_ɓalo nace matarka?" Ta ƙare tana murmushi. Yaƙe kawai ya yi, tunawa da ya yi yanzu haka fa se a iya cewa an kawo yarinyar cikin gidan nan. Yarinyar da be san ma ta ina ze fara gabatar da rayuwarsa da ita ba.

"Maza je ka ku taho tare, ina so na haɗa ku ku duka na muku faɗa. Idan Allah ya yi Malam ya shigo ma se shi ma ya tofa albarkacin bakinsa.." Kallan Ummeeyn ya yi se kace wanda ya ji ta yi saɓo. Itama se ta kalle shi cike da mamaki. Ganin tana masa kallan tuhuma ne ya sanya shi faɗin

"Tom.." yana miƙewa ya soma takawa zuwa inda ɗakinsa yake, daidai kuma lokacin da annurin da ya rage a kan fuskarsa ya ɗauke gaba ɗaya. A nutse ya cigaba da takawa har ya isa bakin ƙofar, har lokacin be dena tunanin yanda wannan al'amari ya kasance ba. Ban da ikon Allah, da kuma umarnin Abeey ta yaya ma ze auri wata Afaaf? A hankali ya saka hannunsa ya ɗora a kan ƙofar ɗakin..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO27*

___Cikin nutsuwa ya turata. Dakatawa ya yi saboda halittar da ya gani a bakin ƙofar, dan be yi tsammanin ganinta a wajen ba. Tana tsugunne a bakin ƙofar kanta kife a kan gwuiwarta. Jin an turo ƙofar ne ya sanyata ɗaga idanunta daidai lokacin da ya kalleta, se kuwa suka yi ido biyu. Ƙirjinta ya wani irin bugawa, lokaci ɗaya ɓacin ranta ya sake tasowa, se kawai ta sake maida kanta kan gwuiwarta. Ɗauke kai ya yi yana ƙarasawa cikin ɗakin yana mamakin abin da ya zaunar da ita a bakin ƙofar ɗakin. Se dai daga yanayin yanda ta kalle shi ya san bakinta cike yake fall da rashin kunya, da tsiwa. Wanda be shiryawa karɓarsu a yanzu haka ba, tunda dai shi kam ba shi ya nemi aurenta ba ballantana yace ze daurewa duk wani abu da za ta masa. Neman waje ya yi ya zauna a ɗan gefen gadon, yana tuna cewar Ummeey ce fa ta aiko shi. Shi kam Ummeey ta haɗa shi da aiki, dan kuwa ba ma ya san wata magana ta shiga tsakaninsa da yarinyar a yau ballantana ma wani rainin ya shiga tsakaninsu. Ɗan lumshe ido ya yi lokaci ɗaya yana miƙewa, kyakykyawar fuskarsa a ɓace ya soma takawa kamar ze fice daga ɗakin. A kausashe sanda ya kusa ƙarasawa inda take yace

"Ki tashi zamu je wajen Ummeey.." Idan labulen ɗakin da suke ciki ya kalle shi, toh Lulu ma ta kalle shi. Se da ya ɗan jinjina kansa sannan ya sake maimaita maganar a karo na biyu. Sarai tana jinsa amma a yanda ta nuna ba ma za ka gane ta san da tsayuwar wata halitta a gefenta ba. Takaici, baƙin ciki gami da haushi su ne suka cikata. Kuma tabbas idan be rabu da ita ba a yanzun nan za ta juye masa kwandon rashin mutuncin da zuciya ke ta angizata da ta yi masa a farkon shigowarsa ɗakin. Se dai koma mene ne gwara ta fara ji ta bakin Mami, idan ta bata shawarar se ta haɗata da wadda ta yanke sannan ta aiwatar da komai. Ta gefenta ya raɓa ya fice daga ɗakin, duk da yanda ransa ya ɓaci hakan be saka shi ya sake ce mata komai ba. Yau ɗin ita ce ranarta ta farko a gidan, saboda haka koma mene ne ze mata uzuri ko dan mutuncin mahaifinta, amma daga lokacin da ta nuna rashin kirkin nata za ta cigaba da yi ya zama dole ya taka mata burki. Shi dama abin da yake tunani kenan, ta yadda zamansu ze kasance ba komai ba. Idan shi ya haƙura ya karɓeta a matsayin mata ita kuma fa? Idan shi ya haƙura ze girmamata matsayin matarsa, ita zata girmamashi a matsayinsa na mijinta?. Taune lips ɗinsa ya yi yana lumshe idanunsa dan tabbas ya ji raɗaɗin ƙin tanka masa ɗin da ta yi.

"A'ah.. Ya kuma kai kaɗai..?" Ummeey ta faɗa tana kallan Gwani. Yaƙe kawai ya yi, dan baya so tun a yanzu Ummeeyn ta soma fuskantar banzayen hali irin na Lulu, duk da dai an ce me hali ba ya fasa halinsa. Ba wani cikakken hankali gareta ba, za ta iya nunawa Ummeeyn ma halinta.

"Ina tunanin ko ta yi bacci ne. Dan na yi magana ba ta amsa ba.." ya ƙare yana neman waje ya zauna.

"Allah sarki baiwar Allah.. Ai gwara ta huta ko ta ji daɗin jikinta.."

"Uhmm.." Kawai ya faɗa dan ko maganar ma ba ya son yinta. Shi kam wannan aure ze iya kiransa da takura. Abu mafi muni kuma halin Lulun, da wata yarinya ce ma me tarbiyya da sanin ya kamata da se ya yi tunanin zamansu ze yiwu cikin kwanciyar hankali. Se dai Lulun ba kamar haka ba ce, ita bauɗaɗɗen hali gareta, me wuyar tanƙwaruwa. Cigaba da zama ya yi a wajen Ummeeyn suka cigaba da hira. Zuwa can dai da Ummeey ta lura ba shi da niyyar tashi se ta kalle shi tace

"Ka bar er mutane ita ɗaya fa.." ɗan lumshe idanunsa ya yi har lokacin ya kasa dena tunanin yanda komai ya kasance.

"Zan tafi Ummeey.."

"A'ah ba da ni ba Affan. Tashi maza ka tafi.. Allah ya bamu alkhairi.." Babu yanda ya iya haka ya miƙe sannan ya amsa da
Chapter 7 · 0% Book details