← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 122

Sashe 80

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ku nemi waje ku zauna Yaya.. Labarin me tsayi ne.. Daughter zauna.." Ta ƙare maganar tana kallan Didi. Babu musu kowannensu ya nemi waje ya zauna a sukwane. Bayan shuɗewar minti 1 Mommah ta shiga faɗa musu abin da ya faru tiryan tiryan kamar yanda Maimuna ta faɗa musu. Shiru suka yi bayan sun gama jin abin da Mommahn ta faɗa. Kafe Mommah da ido kawai Yaya ta yi kamar me son gano wani abun daga cikin fuskarta. Mamaki, tsoro gami da tsananin takaici da kuma jin abin kamar almara duka suka haɗarwa Yaya. Ta fi minti 5 ba tare da ta iya cewa komai ba. Ta ɓangaren Didi kuwa kawai se ta tsurawa Mommahn idanu kusan minti 1, kafin ta janye ta maida shi kan Bad Man. Tsananin tashin hankali da tsoron mutanen duniya ya sanya jikinta ke ta ɓari kamar me jin sanyi. Tuni idanunta sun cika taff da hawayen da dan kansa yake sauka a kan kuncinta. Ashe Areef ba ɗan Mom ba ne? Ashe Mom ba ita ce sirikarta ba? Wannan matar me kirki, mutunci da kima me kuma ƙaunarta ita ce sirikarta? Ita gaba ɗaya kanta ma ya kulle, ƙarƙari abin da ta fi tunani shi ne "Waɗanne irin mutane muke da su a cikin duniyar nan?" Ta tambayi kanta har lokacin zuciyarta ba ta dena bugawa ba.

"Ki na nufin ki ce Areef ɗanki ne?" Yaya ta tambaya tana kallan Mommah da jajayen idanunta.

"Ƙwarai kuwa Yaya.." Girgiza kai Yaya ta shiga yi wasu hawaye na kwarayowa a kan kuncinta. Tabbas ikon Allah ya wuce gaban wasa. Areef ɗan Sa'adah ne ba ɗan Salma ba? Wannan wace irin rayuwa ce? Wane irin yankan ƙauna ne aka musu haka? Wace irin zuciya Mom ke da ita? Se ta saka hannunta ta ɗauke hawayen fuskar tata, kafin ta ɗaga idanunta ta sauke su a kan Bad Man. Se ta masa alama da hannu a kan ya taho. Kafin ma ya taho ɗin ita har ta ƙaraso ta rungume shi cikin tsananin farin ciki. Sun kai wajen second 30 a hakan kafin ta ɗaga kai ta kalli Didi da ke kallansu kamar wata sokuwa. Ta sakar mata murmushi kafin ta mata alama da hannu a kan ta zo. Se da ta kalli Mommah, ashe ita take kalla, ta jinjina mata kai tana murmushi. Cike da sassarfa ta ƙarasa inda Yayar take. Hannunta ta kamo ta jata cikin jikinta, ta haɗa su ta rungume. Sosai jikkunansu suka haɗu waje ɗaya saboda rungumar da Yayar ta musu wanda hakan ya tilastawa bugun zuciyar kowannensu ƙaruwa. Se dai kafin su ankara ma se ji suka yi ta kamo hannayensu ta sanya cikin na juna, bayan ta sake su. Ta riƙe da hannu ɗaya tana ɗaga kai ta kalle su. Gaba ɗaya hannun suka bi da kallo musamman saboda wani baƙon al'amari da ya ziyarcesu. Musamman Bad Man da ya ji wani yarr tun daga ƙasan ƙafarsa har tsakiyar kansa, wanda hakan ya tilasta masa lumshe idanunsa. Ita kam Didi ji take kamar ta janye hannayenta se dai ta bar shi.

"Allah Ya kawo zaman lafiya a tsakaninku.. Ya kauda idanun maƙiya a kanku.. Allah Ya kawo muku farin ciki me ɗorewa a rayuwar aurenku.." Ta ƙare tana murmushi. Addu'a sosai Yaya ta musu kafin ta sakar musu hannayen ta koma ta zauna. Mamakinsa ne har yanzu ya kasa barinta, ta san da a da ne da tuni ya janye hannunsa, se ga shi duk da ta sake su amma ya ƙi sakar mata hannu. Ya kuma ƙi kallanta, kuma ya ƙi bata damar janye nata hannun. Toh kenan me ye ya chanja shi haka cikin ƙanƙanin lokaci? Ta saƙa hakan cikin ranta tana sake ƙoƙarin zame hannunta cike da fatan kar Mommah ko Yaya su gani. Ya wani maaze kamar ba shi ya riƙe hannun ba, ya kuma ƙi kallanta, se ma wani babbasarwa da yake yi tamkar be riƙe komai ba. Jin da ya yi ta ƙi haƙura da janye hannun ya sanya shi cikawa daidai lokacin da ya faki idanunsu su duka ya saka ƙafarsa ya ɗan taka ƙafarta da ta fi kusa da shi. Taɓe baki ta yi tana ji kamar ta yi kuka, shi kam yau muguntar shi ta tashi shi ne yake ta gwada mata. Ta sunkuyar da kai ƙasa tana murza yatsun hannunta. Sarai Mommah na lura da abin da ke faruwa tun ɗazu, ta jinjina kai a ranta tana ganin lallai lokacin da take jira ya zo ya zo mata a daidai. Ya kuma zo mata a lokacin da take da damar yin wani abu.

Tun da ta gama ba su labarin se hankalinta ya sake tashi, gaba ɗaya se ya tafi kan ɗayan yaron nata da takamaimai ba za a ce ga inda yake ba. Hatta bugun zuciyarta da ke fita ba a daidai ba yanzun se ya fi ɗazun fita da sauri. Har ga Allah tsoro take ji, tana tsoro ka da garin son zuciyar Mom ta salwantar mata da rayuwar yaro. Se ta girgiza kai tana ɗaukar wayarta ta danno number Daddy. Ringing 1_2 ya ɗaga wayar. Se da ya fara tambayar jikinta kafin tace

"Yallaɓai ka yi haƙuri.. Hankalina ba ze taɓa kwanciya ba idan ban ganni cikin gidan marayun nan ba.. Duk da a waje suka yar da shi Yallaɓai na kasa dena tunanin samunsa a cikin gidan.. Gaba ɗaya hankalina na can.." Mom ta faɗa muryarta a raunane. Daga can ɓangaren cike da tausayawa Daddy yace

"Kar ki damu Rankiyadaɗe.. ku shirya zuwa an jima da kaina zan kaimu can ɗin.. Na ɗauka da ma ko za ki buƙaci hutu ne a yau ɗin shi ya sa na bari se gobe.. amma tun da ba za ki iya ba ku shirya kawai." Murmushi Mom ta yi kafin ta amsa da

"Na gode sosai Yallaɓai." Daga haka ta katse wayar.

"Tashi maza mu wuce Sa'adah.. Hankalina ya daɗe da tafiya gidan marayun can.." Yaya ta faɗa tana miƙewa duk da yanda jikinta ke a sanyaye bayan gama jin labarin abin da ya faru.

... A zaune yake kan gadon ɗakin nasa, kishingiɗe jikin bangon hamshaƙin gadonsa, idanunsa a lumshe, ya yin da gefensa wasu kwalabe ne guda 2 zube. Ɗaya kuma na hannunsa ya riƙe se dai be kai ga buɗeta ba. Gaba ɗaya ya rasa sukuni tun ɗazu, zuciyarsa tafarfasa take yi. Ɓacin rai ke sake taso masa a duk lokacin da ya tuna da abin da ya faru. Babu abin da ya fi ɗaga masa hankali, ya kuma fi ɓata masa rai irin idan ya tuna tsayin shekarun da ya ɗauka ba tare da gane cewar muguwa ce yake tare da ita ba mahaifiyarsa ba. Wata mace ce yake ɗauka a matsayin mahaifiyarsa, matar da babu ko ɗigon tausayi a cikin zuciyarta, matar da babu imani a lamuranta se tsantsar son zuciya da rashin tsoron Allah. Matar da ya zauna yana mata biyayya duk dan a tunaninsa mahaifiyarsa ce. Ta saka shi ya yi, ta hana shi ya yi. Ashe be sani ba ita ce babbar maƙiyyiyarsu a rayuwa, ita ce wadda ta tarwatsa farin cikin wadda ta haife shi. Ta kuma tarwatsa wannan sunan da za a din ga kiransu da shi na 'En biyu' ta hanyar watsar da ɗayan jaririn, shi kuma ta riƙe shi. Wannan wace kalar rayuwa ce? Ya kasa jurewa, duk yanda ya so tausar zuciyarsa a kan kar ya sha komai hakan ya citira. Dan haka ya ɓalle murfin kwalbar ko tsayawa ya tsiyaya cikin cup be yi ba ya kafa kwalbar cikin bakinsa ya shiga sha a gaggauce. A hankali Mommah ta tura ƙofar ɗakin ta shiga. Idanunta a kansa suka fara sauka lokacin da kwalbar ke cikin bakinsa. Haka kurum ta ji wani irin tsoro ya ziyarceta. Cikin sauri ta juya bayanta ta kalli Didi da ke tsaye tana jiranta. Sam hankalinta ba ya wajen yana kan Little da ke ta tsalle tsallensa tana riƙe da hannunsa. Se ta ƙarasa zuwa cikin ɗakin duk da yanda ƙafafunta ke son bijirewa.

"Areef.." Mommah ta faɗa tana kallansa cike da tashin hankali, da kuma tsoro. Zazzaɓin da ɗazun ya soma rufeta yanzun ya soma dawowa, wanda hakan ya tilastawa jikinta soma rawa. Idanunta har lokacin a kansa tana fatan ya buɗe idanunsa ta fahimci ba abin da take tunani ba ne. Se dai cikin ƙanƙanin lokaci ya ajje kwalbar a gefensa yana buɗe lumsassun idanunsa da suka yi jajur kamar garwashi. Wani kalar lumshewa suke yi da kansu kamar wanda yake sane yake yi. Be tsammaci ganin Mommahn a irin wannan lokacin ba, dan haka da sauri ya gyara zamansa, ya tashi zaune daga kishingiɗen da yake ya sake sauke idanunsa a kan Mommah. Cikin dakushashshiyar muryarsa ya buɗe baki da ƙyar yace

"Mommah..." Ya ƙare yana lumshe idanunsa.

"Me kake yi haka Areef?" Ta yi ƙarfin halin tambayarsa idanunta a kansa cike da tsoro. Ya san Mommahn ta riga ta gan shi babu wani ɓoye_ɓoye. Ko da ma ba ta gan shi ba waɗannan kwalaben da ke zube sun isa su nuna abin da yake yi. Mommahn ta fahimci abin da yake yi ta tambaya ne kawai dan tabbatarwa. Se dai kuma a wanne hali za ta tsinci kanta bayan ta ji da gasken wani abun yake sha. Shin ya za ta ji ranar da ta gano ɗanta kuma ta same shi mashayin giya? An ya kuwa ya yi wa Mommahn adalci? Ya tambayi kansa. Kawai se ya girgiza kai, yana sake jin yanda ƙirjinsa ke masa zafin da har yanzun ya ƙi raguwa.

"Mommah na kasa jurewa.. na kasa jurewa, zuciyata zafi take min Mommah.. Idan ban sha wani abun ba zuciyata za ta iya tarwatsewa."
Chapter 80 · 0% Book details