← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 122

Sashe 11

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ko dai abin da muke tunani ya faru shi ya sa aka yi saurin ɗaura musu aure?" Hero ya faɗa yana haɗe babban ɗan yatsansa da na uku ya murza. Kallansa Ladi da Abida suka yi jin abin da ya faɗa. Kamar kuma wanda ya tuna wani abu, se ya girgiza kai yana faɗin

"Kai.. anya kuwa?"

"Ƙwarai kuwa.. ko dai hakan ne ya faru? Ina tunanin hakan ni ma.." Ladi ta faɗa. Sake girgiza kai Hero ya yi yace

"Toh ba haka ɗin ba ne kenan.."

"Kamar ya ya? Ban gane nufinka ba.." ta tambaya tana kallansa.

"Tunda dai har zan iya hasashen abu, ke ma kuma ki yi, toh mutane da dama ma abin da ze zo kansu kenan.. Kin ga kenan cikin lokaci ƙanƙani za a ramfosu, a gano abin da ya faru. Ba haka ba ne. Abin da kuma ya sa nace ba haka ne ba, idan da hakan ne ya faru ba za a yi saurin ɗaura musu aure ba, dan kuwa kowa ze gano dalilin yin auren.." Shiru Ladi ta yi tana sake jinjina kaifin ƙwaƙwalwa irin na Hero. Tabbas ta yadda da zancensa ɗari bisa ɗari. Hakan ne ya sanyata faɗin

"Uhmm, lallai wannan maganar taka abar dubawa ce.."

... "Jadwa! Jadwa!!" Mami ke ta ƙwalawa kira tun shigowarta gidan. Da sauri Jadwa ta fito, cike da mamakin kiran Mamin.

"Maza ke ki shiryo ki zo na aike ki gidan Lulu.."

"Lulu kuma? Me zan yi mata?" Ta tambaya har lokacin dai cike da mamaki.

"Cewa na yi ki je ki shiryo.. Yaya yace ka da wanda ya je gidan cikinmu.. ina dai ke yarinya ce ai koh? Dan haka je ki shirya zan baki saƙo zuwa wajenta.." Neman waje Jadwa ta yi ta zauna tana taɓe baki da fuska. Tace

"A'ah ni wallahi, babu inda zan je Mami. Tunda dai an samu Kaseem be auri Didi ba ai shi kenan, mu zo mu nemo mafitar yanda ze yi ya so ni.. Ina ruwanmu da wata Lulu kuma don Allah..?"

"Kee Jadwa.. Lulu fa nake miki magana ko ba ki gane ba ne? Shin ba ki ga gidan da aka kaita ba ne? Ki na nufin na yi shiru ta zauna a wannan gidan kamar wadda ba ta da dangi? Toh wallahi ba za ta zauna ba, ko ta halin ƙaƙa se ya saketa ta baro gidan nan in dai ina raye.. Ai Lulu ba kalar gidan nan ba ce, ba matar talakawa ba ce. Ni nan zan tsaya mata.."

"Wai Mami kin manta ni ce ɗiyarki ba Lulu ba?" Jadwa ta faɗa tana kallan Mami, jin wannan magana da take faɗa.

"Ke na sani mana. Duk da dai na san ba zan so ta auri wanda ya fi wanda za ki aura kuɗi ba, amma ai ba zan so ta zauna a wannan gidan ba, gwara ya saketa ta samu wani ta aura.."

"Toh idan kuma ta auri wanda yafi Kaseem ɗin kuɗi fa?" Jadwa ta faɗa tana gyara zama. Girgiza kai Mami ta yi tace

"A'ah hakan ba ze faru ba. Za dai ta samu wani me rufin asiri ne ta aura, amma ba wanda ya fi Kaseem ba.." Matsawa kusa da ita Jadwa ta yi tace

"Ai Mami so nake ki ƙaddara idan hakan ta faru ya za ki yi?" Shiru Mami ta yi na tsawon sakanni kamar ba za tace komai ba, se kuma can tace

"Se na san abin yi mana.." ta faɗa tana miƙewa ta ɗauki jakar da ta ajje a gefenta.

"Ah toh ai Mami abin da nake tsoro kenan. Dan wallahi a kyau dai irin nasu Lulu, babu wanda ze gansu ya ji basu masa ba.." Tsaki Mami ta ja cike da jin haushin abin da Jadwan ke faɗa. Tace bayan ta juya ya kalleta

"Ki min shiru haka nan.. Se abu ya faru sannan ake nemo mafita.. saboda haka ki bar ni yanzu na san yanda zan kuɓutar da ɗiyata daga wannan gidan.." Daga haka ta shige ɗaki. Binta da kallo Jadwa ta yi kawai, ta ma rasa abin da za tace, se kawai ta koma kan kujera ta zauna ta cigaba da danna wayarta.

.. A hankali ya tura ƙofar ɗakin, ga mamakinsa yanzu ma tana bakin ƙofar, se dai yanzu kanta ba ɗore yake a kan cinyarta ba. Idanunta gaba ɗaya suna kan ƙofar ne, jira kawai take ta ji sallamar Mami. Tana ji ya turo ƙofar ɗakin, ta ɗaga kai da sauri ta kalli ƙofar. A kan fuskarsa idanunta suka fara sauka. Cike da takaici ta ɗauke kai, tana sake jin haushin ganinsa da take ta yi tun jiya. Dab da ze giftata ba tare da yace komai ba. Se kuma ya dakata, ya ɗan lumshe idanunsa sannan yace ba tare da ya kalleta ba

"Ki je ku gaisa da Ummeey.."

"Wace Ummeey?" Ta tambaya da sauri, dan a tunaninta ko mantawa ya yi ze ce Mami yace Ummeey. Kamar ba ze tanka ba, se kuma ya ga rashin dacewar hakan, hakan ne ya sanya shi faɗin

"Mahaifiyata.." Daga haka ya yi cikin ɗakin. Ya ɗauki abin da ze ɗauka kana ya taho da niyyar fita. Be ɗauka ze ganta a zaune kamar yanda ya barta ba, se dai be san tunda ta ji ya ambaci sunan wata ba Mami ba ta ji kamar ta tashi ta rufe shi da duka. Me ye haɗinta da babarsa da za ta je ta gaesheta, bayan kawai ta zauna a gidan ne kafin Mami ta zo su tafi? Ita har ga Allah ma ta gaji da jiran Mamin, haƙurinta na dab da ƙarewa a kan rashin ganinta da ba ta yi ba tun da gari ya fara haske. Kwantacciyar sumar dake shimfiɗe a kan fuskarsa ya ɗan shafa kaɗan, kafin a hankali ya sake kallan inda take. Se kace wata me aljanu idan tana wani abu.

"Ke.." ya faɗa yana kallanta. Daga inda take ta murguɗa baki tana hararar gefe, a fili se dai ƙasa ƙasa tace

"Ko ina ruwan mutum da ni oho masa. Shegen shishshigi kamar me.." Jin yana ƙoƙarin sake faɗin wani abun ya sanyata saurin miƙewa tace ba tare da ta kalle shi ba, dan ta san ba za ta iya kallansa ta faɗa masa abin da take da niyyar faɗa ba.

"Ni don Allah ka ƙyale ni. Wai ina ruwanka da ni ne? Me ye haɗina da kai da zan je gaishe da en gidanku? Don Allah ka ƙyale ni. Mami kawai nake jira ta zo mu bar muku gida." Da mamaki yake kallanta jin abin da take faɗa. Se kuma ya taɓe baki, yana girgiza kai har wani murmushi na suɓuce masa. Lallai Afaaf ɗin ba ta san waye shi ba. Yana ganin mutuncin mahaifinta ainun, se dai hakan ba shi ke nuna ze shanye duk wani rashin daraja da za ta yi ba. Ƙiris yake jira ya taka mata birki a kan duk wani hali nata. Duk da be san yaya zamansu ze kasance ba, amma tabbas ze taka mata birki, ze saita mata wannan rashin kunyar da take ji da shi. Dan ya ga alama ba za ta biyu ta daɗin rai ba, burin Abbanta kuma ba ze taɓa cika ba na gyara masa Afaaf ɗin matuƙar yace ze cigaba da binta a yadda take ɗin nan.

"Ka da na dawo na same ki a bakin ƙofar nan.. Gida kuma se an zo tafiya dake za ki tafi? Ba ki ga ƙofar ɗakin a buɗe take ba, ga hanya nan maza zo ki fice.. Ni kuma za ki dawo ki same ni.." Ya ƙare maganar a nutse, kai ba za ka taɓa cewa cikin fushi yake maganar ba, saboda tantagaryar nutsuwar dake cikin muryarsa. Daga haka ya soma takawa dan ficewa daga ɗakin.

"Ai dai nan ɗin ba gidanmu ba ne, muna da gidanmu kuma ba na buƙatar na kowa." Ta faɗa da ɗan ɗaga murya dan ya ji ta. Be bi ta kanta ba, se cigaba da takawa da ya yi. Har ya fita, se kuma ya dawo, ya watsa mata kyawawan idanunsa dake cikin fushi yace

"Na dai faɗa miki.. Kar ki bari na dawo na same ki a bakin ƙofar nan, idan ba haka ba zan baki mamaki.." Bin wajen ta yi da kallo ranta a ɓace. Shin wai me mutumin nan ke nufi da ita ne? Me yasa yake son takurawa rayuwarta dan kawai an ce an aura masa aurenta? Auren da a yau ɗin nan take da tabbacin ze ƙare. Ko ma hakan ne me ye haɗinsa da ita? Ya yi rayuwarsa ta yi tata mana. A yi mutum se neman magana da shishshigi? Ƙwalla ta ji ta taso mata a cikin idanunta. Se ta nemi waje ta zauna a wajen tana faɗin

"Kuma bakin ƙofa ne se na zauna. In ga me hana ni.." Ko minti ɗaya ba ta yi da zaman ba, se jin motsin ƙofa ta yi kamar za a buɗe, ai ba ta san sanda ta miƙe da gudu ba ta yi cikin ɗakin, lokaci ɗaya tana faɗin

"Kuma ba dan kai na dawo ɗakin ba.." ta faɗa tana hararar ƙofar ɗakin. Ga mamakinta ma se ta ji shiru, ashe ba shi ba ne, duk da haka se ba ta koma bakin ƙofar ba. Ta cigaba da zama a ɗakin tana jiran zuwan Mamin. Se dai lokaci na cigaba da ja babu Mami babu alamarta. Anya kuwa ba ta yi kuskuren zama jiran Mami ba? Me yasa har yanzu Mamin ba ta zo ba? Ta sakata ta haƙura ta kwana a gidan, ba tare da fitowa fili ta nuna tsanarta ga Gwani ba, amma har yanzu babu wani sauyi? Ita ga shi ba waya ba ballantana ta kira Mamin ta ji lafiya? Komawa ta yi ta zauna tana ƙiyasta adadin mintunan da ta ƙarawa Mamin, waɗanda idan dai har suka cika Mamin ba ta zo ba toh za ta aikata abin da zuciya ke raya mata.

.. "Ke ashe dama en biyu ne yaran nan amma ba ki faɗa min ba?" Hero ya faɗa yana kallan Abida a fusace. Zaro ido ta yi kafin tace
Chapter 11 · 0% Book details