← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 122

Sashe 78

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haka ne abin da Maimuna ta faɗa.. Se dai wallahi ba mun yi hakan ba ne dan wani abu.. se dan soyayyar da muke masa.. Kuma tun da muke ba mu taɓa cutar da shi ba, dan ba ƙiyayya ce ta saka mu ɗaukarsa ba tsantar soyayya ce.. da.." Wata wawuyar tsawa da Bad Man ya dakawa Aunt Makiyy ita ce ta dakatar da ita ƙarasa abin da ta soma faɗa. Take jikinta ya ɗauki rawa cike da tsoro. Shi kansa saboda tsabar yanda ɓacin rai ke tare da shi har rawa jikinsa yake yi. Idanunsa sun sake rinewa sun yi jajur, fuskar nan ta haɗe irin haɗewar da ban taɓa ganinta ba. Kallo ɗaya za ka masa ka tabbatar da tsananin ɓacin ran da yake ciki. Kamar ba ze ce komai ba se kuma ya ɗaga yatsansa ya nuna Aunt Makiyy muryarsa na fidda wani irin amo ya soma faɗin

"Kuuulll!! Kar na sake jin kin ambaci soyayya a wajen nan, idan ba haka ba daga ke har yayar taki zan lahantaku.." Ya ƙare yana sauke numfashi. Wanda hakan kaɗai ya isa ya nuna maka abin da yake faɗa tun daga ƙasan zuciyarsa yake fitowa. Tun kuwa da ya buga mata wannan tsawar ba ta sake ko da yunƙurin cewa wani abun ba ne. Se ƙasa ma da ta yi da kanta tana ji kamar ta tashi ta fice daga ɗakin. Ita kam Mom suman zaune ta yi, kukan da take yi ya tsaya cakk, jikinta ya sake ɗaukar rawa. Tana ji a jikinta tabbas yau ƙarshenta ne ya zo. Ban da haka ya ya za a yi Makiyya da kanta ta tona mata asiri? Se dai ba ta san ita Aunt Makiyy ta yi hakan ne dan nemawa Mom ɗin mafita ba saboda jin abin da Daddy ya faɗa. Dan ta riga ta san halin er uwatta na taurin kai da ƙeƙashashshiyar zuciya, ko me ze yi ba za ta amsa laifinta ba. Shi ya sa ta ga kamar hakan ne kaɗai ze sanya a fahimce su, musamman idan ta yi amfani da kalmar soyayya. Se dai kamar ba haka ba ne. Neman waje kawai Daddy ya yi ya zauna cike da tsananin mamaki da kuma takaici. Duk da tun ɗazun zuciyarsa ta yadda da abin da Maimunan ta faɗa, amma ko babu komai yana da kyau ya ji ta bakinsu. Shi ya sa yanzu da ya ji maganar daga bakin Aunt Makiyy abin ya fi taɓa shi da yawa. Ashe be sani ba yana zaune ne da mara imani. Muguwa mara tausayi, wadda za ta iya yin komai saboda son zuciyarta. Mace me zuciyar kafirci, wadda babu ko ɗigon tausayi a cikin ranta. Macen da za ta iya raba uwa da 'ya'yanta tun ranar da suka zo duniya, ta ɗauke ɗaya, ta saka a salwantar da rayuwar ɗaya? Wannan wace irin mace ce? Wane irin rashin imani ne wannan? Wanne irin kishi ne wannan na jahilci?

"Zo Areef.. Zo na rungumeka ko na samu sassaucin abin da nake ji cikin zuciyata.." Mommah ta faɗa tana kallansa lokacin da idanunta har wani dishi dishi take gani saboda hawayen da ya cika su. Har wani tangaɗi yake yi lokacin da yake ƙarasawa inda Mommahn take. Shi kansa mamaki ya kasa barinsa. Shin me ya kamata ya yi? Kuka ko kuwa me? Babu ɓata lokaci yana ƙarasawa inda Mommah take ta rungume shi tsam cikin jikinta. Ba ta san lokacin da wani kuka me sauti ya ƙwace mata ba. Tabbas Areef ɗin jininta ne. Se yanzu ne ta fahimci dalilin wata irin soyayya da take masa. Se yanzu ta gane dalilin kasa dena sonsa tun yarinta duk da irin rashin kirkin da Mom ke mata. Se yanzu ta gane dalilin da ya sa take jinsa a can ƙasan ranta. A da ta yi tunanin ko dan ba ta da ɗa ne shi ya sa hakan, dan ba ta taɓa kawo hakan kan kasancewa ba. Se yau ta fahimci ashe dalilin kasancewarsa ɗa a gareta shi ne dalili ba komai ba. Ta sake rungume shi, tana jin wata sabuwar ƙaunar Areef ɗin na ratsata. Soyayyar uwa da ɗanta ta shiga ratsa kowannensu. Shi kansa se yanzu ne ya fahimci dalilin da ya sa yake son Mommahn tun tashinsa, yake kuma san komai nata. Duk kuma da yanda Mom ke hana shi zuwa wajenta da kuma hana shi alaƙa da ita ya kasa. Ashe ashe mahaifiyarsa ce. Ita ce ta tsuguna ta haife shi. Sun kai wajen minti 2 a hakan kowa da abin da ke cigaba da tsarawa cikin ransa kafin Mommah ta sake shi. Hannunta cikin nasa ta kamo shi ta zaunar da shi gefenta, tana jin wani matsanancin farin ciki na ratsata. Se dai gefe guda kuma wata fargaba ke ziyartarta. "Ina ɗan uwan Areef?" Tambayar da ta fara zuwar mata kenan, wadda ta tilastata kallan Daddy daidai lokacin da ya soma faɗin

"Kin raba uwa da 'ya'yanta a ranar da ta haifesu. Kin ɗauke ɗaya kin riƙe ba tare da sanin ɗanta ba ne. Hakan be ishe ki ba, maimakon ki bar mata ɗayan a'ah.. tsananin kishi da rashin imani ya hanaki, se da ki ka ɗauke shi ki ka sanya aka je aka salwantar da rayuwarsa.. Toh ki sani matuƙar na yi bincike ban samu yaron nan ba wallahi se na yi shari'a da ke.."

"Don Allah ka yi haƙuri sharrin shaiɗan ne wa..." Hannu Daddy ya ɗaga mata yana sake jin wata kalar tsanarta na ratsa shi. Fuskarsa a haɗe, muryarsa a cunkushe yace

"Na kuma sake ki saki 3.. Ki kuma jira hukuncin da za a miki na wannan laifi da kika aikata.. ba ma ke kaɗai ba, da duk wani wanda ya taimaka miki kika aikata.." Shiru Mom ta yi bayan jin abin da Daddy ya faɗa. Kamar ta ji abin da ya faɗa kamar kuma ba ta ji ba, se ta yi shiru tana sake tunano abin da ya faɗa ɗin. Saboda tsabar ruɗewa jikinta banda ɓari babu abin da yake yi kamar wadda zazzaɓi ya rufe. Wata ƙara da ta saki ita ce ta sanya Aunt Makiyy riƙota da sauri. Ai ba ta bi ta kanta ba ta sake sakin ƙarar a karo na barkatai

"Na shiga 3 na lalace.. Na shiga 3.. Saki kuma? Shi kenan burin Maimuna ya cika.. Na shiga 3, ta gama da ni.. wayyo Allahna na mutu na lalace." Kwatankwacin kalaman da Mom ta cigaba da furtawa kenan cikin ficewar hayyaci. Aunt Makiyy ta riƙota tana kuka ita ma tana kuka. Maimuna ma da ke gefe kuka take na fitar hankali. Nadama da danasani har yanzu su take yi. Kai ba ma ita kaɗai ba, Talatuwa kanta Maimunan take tayawa kuka. Dan ta san duk da ta yi nadama hukunci kam se ta karɓe shi, dan abin da suka aikata ya yi munin da za a iya barinsu su tafi a haka ba tare da wani hukunci ba. Wayarsa Daddy ya ɗaga ya yi kira na tsawon minti 1 sannan ya ajje wayar. Ya kalli Bad Man da idanunsa ke a lumshe. Har lokacin ya kasa yadda ba mafarki yake yi ba. Wannan abu ya ɗaure masa kai fiye da tunanin me tunani. Ashe shi ɗin en biyu ne? Toh ina abokin tagwaitakar tasa? Ko kuwa garin son zuciyar matar da ya ɗauka a matsayin uwa shekara da shekaru ya saka ba ze san inda yake ba?

"Kama mahaifiyarka ka kaita daƙi.. Zan shigo zuwa an jima." Se a lokacin ya buɗe idanunsa da suka yi kama da na me jin bacci. Ya miƙe jikinsa a sanyaye ya miƙawa Mommah hannunsa a tausashe kamar ba shi ba yace

"Mommah.." Se ta ji kamar yau ɗin wani suna daban ya faɗa mata. Duk tsawon lokacin da ya ɗauka yana kiranta da wannan sunan ba ta taɓa jin sunan ya yi kama da na wadda ta haife shi ba. Se a yau se ta ji yana faɗa hakan ya yi mata kama da ita ce mahaifiyarsa. Kamar kuma a ranar ya fara kiranta da sunan haka ta ji. Ta lumshe idanunta har lokacin bugun zuciyarta be saitu ba. Kama hannun Bad Man ɗin ta yi ta miƙe har lokacin kanta be bar sara mata ba. Dab da za su fice daga ɗakin Mommah ta dakata, abin da ke cikin ranta ta kasa barinsa, gwara ta magantu ko za ta samu nauyin da ke ƙirjinta ya ragu. Se dai kafin ma tace komai Maimuna ta soma faɗi cikin kuka.

"Don Allah Hajiya kar ki bar ɗakin nan ba tare da kin ce kin yafe min ba. Tabbas abin da muka aikata miki mafi muni ne, se dai ni kam na tuba.. dan tun a gidan duniya na fara ganin sakayya, daga wannan masifar se waccan.. ki taimaka min don Allah.." Murmushin yaƙe Mommah ta yi kafin ta soma faɗin

"Duk da na san ba yina kike ba Maimuna.. Se dai ban taɓa tunanin za ki iya aikata min haka ba, duba da cewar babu abin da na miki a rayuwa, se ga shi kin min abin da har na mutu ba zan manta ba. A lokacin da kika yarda kika aikata wannan aikin ba ki yi tunanin wannan ranar za ta zo ba ba se yanzu ɗin da ta zo?" Ta dakata a nan tana girgiza kai, tana kuma jin ɗaci har cikin ranta. Kafin ta maida dubanta kan Mom da har lokacin take surutai duk saboda yanda sakin da Daddy ya mata ya girgizata.
Chapter 78 · 0% Book details