← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 122

Sashe 42

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki koma ki kula da gidan kafin mu dawo" Mommah ta faɗa tana kallan Atine

"Toh Hajiya se kun dawo, Allah ya tsare."

"Ameen.." Mommah ta faɗa sannan ta juya dan zuwa sashen Daddy. Dakatawa ta yi tana kallan lokacin da Daddyn yake ƙarasowa inda take masu tsaron lafiyarsa na bayansa. Daga nesa suka tsaya lokacin da ya kusa isowa inda Mommah take. Se ta saki nurmushi me ƙayatarwa lokacin da ya iso inda take.

"Barka da wannan lokaci Rankayadaɗe.."

"Barka dai Rankiyadaɗe"

"Wajenka nake son zuwa se kuma ga ka a nan."

"Ehh zan ɗan fita ne."

"Toh madallah.. Allah Ya taimaka, Ya kuma tsare." Ta yi maganar cikin kulawa.

"Ameen.. akwai wani abun ne?"

"Ehh Afrah ce ta taaka kwalba shi ne zan kaita asibiti a duba ta."

"Subhanallahi.. kwalba kuma?"

"Wallahi kuwa Rankayadaɗe."

"Tana ina?" Daddy ya tambaya. Nuna motar da Didi ke ciki Mommah ta yi tace

"Tana ciki.."

"Mu je na ganta." Daddy ya faɗa lokacin da ya soma takawa zuwa wajen motar. Babu musu Mommah ta bi bayansa har zuwa wajen motar. Cikin kulawa ya dube ta yace

"Sannu koh Daughter?" Bata lura da tahowarsu ba se maganarsa da ta ji. Aikuwa tana ganinsa se ta soma ƙoƙarin buɗe motar dan fitowa daga ciki.

"A'ah yi zamanki ba se kin fito ba.. ya ƙafar taki?"

"Da sauƙi Daddy.. Barka da wannan lokaci.." ta yi maganar lokaci ɗaya.

"Barka dai.. Allah ya ƙara sauƙi." Daddy ya amsa da hakan. Daga haka ya matsa inda Mommah take yace

"Shi Areef ɗin baya nan ne?" Girgiza kai Mommah ta yi tace

"A'ah ban sani ba dai ko yana ciki.." Daddy be ce komai ba se ɗauko wayarsa da ya yi ya kira number Bad Man. Yana tsaye bakin mirror yana feshe jikinsa da turaren nan nasa me daɗin ƙamshi ya ga kiran Daddyn. Be kawo komai ba ya ɗaga wayar. Bayan sun gaisa Daddy yace

"Ka na cikin gida ne?"

"Ehh.."

"Ina parking space ina jiranka.."

"Ohk.." ya amsa da hakan yana ajje wayar. Ƙarasa shiryawa ya yi sannan ya fito daga ɗakin. Kai tsaye can ɗin ya nufa. Tun kafin ya ƙarasa ya hangi Daddy da Mommah a tsaye. Da farko be kawo komai ba, se kuma daga baya zuciyarsa ta soma raya masa ko dai yarinyar nan ta je ta faɗa musu abin da ta gani a ɗakinsa? Anya kuwa hakan ze faru bayan duk gargaɗin da ya mata? Ƙwafa ya ja yana ɗan cijar leɓensa gami da lumshe sexy eyes ɗinsa kafin ya buɗe su lokaci guda. Duk da abin da zuciyarsa ke raya masa hakan be hana shi sakarwa Mommah da ya fara tozali da fuskarta murmushi ba. Ita ma maida masa ta yi tana faɗin

"Areef.."

"Yes Mommah.. Good evening.."

"Ka na lafiya?" Ta faɗa har lokacin da murmushi a kan fuskarta. Jinjina kai kawai ya yi yana maida dubansa kan Daddy yace

"Daddy.."

"Areef.." Daddy ya faɗa yana kallansa. Ɗaga idanunsa ya yi ya kalli Daddyn dan jin abin da ze faɗa. Se kuwa Daddy ya soma faɗin

"Yanzu ku na gida ɗaya, sashe ɗaya amma a ce matarka ta taka kwalba ba ka sani ba?"

"Kwalba?" Ya maimaita kamar yanzu ya taɓa jin sunan.

"Ta tabbata ba ka sani ɗin ba kenan?" In ji Daddy. Ɗan yin shiru ya yi kamar yace ehh be sani ba, se kuma ya ga rashin dacewar hakan, musamman yanda ya san ran Daddyn ze sake ɓaci ne idan ya ji haka. Hakan ne ya sanya shi faɗin.

"No Dad.. na sani."

"Yah Allah!!" Daddy ya faɗa yana ɗan fesar da iska daga bakinsa kafin ya ɗora da

"Shin ba ka san illar kwalba ba ne ko kuwa rashin kirki ne irin naka da ya hana ka ɗaukarta ka kai ta asibiti a duba ta?" Shiru kawai ya yi dan ba shi da amsar bayarwa.

"Toh ga ta nan cikin mota ka shiga ka kaita a duba mata ƙafa. Wai Areef ba ka tunanin Allah ya kama ka a kan haƙƙin yarinyar nan ne?" Daddy ya faɗa cike da mamakin taurin kai irin na Areef ɗin.

"But Dad akwai.."

"Ban son jin komai idan ba toh ba." Daddy ya katse shi ta hanyar faɗin hakan da kuma amfani da hannunsa wajen dakatar da shi.

Mommah ji take kamar ta cewa Daddyn ya bar Areef ɗin ita za ta kai Didin asibiti. Se dai ta yi shiru ta bar shi. Ta san halin Areef ɗin dama ba me iyawa da shi se Daddyn. Duk taurin kansa idan aka ce Daddy ne ya yi magana toh fa ko ba ya so ze yi shi. Shiru na en wasu sakanni kamar ba ze tanka ba se kuma can ciki ya furta

"Ohk.." fuskar nan ba yabo babu fallasa. Key ɗin motar Mommah ta miƙa masa, be ce komai ba ya karɓa ya wuce zuwa inda motar take. Kai tsaye ya shiga cikin motar ba tare da ya kalli ko da inda take zaune ba ne. Gaba ɗaya ta ɗauka da Mommah za su je asibitin, se dai ganin mutum cikin motar ya sanya ta tunanin ko Mommahn ta fasa ne shi ya sa ta aiko wani ya kaita asibitin. Se dai me? Tun kafin ya tayar da motar wannan mayen turaren nasa me shegen ƙamshi ya ziyarci cikin hancinta. Ƙamshin nan me daɗi da ke sanya wanda ya shaƙe shi lumshe idanu. Hakan ce ta faru da Didi, dan kuwa ba ta san lokacin da ta lumshe idanunta ba lokaci guda kuma tana jin bugun zuciyarta ya ƙaru. Har ga Allah tsoronsa take ji, musamman idan ta tuna shi ɗazun nan lokacin da yake shata mata uban gargaɗi. Se ta kame kanta gefe ɗaya tana Allah Allah su isa asibitin ya sauke ta ya juya. Sosai yake gudu kamae wanda ze tashi sama a kan titin. Har suka isa cikin asibitin be ce komai ba. Sauka ya yi daga motar ba tare da yace da ita komai ba. Ta sauke ajiyar zuciya tana saka hannu ta buɗe murfin ƙofar. Sam ta ma manta da ciwon ƙafarta saboda yanda ta tsorata da irin gudun da yake yi. Se da ta saukar da gaba ki ɗaya ƙafafun nata ƙasa ta ji wani azabtar zafi sannan ta tuna, ta ɗage ƙafar da sauri tana faɗin

"Ahhh.." Ya juya ya maka mata wani kallo sannan ya soma takawa. Bin bayansa ta yi a hankali a hankali cike da lura take tafiyar tana ɗan runtse idanunta saboda zafi. A haka har suka isa cikin ainahin asibitin inda za su ga likita.

.. "'Yallaɓai za ka iya shigowa ai." Shi ne abin da wata nurse ta faɗa tana kallan Bad Man, dan sarai ta gane fuskar shi, barinsa kuma a waje tamkar rashin daraja ne. Siririn tsaki ya ja lokacin da ya fahimci zaman be ƙare ba. Kamar yace a'ah se kuma kawai ya shiga cikin ɗakin. Tana zaune a kan wani gado tana kallan ƙafarta da aka sabuntawa bandage. Ba tare da ya kalleta ba ya nemi waje ya zauna yana cigaba da danna wayarsa. Murmushi nurse ɗin ta sakarwa Didi lokacin da ta ƙarasa inda take tace

"Bismillah Madam.." Tsilli_tsilli da idanu Didi ta yi tana kallan nurse ɗin dan sake fahimtar abin da take nufi. Se ta ga tana haɗa allura. Kafin daga bisani ta sake kallanta tace

"Allura zan miki. Kar ki ji komai ba ni da zafin hannu.. ki cire hijab ɗin" Girgiza kai Didi ta yi, ta buɗe baki tace

"Don Allah kar ki min wallahi na dena jin zafi.." ta faɗa cikin sanyin muryarta.

"Haba Madam kar ki ba ni kunya mana.. babu fa zafi.."

"Eh ai na sani.. ni dai Allah kuwa ba na so.." ta sake faɗa tana girgiza kai. Maida dubanta Nurse ɗin ta yi kan Bad Man da har lokacin be kalle su ba tace

"'Yallaɓai ko za ka taimaka mini.. Madam tsoro take ji, ta manta akwai haihuwa a gabanta." Ta yi maganar cikin iyayi tana murmushi. Kallanta ya yi yana jin yanda ta soma ba shi haushi da maganganunta. Yau ɗin kawai ba ya son hayaniya ne shi ya sa be ce mata komai ba. Se kallan Didi da ya yi wadda ta yi tsilli tsilli da ido kamar shege a rabon a gado. Agogon wayarsa ya kalla ya ga yawan mintunan da suka kwasa cikin asibitin, ya sake jan ƙaramin tsaki yana miƙewa ya soma takawa zuwa cikin ɗakin.

"Yawwah.. toh godiya nake.." Nurse ɗin ta faɗa tana murmushi. Da niyyar yi mata magana ya yi a kausashe dan ta nutsu a yi mata. Se dai kuma ya tuna a inda suke, yanda ya ga tun da suka zo wannan Nurse ɗin ke masa ya sa ya fahimci sun san waye shi. Ya kuma san duk abin da ze yi idanunta na kansa ne. Hakan ne ya sanya shi ƙarasawa dab da Didi ya saka hannunsa ya kamo hannunta a nutse. Da sauri ta ɗaga kai ta kalle shi, se ya sakar mata wani murmushi wanda ba ta taɓa ganinsa a kan fuskarsa ba.

"Tsoron me kuma kike ji bayan ga ni?" Ya yi maganar a hankali kamar wanda ba ya so a ji me ya faɗa. I zuwa lokacin kam Didi se ta kaasa ɗauke idanunta daga kansa. A ranta tana tunanin ko dai ya manta wace ce ita? Ko kuwa dai Nurse ɗin yake so ya faɗawa hakan ya manta yake faɗa mata? Tana shirin ƙwace hannunta ta ji ya sake matsowa kusa da ita ya sanya hannayensa duka biyun ya ɗagota daga zaunen da take ya miƙar da ita tsaye. Share yanda take ta ƙoƙarin ƙwace jikinta ya yi ya saka hannu ya ɗage hijab ɗin zuwa kan wuyanta. Jin da ya yi da gasken ƙwace jikinta za ta yi ya sanya shi yi mata masauki cikin jikinsa, ya kuma riƙeta gam ransa na ɓaci. Se dai ya yi ƙoƙarin haɗiyewa kawai. Ƙasa ya yi da kansa se da ya tabbatar ya kai bakinsa saitin kunnenta sannan yace
Chapter 42 · 0% Book details