← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 122

Sashe 79

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Kin cutar da ni.. Kin cutar da rayuwata da ta 'ya'yana.. Kin saka na yi rayuwa tsawon shekaru masu yawa tare da Areef ba tare da na san ɗana ba ne. Ki na saka almakashi ki datse duk wata alaƙa tsakanina da Areef. Sannan kuma kin raba ni da yarona. Wanne hali yake ciki a yanzu duk ba mu sani ba. Shin yana raye? Idan har yana raye yana ina? Wane hali ze shiga idan ya kasance ya gano iyayensa na raye yayin da shi yake can yana rayuwa a wani waje? Babu uwa, babu uba babu dangi? Kin raba ni da shi ba tare da na taɓa jin ɗumin jikinsa ko shi ya ji nawa ba, kin kuma raba mahaifinsa da shi, haka zalika kin raba ɗan uwansa da shi." Mom ta sake dakatawa a nan saboda yanda ranta ke suya, muryarta har rawa take yi saboda yanda take jin maganar da take furtawa har cikin ranta.

"Idan har kun ga na fara tunanin yafe muku toh 'ya'yana sun haɗu ne waje ɗaya suna rayuwa kamar yanda suka rayu a ciki. Idan kuwa hakan ba ta faru ba ku tabbatar za mu tsaya da ku a gaban Allah.." Daga haka ta juya suka fice daga ɗakin. Daddy ya bisu da kallo cike da tausayawa. Maganar da Mommahn ta faɗa tabbas ta tsaya masa a rai, ya kuma sake tirr da halayen Mom. Ajiyar zuciya Ammi ta sauke, ita kam wannan al'amari ya ɗaure mata kai, wannan rashin imani da me ya yi kama. Se ta miƙe a hankali ta kalli Talatuwa tace

"Allah Ya kyauta.."

"Ameen mun gode sosai.. Allah Ya saka miki da alkhairi.. Ki mana addu'a kafin komai ya ƙare ta yafewa Maimuna don Allah.." Jinjina kai Ammi ta yi kafin ta furta

"Tohm.."

"Wace ce wannan?"

"Ita ce ta rako mu gidan nan Yallaɓai tun daga garinmu.." Talatuwa ta bawa Daddy amsa. Se ya jinjina kai kafin yace

"Madallah.. Mun gode.." Ya san Ammin ta kyauta da ta rako su Maimunan gidan nan, dan haka yanzun da Mommah ba ta nan, se ya rubuta numberta jikin wata takarda da niyyar Mommahn za ta kira ta mata godiya. Daga haka suka yi sallama ta fice daga ɗakin. Ba a ƙara minti 10 cikin ɗakin ba waɗanda Daddy ya kira suka iso cikin ɗakin da umarnin Daddyn. Cikin ƙanƙanin lokaci aka kama Mommah da kuma Maimuna zuwa lokacin da za a gama bincike. Mom kuka take har da birgima kamar ƙaramar yarinya, har kuma lokacin ba abin da ta aikata ke damunta ba, a'ah, sakin da Daddy ya mata shi ne ya tsaya mata, ya dugunzuma mata hankali, yake ƙoƙarin sakawa ta fice a hayyacinta, wanda kuma shi ne ya kusan sakata ƙaramin hauka. Ta din ga surutai tana roƙon Daddyn ya janye sakin da ya mata. A haka dai aka fice da ita daga ɗakin ba tare da Daddy yace komai ba. Se dai mamaki ya ƙi barinsa, musamman da ya fahimci inda maganganun Mom ɗin suka dosa, sam kamar hankalinta ma ba ya kan abin da ta aikata se sakin da ya mata. Ya girgiza kai yana sauke ajiyar zuciya kansa jingine da kujerar da yake kai. Talatuwa da Aunt Makiyy babu abin da suke yi se kuka, haka dai suka bar gidan cike da nadama, da danasani duk da ba su suka aikata laifin ba..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO67*

___Se da ya kaita har cikin ɗakinta sannan ya nemi waje ya zauna. Ta bi shi da kallo har lokacin idanunta ba su dena zubda ƙwalla ba. Bayan shuɗewar wasu mintuna Mommah ta katse shirun da ya ratsa ɗakin, dan kuwa shi ya rasa ma me ze ce. Tsananin ɓacin rai ya hana shi aikata komai. Ji yake tamkar mafarki ne, wai matar da ya ɗauka tsayin shekarun nan matsayin mahaifiyarsa ashe ba haka ba ne. Matar kuma da ya ɗauka matsayin kishiyar mahaifiyarsa ashe ita ce ta haife shi.

"Areef.." Se ya ɗaga kai ya kalleta. Ta sakar masa murmushi duk da har lokacin za a iya kiransa da iya kan fuskarta saboda har lokacin ba ta gama fita daga shock ɗin da labarin da Maimuna ya shigar da ita ba.

"Ɗauki wayar nan ka kira min Yayata.. Ka duba numberta za ka ga an saka 'Soeur' ka sanar mata ta zo gidan nan yanzu"

"Tohm." Ya amsa da hakan. Kai tsaye wayar ya ɗauka ya kamo number Yaya ya kira. Babu jimawa ta ɗaga. Be tsaya ɓata lokaci ba ya sanar mata da saƙon Mommah. Haka kawai ta ji tsoro ya kamata, musamman da ta ji ba muryar Mommahn ba. Dan haka babu ɓata lokaci ta shiga shiri. Cigaba da zama ya yi cikin ɗakin dan ya kasa matsawa ko nan da can ne. Zuwa can Mommah ta kalli Bad Man tace

"Taimaka ka kira min Ɗiyata.. Daga yau ta gama zaman kaɗaici In Sha Allah.."

"Shi kenan abin da za a miki?" Ya yi maganar bayan ya matso kusa da kujerar da take kai. Se ta jinjina kai kafin a fili tace

"Ehh.." Se a lokacin ya miƙe ya fice daga ɗakin. Mommah ta bi shi da kallo tana jin wani murmushi na ƙwace mata.

"Allah Ya maka albarka.. Ya bayyana min ɗan uwanka.. Ya sa yana raye cikin ƙoshin lafiya." Ta yi maganar a sanyaye.

A hankali ya tura ƙofar ɗakin, tana kwance kan gadon Little a gefenta yana rubutu cikin wata jotter, ta yi shiru kamar me tunanin wani abu. Daidai lokacin ya shigo cikin ɗakin. Tashi ta yi da sauri ta zauna zaune a kan gadon tana gyara zaman rigar jikinta.

"Uncle.." Little ya faɗa lokacin da ya taso da gudu zuwa wajen Bad Man. Hannu ya saka ya riƙo shi yana ƙaƙalo murmushi yace

"Little.."

"Na'am.." Be sake cewa komai ba se takawa da ya yi zuwa cikin ɗakin, a nutse ya kalleta yace

"Ɗauko hijab ɗinki ki zo mu je Mommah na kiranki." Har ga Allah ba ta san lokacin da ta ɗaga kai ta kalli fuskarsa ba. Kwata kwata kamar ba shi ba. Da ma tun da ya shigo ɗakin se take ganin kamar ba shi ba. Yanzun kuma da ya yi magana se ta yadda tabbas akwai wani abun. Toh me ya dame shi? Ta tambayi kanta tana cigaba da kallansa. Daidai lokacin da ya ɗaga kai ya kalleta, se kuwa ta tsinci idanunsa cikin nata idanun. Ta yi maza ta janye tana jin wata faɗuwar gaba na ziyartarta. Se ya kasa janye idanunsa daga kanta. Ya bita da kallo lokacin da ta ƙarasa bakin wardrobe don ɗaukar hijab. Duk da yanda take ta wani sum sum da kai, tana cakuɗe jikinta waje ɗaya saboda doguwar riga ce kawai a jikinta, hakan be hana shi ganin yanda rigar ta yi wa ƙaramin jikinta me kyawun fasali kyau ba. Se lokacin ta yi saurin zura hijab ɗin tana cuno baki saboda kama shi da ta yi yana kallanta sannan ya lumshe idanunsa yana ɗauke kai cikin basarwa. Se kuma ya kama hannun Little ya fice daga ɗakin. Se a lokacin sannan ta zura takalmi ta bi bayansa, cike da mamakin kiran Mommahn, kuma wai shi aka aiko ya kirata. Ba dai tace komai ba haka ta cigaba da binsa har zuwa sashen Mommah. Se da suka isa palour sannan ta soma yin wajen da kujerun Mommahn suke dan neman waje ta zauna.

"Wani yace ki zauna a nan ne?" Ya faɗa yana kallanta. Se ta girgiza kai tana ji duk ta muzanta. Be sake cewa komai ba ya yi gaba dan har yanzu shi kaɗai ya san halin da zuciyarsa ke ciki. Tun da ta lura da inda suke ƙoƙarin shiga se ta ji jikinta ya yi sanyi. Toh me ya faru? Me ze shigar da su har bedroom ɗin Mommahn? Kafin ta ida tunanin ya saka hannunsa ya buɗe ƙofar, cikin lokaci ƙanƙani kuma ya saka kansa ciki. Duk da yanda jikinta ya yi sanyi hakan be hanata runtse idanunta ba ta yi shahada kawai ta faɗa cikin ɗakin ita ma. Da mamaki Yaya take kallan Didi har ma da Bad Man da suka shigo ɗakin. Ba ma ita kaɗai ba, ita kanta Didi kallansu take cike da mamakin, gefe guda kuma cike da son sanin dalilin da ya kawo su har cikin ɗakin Mommahn. Yaya ta buɗe baki da niyyar yin magana Mommah da yanzun ke zaune tace

"Ga ɗanki nan Yaya.. ga kuma sirikarki nan.." Ta ƙare tana nuna su Didi. Kallan Bad Man Yaya ta sake yi, ta kuma kalli Didi, kafin ta maida dubanta kan Mommah cike da mamakin abin da ya shiga kanta. Me ke damun Sa'adahn? Shin wannan da ke tsaye ba ɗan gidan Salma ba ne? Ita kuma macen matarsa? Toh me take nufi da abin da take faɗa? Ita kanta Didi fa kanta ya gama kullewa. Karin bayani kawai take buƙata, dan gaba ɗaya ma ta rasa gane inda maganar Mommahn ta dosa.

"Ban gane abin da kike nufi ba Sa'adah?" Yaya ta faɗa tana kallan Mommah. Ajiyar zuciya Mommah ta sauke, cikin raunanniyar murya tace
Chapter 79 · 0% Book details