← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 122

Sashe 27

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zan dawo idan kin huce.." Daga haka ba ta jira abin da Lulun za tace ba ta fice daga ɗakin har lokacin mamaki ya ƙi barinta. Kasa ko da kallanta ne Lulu ta yi se faman sauke ajiyar zuciya da take yi. Babu sautin kuka se hawayen dake ta sintiri a kan kuncinta. Ta rasa ma abin da ya kamata ta yi, gaba ɗaya kanta ya kulle.

.. Cigaba ta yi da kwashe haɗaɗɗen abincin cikin warmers. Har lokacin jikinta babu kuzari, ƙoƙari kawai take yi dan ka da Baba Atine ta ji babu daɗi. Se da ta gama komai sannan ta ɗauko su a hannu ta fito daga cikin kitchen ɗin. Idanunta na a kan ƙofarsa tana tunanin ta inda ya kamata ta yi. Ta san dai idan dai har ta ajje masa abincin ze iya gane ita ke ajje Coffee ɗin nan. Ita kuma ba ta so hakan ta faru, hakan ne ya sanyata tsayawa a bakin ƙofar idanunta a lumshe tana tunanin ta inda ya kamata ta fara. Se da ta yi namijin ƙoƙari kafin ta iya ɗaga hannunta ta shiga knocking na ƙofar tana runtse idanunta da kuma sake ƙanƙame abincin saboda tsaro ka da ya ɓare a wajen, musamman yanda ta ji jikinta na rawa ta san hakan na ita faruwa.

Sanye cikin riga mara hannu da kuma gajeren wando, kunnensa ɗauke da Bluetooth yana jin waƙa. Se da ya gama jin waƙar sannan ya cire ya ajje a kan gadon sannan ya nemi waje ya zauna dan duba wani aiki da Kaseem ya turo masa. Ba dan ya so ba se dan roƙon da Kaseem ɗin ya yi ta masa, hakan ne ya sanya shi soma dubawa. Se ya ji ana knocking na ƙofar. Share wa ya yi kamar be ji ba, se da ya sake ji an yi sannan ya ɗan ja ƙaramin tsaki yana miƙewa ya ƙarasa inda ƙofar take, ya saka hannunsa ya buɗe. Yana shirin komawa ta yi ƙarfin halin tattaro duk wani kuzarinta tace

"Ga abinci.. Baba Atine tace na kawo maka.." Ta faɗa ba tare da ta kalle shi ba, se ƙasa da take kalla saboda yanda yake mata kwarjini, uwa uba kuma shigar jikinsa. Dakatawa ya yi kamar ba ze juyo ba, se kuma ya juya a hankali yana kallan uwar ƙarfin halin nan.

"You??" Ya yi maganar kamar me neman ƙarin bayani, se dai fuskarsa kaɗai za ka kalla ka san ba ƙarin bayanin yake nema ba.

"Didn't i warn u? Ko kanki ba ƙwaƙwalwa ne? Ko kina so ne a yanzun nan na datse abin da ya bar ki kike zama cikin gidan nan?" Ya ƙare a zafafe yana kallanta. Se da ya ɗan sauke ajiyar zuciya sannan ya ɗora da

"Idan kika bari na sake ganin ƙafarki a nan.. wallahi zan shata miki cin mutuncin da har ki mutu ba a taɓa miki irinsa ba.. Shashasha.. Bar nan.." ya ƙare cikin ɗaga murya yana nuna mata hanya. Jikinta har wani karkarwa yake yi bayan da idanunta suka gama cika da ƙwallar da har ta fara zubowa kan fuskarta. Tana ƙoƙarin juyawa abincin hannunta ya suɓuce saboda yanda hannunta ke rawa. Nan take ya ɓare a wajen gaba ɗaya. Cikin ɓacin rai ya sauke idanunsa a kan abincin lokacin da take ƙoƙarin barin wajen, nan ma dai a tsawace yace

"Heyy.. wait." Kamar kar ta tsaya, se dai yanda ya yi maganar ya tsoratata hakan ne ya sanyata dakatawa, kafin kuma ya ƙara mata bayani, tunda ta fahimci abin da yake nufi se ta juyo har lokacin ta kasa kallansa, yana nuna abincin yace

"Oyah.. kwashe.." Tun kafin ya sauke maganar ta saka hannu ta soma kwashewa hawayen idanunta na ɗigowa har ƙasa. Amma duk wannan ba damuwarta ba ce. Damuwarta ɗaya ta bar wajen gaba ɗaya ma ta dena ganin wannan halittar mara kirki. Se da ta kwashe tass sannan ta miƙe ta wuce kitchen ta ajje kana ta fito daga cikin kitchen ɗin ta wuce ɗaki. Kan gado ta faɗa tana fashewa da kukan da tun ɗazu ta ƙi barinsa ya fito fili. Kanta kife a kan pillow take kukan kamar ranta ze fita. Tabbas ta ji mugun zafin abin da ya yi mata, ta kuma rasa dalilinsa na yi mata hakan. Me ta yi masa? Me ya sa ya tsaneta? Me ya sa halayensa suke haka? Cigaba ta yi da kukanta me cin rai tana sake tuna abin da ya faru. Ko fuskarsa ma ita ba ta son gani a halin yanzu. Saboda haka ko mene ma ita ba za ta sake yi masa ba, hatta Coffee ɗin ma ta dena. Dan ba ta ga amfanin kyautatawa mutumin da be san darajarka ba ko kaɗan. Ji take kamar ta ɗauki waya ta kira Ammi ta faɗa mata matsalarta, se dai kuma sam ba ta son ɗaga mata hankali, ba ta so kamar yanda hankalinta yake a tashe na Ammin ma ya tashi. Wata irin kewar er uwarta ta shiga ratsata tana jin yanzu haka da tana kusa da ita da ta samu wadda za ta faɗawa damuwarta, ta kuma ɗora kanta a kafaɗarta ta yi kuka ko ta ji sanyin abin da take ji.

... Tsaki ya ja a karo na biyu yana faɗin

"Ya haka?" Ya yi maganar sanda ya ɗauki wayarsa ya shiga dannawa. Number Mom ya danna ya kira ya kara a kunnensa. Babu daɗewa Mom ta ɗaga

"My boy.." shi ne abin da Mom ta faɗa. Be bi ta kan hakan ba yace

"Mom. Coffee ɗin.."

"Coffee kake so? Bari na saka a kawo maka yanzun nan.." Cikin mamaki yace

"Nake so kuma? Wanda kike ajje min fa?" Ita ma cike da mamakin tace

"Ni kuma? Yaushe?" Ta tambaya tana ɗan ƙanƙantar da idanunta.

"Ki na nufin ba ke ba ce..?" Ya tambaya hannunsa cikin baƙar kwantacciyar sumar kansa. Miƙewa tsaye Mom ta yi tace

"Me ya faru ne wai?"

"Just tell me pls.."

"Ba ni ba ce Areef.. Wani abun?" Ta tambaya tana jiran jin amsar da za ta fito daga bakinsa. Se dai be sake cewa komai ba se katse kiran da ya yi fuskarsa a yamutse ya tattare girar sama da ƙasa kamar me nazari. Idan dai har ba Mom ke kawo masa Coffee ba wa ke kawo masa kenan? Ko dai Mommah ce?

"Exactly.." ya faɗa a kan jajayen laɓɓansa dake zagaye da kwantacciyar ƙasumbar da ta sha gyara har wani santsi santsi take yi. Babu ɓata lokaci ya saɓi jiki se sashen Mommah.

... "A'ah Areef.." Mommah ta faɗa tana kallansa lokacin da ya shigo cikin ɗakin. Ƙarasawa ya yi ya nemi waje ya zauna, ya ɗauki ƙafarsa ɗaya ya ɗora a kan ɗaya sannan yace

"Mommah.."

"Na'am.."

"Coffee ɗin da kike turawa a kai min shi na biyo.." ya yi maganar yana kallan Mommahn. Da mamaki Mommah tace

"Coffee kuma? Anya kuwa ni?" A'ah zuwa lokacin fa kansa ya kulle, toh kenan idan dai duk cikin su biyun ba su ba ne, wane kenan yake masa Coffee ɗin. Jin da Mommahn ta yi be ce komai ba ya sanyata faɗin

"Kamar matarka ke yi maka fa.." ta faɗa tana kafe shi da idanu dan ganin reaction ɗinsa.

"Me ye hakan?.." ya faɗa cikin basarwa yana riƙe ƙafarsa ɗaya dake kan ɗayar ƙafar. Ta riga ta san halin Areef ɗin, ta kuma san yanzun ma yana sane yace hakan, ta kuma san ko za ta kwana tana sake maimaita masa kalmar ba ze nuna ya gane ba. Dan haka tace

"Yarinyar dake zaune a sashen da kake ita ce take yi maka.." Kallan Mommah ya yi na tsawon sakanni ba tare da yace komai ba. Ta yaya ma ze yadda da hakan? Yarinyar da tun ranar farko ya gargaɗeta da shiga masa ɗaki ballantana a kai ga kawo masa wani abun? Anya kuwa? Ƙaramin tsaki ya saki yana ɗan lumshe idanunsa sannan ya buɗe su a lokaci ɗaya. Daidai lokacin da Mommah ke faɗin

"Ka fahimta koh?" Kamar ba ze ce komai ba dan gaba ɗaya kansa ya kulle, ashe be sani ba ya jima yana shan abun hannun yarinyar bq tare da ya sani ba? A karo na barkatai ya sake jan tsaki yana ji kamar ya miƙe ya bar ɗakin kawai. Se dai be tashin ba ya cigaba da zama har kuma lokacin be ce komai ba. Da dai ya fahimci da gasken Mommah ke yi ita ɗin ke yi masa, se ya gyara zamansa yana sake cunkune fuska

"Ya za a yi na dinga samu?" Ya faɗa cikin basarwa. Ɓoye murmushinta Mommah ta yi sannan tace

"Toh ni dai a shawarce ka sameta da kanka ka mata magana a kan ta dinga yi maka, ai hakan ba komai ba ne.."

"Wa?" Ya tambaya a sheƙe irin kuma cikin rainin hankalin nan.

"Kai mana.." Mommah ta faɗa tana kallansa. Girgiza kai ya yi yana taɓe baki sannan ƙasa ƙasa ya furta

"Yarinyar dake jiran takaddarta? Idan da na sani ma ko kallan inda Coffee ɗin yake ba zan yi ba.. Who is she? She is just like a maid fa." Ya ƙare yana yamutsa fuska. Ajiyar zuciya Mommah ta sauke cikin kwantar da murya tace

"Babu komai fa Son.. ka na ji koh? Just ka ɗauketa as a maid ɗin, se ma ya fi sauƙi. Kawai faɗa mata za ka yi ta dinga yi maka, kafin zuwan ranar.." Mommah ta faɗa a ranta cike da fatan juyewar reshe da mujiya. Cike da fatan ya amince da abin da ta faɗa masa ɗin. Cike da fatan hakan ya zama silar daidaituwarsu shi da Afrahn.

"Nooo.." ya faɗa yana miƙewa cike da jin haushin abin da ya faru. Shi dai ba ya tunanin ze iya tsayawa ya saka yarinyar yi masa abu, har hakan ya sa ta fahimci ma ze iya cin abin hannunta ba, se dai Coffee ɗin nata ne kamar ana saka masa wani sinadari me matuƙar daɗi da ƙayatarwa. Ya ɗan lumshe idanunsa yana buɗewa a fili ya ja tsaki yana sake mamakin yanda aka yi ya kwashe kwanaki yana shan Coffee ɗin ba tare da ya fahimci me kawo masa ba..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO38*
Chapter 27 · 0% Book details