← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 122

Sashe 105

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba na son ƙamshin.." Ta faɗa tana girgiza kai. Kallan inda take kalla ya yi. Se yanzu ya fahimci dalilin aman nata. Wato abincin da Baba Atine ta kawo ne ba ta san ƙamshinsa. Da sauri ya ƙarasa ya ɗauka ya fitar da shi daga cikin ɗakin. Se a lokacin ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe idanunta lokaci guda tana ɗan sauke numfashi a jere a jere. Babu daɗewa ya shigo cikin ɗakin. Ya ƙaraso inda take, cikin kulawa yace

"Me za ki ci? Ki na so a dafa miki wani abu ne?" Kallansa kawai ta yi, kamar ba za tace komai ba se kuma tace

"Ba na son cin komai." Numfashi ya ɗan saukar a hankali ya girgiza kai yace

"Dole za ki ji yunwa. Tun da abin da kika ci ɗin kin zubar.." Ya ɗan dakata a nan kafin ya ɗora da faɗin

"Ko za ki ci abincin gidan Ummeey na je na kawo miki yanzun?" Se ta sake girgiza kai tana ɗan runtse idanunta. Fuskarta ya bi da kallo tausayinta na ƙara kama shi. Kawai se ya juya da nufin ficewa daga ɗakin. Ta yi saurin sanya hannunta ta riƙo hannunsa. Dakatawa ya yi saboda be tsammaci hakan ba. Ya bi hannun nasu da kallo kafin a hankali ya juyo ya zuba mata idanunsa da ke cike taff da tausayinta.

"Ba zan iya ci ba Allah kuwa.. Ba na jin yunwa ko kaɗan. Idan kuma na ce zan gwada ci, ragowar na cikina ne ze dawo." Ta yi maganar da iya gaskiyarta. Iska ya fesar daga bakinsa yana cigaba da kallanta. A nutse ya shiga takawa zuwa inda take. Kai tsaye kusa da ita ya nema waje ya zauna. Cike da tausayinta ya ja ta cikin jikinsa ya rungume. Babu musu ta kwantar da kanta tana lumshe idanunta. Numfashinta da ke sauka da ɗan sauri sauri ya cigaba da fita a haka. Cikin kulawa yace

"Allah Ya miki albarka, Ya albarkaci abin da ke cikinki.. Kowacce uwa kafin ta haihu akwai kalar abin da take fuskanta. Ina fatan Allah Ya fito mana da shi lafiya. Ke kuma Ya ƙara miki lafiya." Ya yi maganar yana sake riƙota sosai cikin jikinsa. Kawai se ta sake runtse idanunta sosai tana jin soyayyar abin da ke cikin nata na ratsata. Burinta ɗaya ta ga ranar fitowar shi ta kalle shi a ce wai ɗanta ne. Sun kai kusan minti 10 a haka kowanne na saurarar bugun zuciyar ɗan uwansa. Zuwa lokacin numfashinta ya saitu ya koma fita daidai. Jin ta soma sauke numfashi a hankali ya sanya ya fahimci bacci za ta yi. A hankali ya ɗan zameta daga jikinsa yana komawa ya kishigiɗa kan gadon sosai. Ya kalli inda take se ya ga har ta farka, da alama dama baccin be yi nisa ba.

"Afuwan na tashe ki." Se ta ɗan yi murmushi tana binsa da kallo. Sauƙin halinsa na burgeta, abin da da ba ta san yana da shi ba, dan ba ma ta bawa kanta damar fahimtar hakan ba. Miƙa mata hannu ya yi yana ɗan yin ƙasa da kansa alamar ta zo. Kawai se ta bi shi da kallo. Se a lokacin ta tuna abin da ke jikinta. Ta girgiza kai tana ƙoƙarin jan bargo dan lulluɓe jikinta. Sauka daga gadon ta soma ƙoƙarin yi. Rashin fahimtar abin da ze saukar da ita ya sanya shi faɗin

"Wani abu?" Se ta girgiza kai tana ɗan turo bakinta gaba. Ya yi murmushi bayan ya kalli kyakkyawan ƙaramin bakinta da ta turo. Ba ta jira ya sake cewa komai ba ta yi yunƙurin sauka. Ya yi saurin saka hannunsa ya riƙota se gata ta faɗo a jikinsa. Ta buɗe ido da sauri tana ji kamar ta fashe da kuka.

"Ina za ki je?"

"Kaya zan saka fa." Ta faɗa tana yamutsa fuska.

"Kaya kuma? Wannan me ye a jikinki?" Ya tambaya yana kallan jikinta da ke tashin wani irin ƙamshi na musamman. Yanda ta ji idanunsa a kanta ne ya sanya ta yin baya wai dan ya dena ganinta. Se dai ba ta san hakan ba ta dama ya yi ta sake shigewa cikin jikinsa ba. Ya kuwa sake mata kyakkyawan masauki a jikin nasa.

"Don Allah.." Ta faɗa tana sake yunƙurin tashi.

"Ni wannan ya ishe ni.." Ya yi maganar cikin basarwa yana zagayeta da hannayensa. Maganar da ya yi ne ta sanyata ɗaga kai ta kalle shi. Se ya kashe mata ido ɗaya. Babu shiri ta janye kanta. Ita dai har yanzu ta kasa dena mamakin Gwanin. Da dai ta da gasken ba sakinta ze yi ba, se kawai ta haƙura. Tana jinsa yana gyara mata kwanciya. Ya kwantar da kanta a saman ƙirjinsa yana sake gyara kwanciyarsa sosai. Shiru ya wanzu na tsawon lokaci. Duk ta kasa sukuni, se gyara kwanciyar take yi. Zuwa can Gwani ya buɗe idanunsa da ke a lumshe.

"Afaaf.." Ya kira sunanta kamar ba muryarsa ba. Ɗaga kanta da ta yi shi ne ya tabbatar masa da ta ji shi. Hakan ne kuma ya sanya shi ɗorawa da faɗin

"Don Allah ki ce ki na sona Afaaf.. Ina ƙaunar jin wannan kalmar daga bakinki. Na daɗe ina dakon soyayyarki cikin zuciyata, na kuma sanar da ke. Se dai har yanzu ban samu amsata ba. Ki taimaki wannan zuciyar ki agaza ki amshi soyayyata. A yanzu ne kaɗai zan iya tabbatar da kalmar da kika faɗa min har cikin zuciyarki ki na nufin hakan." Ya ƙare a raunane. Shiru ta yi tana jin yanda zuciyarta ke bugawa. Har cikin ranta ta ji maganar nan ta shi. Ta kuma rasa me za tace, ta ina za ta fara? Shin da gaske abin da ta faɗa ɗin ya fito ne tun daga cikin zuciyarta ko kuwa ganin Iftihal ne kawai ya sanyata faɗin hakan? Girgiza kai ta yi tana jin ƙwallar da ba ta san dalilinta ba na tarar mata cikin idanu. Yau kam dole ta magantu, ya zama dole ta ce wani abu, ko ta huta, ta hutar da kyakykyawar zuciya irinta Gwani Affan.

"Don Allah ka yi haƙuri.. Wallahi ban san lokacin da hakan ta faru ba." Da ƙarfi zuciyarsa ta harba jin abin da ta faɗa. Kenan tana nufin ba ta sonsa?

"Ya ilahy.." Ya ambata a kan laɓɓansa. Se dai maganarta ta katse masa tunanin, sanda ta cigaba da faɗin.

"Tabbas ina sonka.. Se dai ban soka saboda kai wani ne ba. Ban soka saboda gano asalinka ba. Ban san lokacin da hakan ta faru ba, ban kuma yi niyyar bari ka sani ba saboda kar ka yi irin wannan tunanin nawa. Na yi ƙoƙarin cigaba da kasancewa asalin Luluta se dai na kasa. Duk yanda zan yi na kasa. Ban san da wanne ido zan kalleka na kare kaina ba duk lokacin da irin wannan tunanin ya zo maka ba. Se dai duk yanda na ke kame kaina ashe ba zan iya ba, na ɗauka idan na cigaba da kallan Iftihal tana shige maka ba zan ji komai ba. Se na ga ashe ba haka ba ne. Ban tabbatar da na daɗe da soma sonka ba se da Iftihal ta soma ƙoƙarin shiga rayuwarka. Ina tsoron kar ta ja ra'ayinka musamman saboda ni ɗin da na ƙi baka haɗin kai, shi ya sa zuciyata ta umarce ni da sanar da kai abin da ke cikinta. Ina sonka.." Ta ƙare tana cusa kanta cikin ƙirjinsa, dan ita kaɗai ta san kunyar da take ji lokacin da take furta waɗannan maganganun. Wata irin gingimarin ajiyar zuciya Gwani ya sauke, muryar Lulu na sake yin amsa kuwwa cikin kunnansa. Ji yake tamkar mafarki yake yi, hakan ba lallai ya taɓa faruwa ba. Se dai yanda yake jin amon sautin muryarta cikin kunnuwansa shi ne yake sanyawa ya ji tabbas fa da gaske ne hakan ke faruwa. Da gaske yau Lulu ce ke faɗin tana son shi, bayan tsawon lokacin da ya ɗauka yana sonta. Be ga amfanin maimaita mata tambayar da gaske take ba tun da yanzun ma tabbatar masa take bayan sanar da shi da ta yi a waccan ranar. Ya kai wajen minti 5 ba tare da ya iya cewa komai ba. Se daga baya kafin ya soma faɗin

"Har abada wannan tunanin ba ze taɓa shiga kaina ba. Ba ki ƙi ni dan ba ni da arziƙi ba, kawai ba kya sona ne. Babu kuma dalilin da ze sa na yi tunanin kin fara sona saboda wani abu. Kawai Allah Ya kawo abubuwan a lokaci ɗaya ne. Haƙiƙa na yi farin ciki, na yi farin ciki mara iyaka. Ina son ki kodayaushe, zan kuma cigaba da sonki har abada." Ya ƙare yana ɗago kanta ya zuba mata idanunsa da suka sauya kamar ba nasa ba. Lumsassun idanunta ta zuba masa ita ma tana ji tamkar yau ta soma ganinsa. Se dai har ya gama maganarsa ta kasa sake ko da yunƙurin sake cewa wani abun ne. Haɗe tazarar da ke tsakanin fuskokinsu ya yi
ya shiga sauke mata wasu uban kisses kamar ze cinyeta. Fuskarta yau kam ta ga sumba. Haka zalika bakinta da yau ɗin ya tabbatar me shi ya bayyana. Kai daga ƙarshe ma se jirkitata ya yi ta koma kan gadon, ya shiga aika mata da zafafan saƙonni cike da matsananciyar ƙaunarta.

Ni dai daga haka se na ce Asuba ta gari.
Chapter 105 · 0% Book details