← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 122

Sashe 9

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Ohk.. Bari mu gama maganar ka je ka yi baccin... Afrah wannan ne mijinki.. Areef wannan ce matarka Afrah.." Daddy ya yi maganar a lokaci ɗaya. Ɗaga kai Bad ya yi ya kalli Didi da ta kasa ɗaga idanunta ta kalli wanda Daddyn ke cewa shi ne mijinta. Wani irin harbawa zuciyar Didi ke yi tun bayan jin abin da Daddyn ya faɗa, se ta sake maida kanta ƙasa har lokacin bugun zuciyarta be gama saituwa ba. Jin ba wani fuskantar abubuwa yake yi ba in banda wani jahilin bacci da yake ji ya sanya shi faɗin

"Ohk.." Kawai. Kallansa Daddy ya yi yana mamakin yanda ya yi reacting kamar komai normal, wanda hakan ba ƙaramin faranta masa rai ya yi ba. Se ya yi murmushi dan shi ya ɗauka ya karɓi auren ne hannu biyu yace

"Ohk je ka yi baccin. Za mu yi magana gobe In Sha Allah.." Be ce komai ba se miƙewa da ya yi ya soma takawa dan ficewa daga ɗakin. Hankali a tashe Mom ta miƙe tana faɗin

"Ina za ka je? Aou tafiya za ka yi ba tare da ka sawwaƙewa yarinyar nan ba? Kai ko dai asiri aka maka ne ban sani ba? Dawo nan ka saketa a gaban kowa da kowa, magana ta ƙare a yanzun nan ba se wata rana ba.." Mom ta faɗa cikin ɗaga murya. Ko bi ta kan Mom be yi ba ya fice daga ɗakin. Cikin sauri Mom ta juya da niyyar sake yin magana ta ga Daddy na binta da wani irin kallo. Tun kuma kafin tace komai ɗin ya soma faɗin

"Ashe dama ke kike ƙoƙarin ɗora yaron nan a kan hanyar da ba ta dace ba? Ashe ke kike tunzura yaron nan har yake ƙoƙarin bijire min? Ashe ke kike zuga shi a kan ya bijirewa umarnina? Toh ki buɗe kunnenki da kyau ki ki ni. wallahi duk ranar da kika saka yaron nan ya saki wannan yarinyar, ki tabbatar ke ma a ranar za ki karɓi takaddarki.."

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO28*

___Daddy ya faɗa fuskarsa a haɗe. Da matuƙar mamaki Mom ke kallan Daddy, dan bata taɓa tunanin abin da ze fito daga bakinsa ba kenan.

"Yallaɓai..?" Ta faɗa har lokacin cike da mamakin dai. Ɗaga mata hannu ya yi tun kafin ta ƙarasa faɗar abin da ta yi niyyar faɗa kana yace

"Abin da kika ji na faɗa shi nake nufi.." Daga haka ya fice daga ɗakin. Binsa ta yi da kallo kamar wata doluwa tana jin yanda ilahirin jikinta ya yi sanyi, kunya da haushin abin da ya faru a gaban Mommah na kamata. Me yasa ta kasa controlling kanta har hakan ya faru a gaban Mommahn? Ba tare da ta sake kallan kowa ba ta ja tsummar ƙafafunta ta bi bayan Daddy da ya fice daga ɗakin a fusace. Se a lokacin Mommah dake zaune gefe ta yi shiru hannunta a kanta kamar me tunani ta miƙe, ta ƙarasa inda Didi ke zaune kamar wadda aka dasa a wajen. Ita kanta da bata san ainahin abin da ya faru ba jikinta wani irin rawa yake yi, kuka ke shirin taho mata musamman yanda ta ji ana zancen saki kuma kamar a kanta ake maganar. Kenan idan haka ne wane ne mijin nata? Kenan ba shi ke sonta ba? Toh idan dai haka ne ya aka yi aka yi auren? Ita gaba ɗaya kanta ya kulle da wannan lamarin. Kamar daga sama ta jiyo muryar Mommah na faɗin

"Daughter.." Se ta ɗago da sauri, dan babu ƙarya ta tsorata, dan ba ta yi tsammanin akwai mutum a kusa da ita ba. Kafin tace komai Mommah tace

"Tashi mu je na raka ki ɗakinki, dare na yi.." Miƙewa ta soma yi jikinta a matuƙar sanyaye, kyawawan brown eyes ɗinta sun cika taff da ƙwalla, wadda ke jiran ƙiris ta zubo. Har cikin part ɗin dake kusa da na Mommah ta kaita, bata barta iya nan ba se da ta kaita har cikin bedroom. Sannan ta kalleta bayan ta yi murmushi tace

"Ki yi duk abin da za ki yi anan.. Zan aiko a kawo miki abinci, zuwa da safe idan Allah ya kai mu zan shigo.." Da sauri Didi ta kalleta jin tana ambatar da safe za ta shigo. Kenan anan za ta barta ita kaɗai? Jin Didin ba tace komai bane ya sanya Mommah faɗin

"Ya sunanki ne?"

"Afrah.." Ta faɗa cikin sanyayyiyar muryarta tana iya ƙoƙarinta wajen maida hawayen dake ƙoƙarin zubowa. Karo na farko kenan da ta yi magana tun zuwanta cikin gidan.

"Suna me daɗi.." Mommah ta faɗa tana murmushi. Se ta ɗora da

"Se da safe..?" Ta ƙarasa maganar cikin sigar tambaya. Da sauri Didi ta girgiza kai, sannan tace a sanyaye

"Don Allah.." ta yi maganar tana riƙo hannun Mommahn. Murmushi Mommah ta yi kana tace

"Shi kenan.. Zan turo miki Atine za ta zo ta tayaki kwana ko da na kwana biyu ne, kafin komai ya daidaita.." Cikin jin daɗi tace

"Tohm.." Se a lokacin ta saki hannun Mommah, ita kuma ta miƙe ta fice daga cikin ɗakin tana mamakin yanda ta ji lokaci ɗaya Didin ta kwanta mata. Tana nan zaune cikin ɗakin kamar marainiya, ta kaasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne se baza idanu kawai da take yi, dan kuwa ita bata saba zama a ɗaki ita ɗaya a irin wannan lokaci ba. Ta riga ta saba ganin Lulunta kodayaushe a gefenta. Se kawai ta shiga bin haɗaɗɗen ɗakin da ya ginu bisa tsari da kallo. Can se ga sallamar Atine cikin ɗakin, cikin farin ciki ta amsa sallamar se dai murya a sanyaye. Ƙarasowa Atine ta yi tana kallanta da murmushi kan fuskarta tace

"Barka da wannan lokaci Rankiyadaɗe.."

"Ina yini?" Didi ta katseta da faɗin hakan. Se ta sake yin murmushi tana amsa gaisuwar tata.

"Ga abinci nan, Hajiya tace a kawo miki.." ta faɗa tana nuna mata wasu warmers masu kyau da ta shigo dasu.

"Na gode.." Didi ta faɗa dai. Murmushi Atine ta yi, se kuma tace

"Kina buƙatar wani abun ne Rankiyadaɗe?" Ita duk idan tana mata abubuwa kamar wata ƙanwarta duk kunya ke kamata wallahi. Dan haka se ta girgiza kai kawai.

"Toh se da safe.." Atine ta faɗa. Kallanta Didi ta yi da mamaki tace

"Ba anan za ki kwana ba dama?" Ta tambaya cike da sarewa.

"Anan zan kwana amma a parlour.."

"Don Allah ki kwana anan kin ji?" Didi ta faɗa tana kallanta fuska a raunane.

"A'ah Rankiyadaɗe ki dai bari na kwana a can ɗin.. Idan kina buƙatar wani abu se na zo.."

"Don Allah Baba, wallahi tsoro nake ji.." Didi ta sake katseta da faɗin hakan. Se da Atine ta sauke ajiyar zuciya sannan tace

"Toh shi kenan.." Cikin farin ciki Didi tace

"Yawwah.." har murmushin da bata shirya masa ba na fitowa. Haka ba dan Atine ta so ba ta zauna cikin ɗakin duk a takure, tana ganin kamar ta zaƙe ne ta kwana ɗaki ɗaya da matar masu gidan. Ita kuwa Didi ko a jikinta, daɗi ma ta ji na zuwan Atinen, se a lokacin kuwa ta saki jiki ta samu ta ɗan yi wanka, kana ta fito ta tayar da Sallah.
Chapter 9 · 0% Book details