← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 122

Sashe 68

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mun gode sosai.." Ammi ta faɗa tana murmushi. Bin gidan da ya nuna Maimuna ta yi da kallo, tun da suka shigo layin jikinta ya yi wani bahagon sanyi. Duk da ba a iya ganin ya yanayin jikinta yake amma ko a fuskarta se ka fahimci hakan. Abubuwa da dama ne suke dawowa cikin kwanyarta a wannan lokacin. Se yanzu take tunanin ƙalubalen da za ta fuskanta duk lokacin da ta faɗi dalilinta na zuwa gidan. A take jikinta ya ɗauki rawa, se take ji kamar tace su koma. Ji take kamar ta juya saboda tsananin yanda take jin bugun zuciya. Idanunta da ke kallan ƙasa ta bari suka cigaba da kallan ƙasan lokacin da Talatuwa ke turata suna cigaba da tafiya.

"Wa kuke nema?"

"Alhaji Matawalle.." Talatuwa ta faɗa tana kallan ƙaton mutumin da ke kallanta fuskarsa babu annuri.

"Ya san da zuwanku ne?" Se ta girgiza kai tana duban Ammi cikin neman ƙarin bayani.

"Amm bawan Allah da yake ba mu san ya tsarin yake ba ne shi ya sa ka ji mun ce haka. Mun san ta yanda muka biyo ɗin be yi ba, amma kuma saboda abin da ke tattare da mu shi ya sa ba mu ji komai ba wajen faɗin muna son ganin Alhaji Matawalle."

"Lallai fa.." Mutumin ya faɗa yana jinjina kai. Be sake cewa komai ba ya juya. Talatuwa ta kalli Ammi tace

"Hajiya da ma haka abun yake?"

"Kar ki damu.. In Sha Allah za mu samu ganinsa." Se ta karkaɗa kai tana faɗin

"Toh Allah ya sa." Zuwan wasu matasa su biyu ne ya sanya Talatuwa kallansu daidai lokacin da wani dogo a cikinsu ke faɗin

"Se dai gobe ku dawo. Yau ba ya buƙatar ganin kowa." Shiru ne ya wanzu a wajen. Maimuna dake kan kujera ba ta iya ganinsu ta ji ina ma za ta iya ɗaga kai ta kalli mutumin dan ta masa magana. Se dai kuma hakan ba ze yiwu ba. Ga shi kuma gaba ɗaya ma ba ta da wannan ƙwarin gwuiwar, dan ta daɗe da rasa ƙwarin gwuiwar tun bayan shigowarsu Kano.

... Har ƙasa ya tsuguna cike da ladabi yace

"Rankayadaɗe wasu mutane sun takura suna son ganinka ne. Mun yi niyyar korarsu ne ma da, toh kuma mun san ba ka so, shi ya sa muka fasa. Duk da ka ce yau ba ka san ganin kowa amma yanda na ga mutanen ya sa na ce bari na zo na faɗa maka Sir."

"Kamar dai yanda na faɗa ɗin ne. Ba na son ganin kowa a yau ɗin nan. Ku ji da duk mabuƙatan kawai" Se da ya ɗan yi shiru yana tunanin ta inda ze soma. Har Bad Man dake gefe na ƙoƙarin ba shi umarnin tashi ya fita se ya ji yace

"Haka muka sanar da su Rankayadaɗe.. Mun kuma yi ƙoƙarin taimaka musu suka nuna su ba taimako suke so ba kai suke son gani. Da suka ga dai mun hana da gaske, se suka ba ni wannan takardar wai a taimaka a baka." Kallan takardar Daddy ya yi cike da mamaki. Se ya saka hannunsa ya karɓa ya karanta abin da ke ciki. Cigaba ya yi da kallan takardar na tsawon wasu sakanni kafin ya ɗaga kai ya kalli saurayin yace

"Ka shaida musu su shigo nan.."

"An gama Rankayadaɗe." Ya faɗa cikin girmamawa. Kallansa Bad Man ya yi cike da mamakin abin da ya faɗa ɗin.

"Daddy.."

"Babu komai Areef.. Idan magana ce me muhimmanci bari na gama da saurarar waɗannan." Ajiyar zuciya Bad ya sauke yana miƙewa tsaye.

"Tohm." Daidai lokacin da yake ƙoƙarin fita, Ammi, Talatuwa da kuma Maimuna dake a kan kujerar masu matsala irin tata suka saka kansu cikin ɗakin, da taimakon wani daga cikin yaran Daddy. Ya ɗaga kafaɗa yana sake mamakin dalilin Daddyn na cewa a barsu su shigo nan ɗin.

.. Mota ɗaya ce se dai haɗaɗɗiya ta shigo cikin gidan. Cikin rawar jiki wasu mutane 2 suka bi bayan motar har zuwa inda ta tsaya.

"Daga ƙarshe dai mun dawo." Aunty Makiyy ta faɗa tana murmushi. Ita ma Mom murmushi ta yi kafin tace

"Ke bari kawai.. Duk da dai na san ze yi faɗa a kan abin da na yi. Amma buƙatata kawai nake so ta biya."

"Ai Yaya ke ɗin nan koh?" Ta ƙare tana girgiza kai.

"Kya dai ji da shi." Mom ta faɗa tana sanya ƙafarta waje ta sauka daga cikin motar. Ita ma Aunt Makiyy sauka ta yi suka soma takawa zuwa ciki. Daidai za su gifta sashen mommah Aunty Makiyy tace

"Ni kam ban ga juyarki ba Mom." Ta ƙare tana riƙe dariyarta. Dariya ita ma Mom ta yi tana faɗin

"Au tawa ce ma? Lallai ma Makiyya ba ki da kirki.." Kafin Aunty Makiyya ta sake cewa komai Bad ya fito daga cikin ɗakin Daddy. Duk da be yi tsammanin dawowar Mom ɗin a wannan lokaci ba, amma hakan be saka shi sakar mata murmushi ba ya ƙarasa ya bata side hug yana faɗin

"Welcome Mom.." Rungume shi ta yi sosai tana murmushi. Don ba shakka ta yi kewar ɗan nata. Se da ta sake shi sannan tace tana kallansa

"Ka na lafiya Son?"

"Ehh.. Kun dawo lafiya?" Ya faɗa bayan ya bawa Aunty Makiyy nata hug ɗin da ya fi kama da gaisuwa kusa kusa.

"Lafiya ƙalau." Suka amsa kusan a tare.

"Zan ɗan fita Mom.. Se zuwa anjima."

"A'ah ka san wani abu Areef?" Aunt Makiyy ta faɗa bayan ta riƙo hannunsa lokacin da yake ƙoƙarin barin wajen. Se ya dakata ya kalleta lokacin da take faɗin

"Mom fa ta yi laifi. Saboda haka ka tsaya mu shiga tare, idan ma haƙuri ne mu ba shi tare." Ɗan shiru ya yi se kuma yace

"Yana da baƙi fa."

"Baƙi kuma?" Cewar Mom cike da mamaki. Ba ta jira ya amsa mata ba ta ɗora da faɗin

"Baƙi a cikin ɗakin nan? Wane irin baƙi ne wannan? Ko kuwa Abbun Kaseem ne?" Girgiza kai ya yi ya ɗan ɗaga kafaɗa sannan yace

"Ban sani ba gaskiya.. Ni ma abin da ya fito da ni kenan." Hannun Aunt Makiyy Mom ta kamo tace

"Kin ga ku wuce mu je. Ko su waye su fito su tafi kowanne palour ne amma dai ban da wannan. Wannan ma ai rashin daraja ne da sakawa a zubarwa da mutum mutuncinsa. Na kuma san ba aikin kowa ba ne se waccan uwar iyayin."

"Yi haƙuri.. mu je ɗin." Aunt Makiyy ta faɗa tana bin bayan Mommah zuwa cikin ɗakin..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO61*

___ Ba Lulu ce ta koma ɗaki ba se da suka gama aikin tsaff. Ta kuma taimakawa Ummeey sosai, taimakawar da ta matuƙar yi wa Ummeey daɗi. Ta kuma sake jin ƙaunar Lulun na ƙaruwa a ranta.

Buɗe plate ɗin ta yi a fili tana faɗin

"Da na taɓa ci ai da se na ci yasin." Ta faɗa tana kallan kwaɗon yaɗiyar da Ummeey ta haɗa ya ji kayan haɗi, ban da ƙamshi babu abin da yake yi. Tun ɗazu ya bata sha'awa, se dai kuma ba ta taɓa ci ba. Hakan ne ya sa take tunanin soma ci. Se kawai ta saka wankakken hannunta cikin plate ɗin ta ɗiba ta kai baki. Lumshe idanunta ta yi lokacin da ta tauna ta ji daɗi. Se ta jinjina kai har lokacin idanunta a rufe. Se da ta taune na bakinta tsaff kafin ta buɗe idanunta a kan yaɗiyar tana faɗin

"Allah kuwa Ummeey ƙwararriya ce." Ta faɗa tana sake ɗibar wata lomar. Babu daɗewa kuwa se ga shi ta tashi yaɗiyar tass, har da suɗe hannu. Dariya ta yi lokacin da ta tuna furucinta na farko

"Da na taɓa ci ai da se na ci." Se gata ta cinye tsaff. Da ma wani abun idan ba ka taɓa ci ba ka da ka ce ba ka ci, dan ba ka san yanda ɗanɗanonsa yake ba. Banɗaki ta wuce ta wanko hannunta sannan ta fito daidai lokacin da yake shigowa cikin ɗakin. Se ta ƙarasa ta ɗauki plate ɗin ta wuce da shi ɗakin nan kafin ta dawo ta nemi waje ta zauna. Ƙarasa ware naɗin kansa ya yi yana sauke idanunsa a kanta. Kamar ba ze ce da ita komai ba se kuma yace

"Ya dai kamata ki dinga barin jikinki na shan iska haka nan.. Bacci hijabi, karatu hijabi, sallah hijabi, cin abinci hijabi, komai ma hijabi.. A dinga haƙura da shi wani lokacin tun da ki na gida." Shiru ta yi tana murza yatsan hannunta da ɗayan hannunta. Kai ba za ka ɗauka za ta ce wani abu ba. Se a hankali tace

"Ai dai jikina ne, kuma ɗakina." Ta faɗa tana ɗauke kai bakinta kamar ze faɗo. Be san lokacin da murmushi ya ƙwace masa. Wato kalmar "Ɗakina" ta ba shi dariya ainun. Yau ita ce da kanta take faɗin ai ɗakinta ne? Se ya girgiza kai kawai yana cigaba da abin da yake yi, a ransa yana saƙa yanda ze rabata da wannan zama da hijab ɗin kullum kamar me.

...Ajiyar zuciya Bad ya sauke yana soma takawa ya bi bayansu Mom ɗin zuwa ɗakin Daddy.

"Assalamu Alaikum.." Aunty Makiyy da kuma Mom suka haɗa baki wajen faɗin hakan. Ba su jira amsar kowa ba suka dirfafi cikin ɗakin. Kallan waɗanda Bad Man ya kira da baƙin Daddy Mom ta yi ɗaya bayan ɗaya. Sannan ta ɗauke kai da shirin zuwa ta zauna. Se kuma da sauri kamar wadda ta tuna wani abu ta maida dubanta kan Maimuna. Ƙirjinta ya buga da ƙarfin gaske. Se ta kai hannunta ta murza idanunta dan sake tabbatar da abin da take gani, har kuma lokacin ba ta janye idanunta daga kan Maimuna ba.

"Maimunatu.." Ta yi ƙarfin halin faɗa muryarta na rawa.

"Na'am.." Maimuna da idanunta suka yi jajir ta amsawa Mom kiran sunanta da ta yi. I zuwa lokacin suman tsaye ta yi. Cikin lokaci ƙanƙani jikinta ya ɗauki rawa na tashin hankali. Ta kasa ko da motsawa daga nan ne zuwa can. "Maimunatu! Maimuna!!" Shi ne kaɗai abin da take iya maimaitawa.
Chapter 68 · 0% Book details