← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 122

Sashe 118

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yallaɓai ka ba mu izini mu fitar da wata mata daga cikin layin nan.. Tun ɗazu take nacin se ta shigo, dalilin da ya sa muka ƙi barinta ta shigo kuma kamar akwai alamun rashin hankali a tattare da ita. Se dai mun yi ƙoƙarin korarta, lura da hakan ya sa muka ƙyale ta. Se dai har yanzu tana can wai ita a lallai dole kai take son gani." Cike da mamaki Daddy yace

"Ni kuma?" Ya faɗa mamakin na bayyana a kan fuskarsa.

"Ka ce me rangwamin hankali ce, ya aka yi kuka san abin da take nufi?" Daddy ya tambaya yana kallansa.

"Yallaɓai ba na ce ba.. Amma tabbas haka take ta faɗa, shi ya sa ma na zo na sanar da kai." Sauke numfashi Daddy ya yi kafin yace

"Ku barta ta shigo." Cikin girmamawa ya amsa da

"An gama Sir." Daga haka ya juya. Ƙarasawa Daddy ya yi ya jingina da motar da za su shiga. Da ma tuni Mommah ta ƙarasa jikin motar.

"Rankiyadaɗe bari na ganta se mu wuce." Daddy ya faɗa yana kallan Mommah.

"Babu damuwa." Ta ƙare tana murmushi. Bayan wajen minti 3 se ga mutumin nan na ɗazu ya ƙaraso, bayansa wata mata ce me matsakaicin tsawo. Baƙa ce wuluk, irin baƙin nan da wahala ke kawo shi dan har wani dabbara-dabbara fuskarta ta yi. Kayan jikinta kansu sun yi wani iri, alamar sun daɗe a jikinta. Ban sani ba ko dalili kenan da ya sa kallo ɗaya suka mata na mahaukaciya. A ido ma tabbas ta yi kama da masu taɓin hankali. Se dai yanayin yadda take tafiya ya sani tantamar an ya kuwa mahaukaciyar ce? Daga Mommah har Daddy kallanta suke yi. Ita dai Mommah sanin da ta yi ba ta santa ba ya sanyata ɗauke kai daga kan matar ta maida kan Daddy dan ganin yanayinsa. Tana ƙarasowa matar ta zube a kan ƙafafunta tana fashewa da wani irin kuka irin me fitowar nan daga can ƙasan zuciya. Zare sunglasses ɗin da ke idanunsa Daddy ya yi yana kallan halittar da ke gabansa cike da tsananin mamaki. Mutumin na ida juyawa matar ta soma faɗin

"Don girman Allah Alhaji ku yafe min kai da Sa'adah, ku yafe min don Allah ko na samu na ga daidai a al'amurana. Ku taimaka min don Allah.." Cikin lokaci ƙanƙani bugun zuciyar Mommah ya ƙaru, wato ko daga bacci ta tashi ta ji muryar nan ai ta shaida wace ce, ballantana kuma ba hakan ba ne. Hajiya Salman ce ta dawo haka? Hajiya Salman ce ta sauya ta zama kamar almajira? Ina gayun nata? Ina en uwanta? Tambayoyin da Mommah ke ta yi wa kanta kenan tana cigaba da kallanta. Shi kansa Daddy ya yi matuƙar shiga mamaki ganin wannan ɗin Mom ce. Runtse idanunta Mommah ta yi lokacin da ta ji Mom ɗin ta cigaba da faɗin

"Na san na zalunci rayuwarku.. Musamman ma ke Sa'adah, na cuce ki, na raba ki da 'ya'yan da kika haifa saboda son zuciyata. Se dai yanzu da nake a gabanku a duƙe wallahi da gaske nake na tuba, na yi nadama. Kowa ya juya min baya, ban sani ba ashe dan ina tare da kai ne ake nuna ana ƙaunata, na ɗauka idan na je wajensu bayan sakina da aka yi za su karɓe ni, se na ga ashe abun ba haka ba ne. Makiyya ce kaɗai take tare da ni har ila yau. Se dai mijinta ya ƙi yarda in zauna masa a gida. Ban san yanda zan yi ba, na rasa mafita, hakan ne ya sa na fara fita nemarwa kaina abin da zan ci. Kalli yadda rayuwa ta juya min baya, waɗanda suka sanni a baya ma yanzu ba sa gane ni ɗin ce. Rayuwa ta yi min juyin waina, ji na nake kamar ba a raye ba. Don Allah ku ji tausayin halin da nake ciki ku yafe min." Ta ƙarasa maganar tana sake fashewa da kuka. A hankali Mommah ta saka hannu ta buɗe ƙofar motar da suke kusa da ita, tana shirin shiga ta ji Daddy ya riƙo hannunta. Dalili kenan da ya sanya ta dakatawa se dai har lokacin ba ta ɗago kanta ba, dan kuwa idanunta sun tara ƙwalla sosai, tuna abubuwan da suka faru kawai take yi. Tuna irin tsantsar zaluncin da Mom ɗin ta mata take yi. Se take ji kamar tsayawa ma ta cigaba da saurarar neman yafiyar da take ɓata lokaci ne. Kallanta Daddy ya yi ya girgiza mata kai dan son bata ƙwarin gwuiwa. Ta girgiza kai tana ƙoƙarin maida ƙwallar idanun nata. Maida dubansa kan Mom Daddy ya yi, kamar ba ze ce komai ba se kuma yace

"Ki tashi ki je, da ma kowa ya yi na gari ai kansa. Abin da kika aikata sakayya ce ke bibiyarki. Ki kuma gode wa Allah da ya haska miki zuwa neman yafiya wajen wadda kika aikatawa laifin. Don haka ki tashi ki je, sannan kuma kamar yadda na faɗa miki ba na buƙatar sake ganinki cikin gidan nan." Daga haka Daddy ya soma ƙoƙarin shiga motar.

"Don Allah Alhaji ku yafe min. Ka saka baki Sa'adah ta yafe min, kar ku bar ni cikin taraddadi domin Allah.." Mom ta faɗa tana ji kamar ta saka ihu ko za ta ji sauƙin abin da take ji.

"Ba ki ce komai ba..?" Daddy ya faɗa yana kallan Mommah da ta zauna cikin motar. Girgiza kai Mommah ta yi tace a sanyaye

"Ba ni da abin cewa.."

"Kin yafe mata?" Daddy ya tambaya yana kallanta sosai. Da sauri ta girgiza kai kafin tace

"Ba na ji zan iya yafe mata Yallaɓai.. Ni kaɗai na san abin da nake ji a cikin zuciyata. Don Allah mu bar maganar." Sauke numfashi Daddy ya yi, tabbas ya san abin da take ji, ya kuma san tana da gaskiya. Se dai shi kansa duk fushin da ya ɗauka da Mom ɗin yau da ya ganta se da ya ji tausayinta. Dan haka cikin rarrashi yace yana kallan Mommahn.

"Tabbas abun da ciwo, a cuce ka kuma a zo a baka haƙuri.. Se dai ki sani ko Allah ma muna masa laifi kuma ya yafe mana. Ko da ba ki duba komai ba ki duba hakan, ki kuma duba yadda ta yi nadama.. Ba ina nufin ku cigaba da alaƙa ko wani abu makamancin haka ba, a'ah.. Kawai dai ina so ne na ji kalmar yafiyar daga bakinki. Ki yi haƙuri ki yafe mata ɗin." Runtse idanunta Mommah ta yi, kusan minti 1 da gama maganar Daddy ba tace komai ba. Se zuwa can tace a sanyaye.

"Allah Ya yafe mana gaba ɗaya."

"Ameen.. Allah Ya miki albarka, Ya ƙara raya zuri'a, Ya albarkaci yaran nan." Ba ta iya amsawa a fili ba se komawa da ta yi ta jingina da kujera. Daddy ya fita daga cikin motar. Har lokacin Mom na nan a gantale, har kuma lokacin ta kasa cire rai a kan yafiyar Mom ɗin.

"Kin yi sa'a Allah Ya saka mata tausayi a cikin zuciyarta, bayan abubuwan da kika aikata mata, se ga shi ta yafe miki.." Da sauri ta ɗaga kai ta kalli Daddyn, ba ta taɓa tunanin haka ne ze fito daga bakinsa ba. Da gaske Mommahn ta yafe mata? Da gaske ta yafe duk laifin da ta mata?. Maganar Daddy ce ta katse mata tunani lokacin da ya cigaba da faɗin

"Se dai fa ki sani, yafe mikin da ta yi ba shi ne ke nufin cigaba da bibiyarmu ba. Tun da kin samu abin da kike so, ina so ki yi nesa da mu, ki je ki cigaba da rayuwarki." Ita zancen yafiya ma kaɗai da ya mata ai ya ishe ta, ko bayan nan ya faɗi wani abun ai ba za ta damu ba tun da dai Mommahn ta yafe mata.

"Na gode sosai, na gode, na gode, Allah Ya saka da alkhairi. Na gode. Don Allah ka yi wa Hajiya godiya, Allah Ya saka mata da alkhairi, na gode." Shi ne abin da Mom ta yi ta faɗa kamar za ta aro baki.

"Ki gode wa Allah.." Daddy ya faɗa. Daga haka ya juya ya shige cikin motar. A sukwane ta miƙe haka tana ji tana gani duk daular nan da a da take ciki, ta fice ta bar gidan. Har juyawa take ta kalli gidan da zarar ta yi nisa. Da ta san rayuwa za ta juya mata baya haka, da tun farko ta zauna a matsayin wadda ba ta da ɗa, tun da ga Mommah nan duk da a da da ake tunanin ba ta da komai hakan be rage ko kaɗan daga soyayyar da Daddy yake mata ba. Ko da kuwa Daddy ya faɗi ya mutu za ta samu kuɗi. Se dai da yake a lokacin sheɗan ke ta ingiza ta, ba ta taɓa kawo hakan ba. Ita burinta kawai duk dukiyar ta zamo tasu. Wannan shi ne kaɗai burinta. Ashe ba ta san ranar danasani na nan zuwa ba. Se ga ta ta zo a kurkusa babu daɗewa da tonuwar asirinta. Ba ta san lokacin da kuka ya ƙwace mata ba. Ta saka gefen hijab ɗinta tana goge hawayen. A haka ta fice daga tanƙamemen layin gidan na Alhaji Matawalle.

... A karo na barkatai ya sake kallan Didi da ke zaune a kan kujera, ta ɗora kanta a kan kujerar ta yi shiru kamar me tunani. Se da ya ƙarasa abin da yake sannan ya miƙe. A nutse ya ƙarasa ya zauna dab da ita yana kallanta. Kafin ya saka hannunsa ya riƙo hannunta. A hankali ya furta

"Wai ɓacin ran na mene ne? Me ke damun Babyna?" Ya ƙare yana zuba mata idanunsa. Lumshe idanunta ta yi fuskarta a narke kamar wadda ke shirin yin kuka. Ta girgiza kai jiki a sanyaye.

"Ni ma ban sani ba." Ta faɗa da iya gaskiyarta, dan ba ta san ainahin abin da ke damunta ba. Ita dai kawai ta tashi da ɓacin rai.
Chapter 118 · 0% Book details