← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 122

Sashe 84

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni ma ban san zan zo ba Lulu." Ta yi maganar lokacin da suka saki juna. Se a lokacin sannan ta gaishe da Mommah, Mommah ta amsa da ƙawataccen murmushi a kan fuskarta. Tsananin kamar da Lulu ke yi da Didi shi ne abin da ya sa ta kasa ɗauke ido daga kansu, dan babu ƙarya sun mata kyau sosai. Musamman da suka haɗu, se kyawunsu ya ƙara fitowa sosai. Hannun Didi Lulu ta kama suka nemi waje suka zauna, ita dai Didi se bin Lulu take da kallo saboda yanda ta ga ta ɗan chanja. Se ta ga kamar ba ita ba, ita idan ma ba idanunta ke mata ƙarya ba gani ta yi Lulun ta yi ƙiba, har haske ma ta ƙara. Gaisawa Mommah da Ummeey suka yi da fara'a kamar sun san juna. Kafin Didi ta gaishe da Ummeey cike da girmamawa. Ta amsa cikin fara'a ita ma tana sake kallan kamannin Lulu da Didin. Zuwa can babu daɗewa Abeey suka yi sallama tare da su Daddy. Suka ƙaraso suka nemi kan tabarmar suka zauna. Se suka gaisa da Ummeeey. Ta amsa tana tambayarsu sun zo lafiya?. Daga haka se wajen ya yi shiru na tsawon sakanni, kafin Abeey ya katse shirun da faɗin

"Ina yaron nan?"

"Yanzun nan ya fita.. Amma ba daɗewa ze yi ba yanzun za ka gan shi.."

"Toh madallah.." Abeey ya amsa da hakan. Cigaba da zama suka yi. Daddy, Bad Man, Mommah har ma da Didi duk sun ƙagu su ga wa za su gani a matsayin ɗan uwan Bad Man.

"Ke wai me ye wannan?" Didi ta faɗa ƙasa ƙasa tana kallan Lulu da ta ga alamar satar kallan mutane take idan ta ga babu idanun kowa a kanta ta ci abinta.

"Kwaɗo ne mana.. Ki ji Didin nan."

"Oh da ma ki na ci ne?" Didi ta faɗa tana kallanta.

"Oho ni dai yanzu ina ci.." Ta faɗa tana ɓata rai. Daidai lokacin da Gwani ya shigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, sanye cikin shigarsan nan dai da kuka sani. Kansa ma nannaɗe kamar ko yaushe. Ya yi kyau na musamman, musamman kuma da ya kasance kalar kayan da ke jikinsa me duhu ne. Se ya mugun hawa kan fatarsa, ya yi kyau ainun. Kallan Gwanin Didi ta yi, daidai lokacin da wani abu ya saƙu a zuciyarta. Duk da an kira sunan Affan a farko, sun kuma zo cikin gidan nan ta ga Lulu, hakan be sa ta kawo komai ba se yanzu. "Kenan Ya mu'allim shi ne twin brother ɗinsa? Ɗayan ɗan Mommah?" Ta tambayi kanta. Ƙarasawa Gwani ya yi cikin girmamawa ya gaishe da waɗanda ya kamata. Mommah dai kawai kallansa take yi tana jira ta ji abin da Abeey ze faɗa. Sosai tarbiyyar yaron ta burgeta, yanayin shigarsa da kuma nutsuwarsa, se take ji ina ma ina ma..?
Se ya miƙawa Bad Man hannu yana murmushi yace

"Kai ne a gidanmu yau?" Kawai miƙa masa hannu Bad Man ya yi ba tare da yace komai ba. Dan lokacin tuni zuciyarsa ta fara saƙa masa wani abu. Jira kawai yake Abeey ya yi magana. Kamar kuwa Abeey ya san me yake saƙawa se kuwa cewa ya yi

"Wannan shi ne Affan.." Shi ne abin da ya furta kawai yana kallan Gwani. Gaba ɗaya en wajen se suka ɗaga kai suka kalli Gwani, ciki kuwa har da Lulu da Ummeey kamar waɗanda ba su taɓa ganinsa ba. Duk se ya ji ya tsargu. Kawai se ya juya da nufin barin wajen, daidai lokacin da Mommah ta miƙe. Muryarta a sanyaye tace

"Affan.." Se ya dakata yana juyowa. Daidai lokacin da Mommah ta ƙaraso, kawai se ta kamo hannunsa ta kalle shi, a cikin ranta tana ji lallai wannan ɗin shi ne ɗan uwan Areef. Shi ne ɗayan ɗan nata da take nema.

"Lallai tabbas na ji a jikina ɗana ne wannan.." Ta yi maganar tana jin wasu hawaye masu ɗumi na zubowa a kan kuncinta. Cike da mamaki Gwani ke kallanta, yana mamakin jin abin da ke fitowa daga bakinta. Sam ya kasa fahimtar inda zancenta ya dosa. Hakan ne ya sa ka na ganinsa ka ga wanda yake a dame. Ba tare da lura da hakan ba, ta ja shi ta rungume. I zuwa lokacin fa kansa ya sake kullewa. Se dai be san dalilin da ya sa lokacin da ta rungume shi ɗin ya ji wani sanyi cikin zuciyarsa ba. Wani irin sanyi ne ya shiga ratsa Mommah, makamincin wanda ta ji lokacin da ta rungume Areef bayan sanin ɗanta ne. Gefe guda kuma wani farin ciki mara misaltuwa na mamayeta, irin farin cikin nan me sanya me yinsa kuka.

"Lallai babu musu kam Affan shi ne ɗanku.." Abeey ya faɗa jikinsa a sanyaye. Ai babu shiri Gwani ya tashi daga rungumar da Mommah ta masa. Ya kalli Abeey da ya ji ya yi maganar. Bugun zuciyarsa tuni yanayin fitarsa ya ƙaru. Hatta idanunsa har sun soma chanjawa. Cike da fargaba yake kallan Abeey cikin son jin ƙarin bayani a kan abin nan da yake faɗa, da kuma abin da ya ji Mommah ta faɗa. Idan dai har ya ji da gaske me suke nufi da hakan?. Cikin ƙarfin hali ya soma faɗin

"Ban gane abin da kake faɗa ba Abeey.. Don Allah ka sanar da ni abin da na ji ka na ƙoƙarin faɗa.. Na kasa ganewa Abeey.. Ummeey me Abeey ke ƙoƙarin faɗa ne a wajen nan?" Ya ƙare maganar yana kallan Ummeey. Ai ko wuƙa aka saka a wuyan Ummeey ba ta tunanin za ta iya furta komai a irin wannan lokacin. Gaba ɗaya ta ruɗe, ganin abun take kamar mafarki. Ba ta yi tunanin ranar za ta zo mata a haka ba duk da yanda ta tsammaci zuwanta. Kawai se ta kautar da idanunta daga kan Gwanin, saboda yanda zuciyarta ta cigaba da karyewa. Ya girgiza kai yana ji kamar zuciyarsa za ta tsarwatse

"Babu wanda ze min bayanin abin da ke faruwa?" Gwani ya faɗa cike da sarewa. Se a lokacin sannan Daddy ya soma faɗin

"Ka kwantar da hankalinka Affan.. Har yanzu Malam shi ne mahaifinka, matarsa kuma ita ce mahaifiyarka, dan kuwa har abada ba ka da kamarsu.. Se dai yanzu ana magana ne a kan sanin wane ne kai tun ranar da ka zo duniya.. shi ya sa aka sakomu cikin maganar. Tabbas mu ne iyayenka Affan.." Daga nan Daddy ya shiga faɗa masa abin da ya faru tun lokacin da aka haifesu. Raba su da aka yi, da kuma yar da shi da aka yi a bakin gidan marayu. Ba Ummeey kaɗai ba, hatta Lulu ta jijjiga da jin abin da ya faru. Tsananin tashin hankali ya sanya tuni jikinta ya soma ɓari, ta shiga kallan Gwani kamar yau ta soma ganinsa. Ummeey kanta kallan Gwanin take yi har ma da Bad Man. Ita kanta ta shiga matuƙar mamaki, da tashin hankali bayan ta ji abin da ya faru. Ba ta taɓa tunanin za a iya samun mutane marasa imani kamar waɗannan a gaske ba se yau. Tausayin Affan ɗin ya kamata. Ba ma shi kaɗai ba har da mahaifiyarsa da ɗan uwansa.

Dumm haka Gwani ya ji kunnansa ya yi masa bayan gama saurarar abin da ya faru. Tuni kyawawan idanunsa sun kaɗa sun yi wani irin ja kamar garwashi. A hankali ya shiga zamewa kan tabarmar da Bad Man ke zaune ya zube a kanta. Ya runtse idanunsa yana jin wani jiri na kwasar shi. Kansa ya kifa a kan hannunsa cikin rashin sanin abin yi. Gaba ɗaya kansa ya kulle, gaba ɗaya komai ya tsaya masa cakk. Ummeey da Abeey ba iyayensa ba ne? Su ɗin ɗaukarsa suka yi daga gidan marayu? Ainahin iyayensa su ne waɗanda yake gani yanzu haka a zaune? Kawai se ya cigaba da ajje numfashi saboda yanayin yadda bugun zuciyarsa ke fita da sauri da sauri, kamar wanda ya yi tsere. Shi kam yau ya ma rasa a cikin wane fanni ze saka wannan rana. Sam ya kasa tunanin komai, ban da abin da ke faruwa yanzu babu abin da yake tunawa. Ummeey da Abeey ba iyayensa ba ne, iyayen Abokinsa Areef da suka haɗu babu daɗewa su ne iyayensa. Ya yin da shi kuma ya kasance ɗan uwan tagwaitakarsa. Shi ne kawai abin da yake tunani.

Shiru wajen ya ɗauka tamkar babu kowa a wajen, kowa kuma se ya samu damar yin magana da zuciyarsa. Ita dai Ummeey gaba ɗaya ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne, hankalinta gaba ɗaya na kan Affan ɗinta. Wanda zuwa wani lokaci da ta ga har yanzu be ɗago ba se ta ɗaga kai ta kalli ɗan uwansa da ta shaida fuskarsa ɗazun. Se yanzun ne ta gane dalilin da ya sa tun farkon jin muryar Areef ta kasa sukuni, dan kuwa bambancin kaɗan ne, shi ne shi Bad Man muryarsa a ɗan tsaitsaye take, ya yin da ta Gwani ke a kwance. Lol.. Dan kuwa kasancewarta haka ne ya sanya take kama da ta larabawa musamman idan yana larabci. Tun a lokacin ta shiga tunanin ko dai ɗan uwan Affan ne? Amma kuma idan ɗan uwansa ne me ya raba su? Ina iyayensu? Rashin bawa hakan muhimmanci ya sanyata watsarwa gaba ɗaya, se ta bar shi a ikon Allah ne kawai ya sa muryar tasu ke kama. Ita kanta Didi se a yanzu abubuwa da dama suka dawo mata. Ba tun yau ta soma jin kamanceceniyar muryar Gwani da Bad Man ba. Se dai fahimtar ba su da wata alaƙa ya sanyata watsar da lamarin dan ta san ba shi da muhimmanci. Ashe ba haka ba ne.. Ashe ikon Allah en biyu ne. Shi ya sa sau da dama ma se ta ga idan ya yi wani abun ya yi mata kama da wani. Ashe da ɗan uwansa Gwani ne.
Chapter 84 · 0% Book details