← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 122

Sashe 48

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mom.. ba na son zuwa ne.." ya katseta da faɗin hakan a ƙagauce.

"Ba za ka iya yin wani abu dan ni mahaifiyarka ba?" Shiru ya yi yana mamakin wannan abu na Mami. Dan dai ta bar yi masa zancen ya sanya shi faɗin

"Shi kenan. Zan yi tunani a kai.."

"Sure?" Ta tambaya tana kallansa. Se ya jinjina kai yana ajje numfashi a nutse. Daga haka ya tashi fice daga ɗakin. Mom ta bi shi da kallo, a ranta tana fatan a ce ya yadda da wannan ƙudurin nata.

.... Duk abin da take yi jikinta a matuƙar sanyaye yake. Tana kuma yi cike da takatsantsan musamman saboda ciwon da ke ƙafarta. Ita ji take ma kamar kar ta yi komai. Se dai kuma idan ta tuna da Mommah se kawai ta haƙura ta cigaba da abin da take yi. Se da ta gama komai sannan ta sauke numfashi tana ɗaukar Coffee ɗin dan wucewa da shi ɗakin Bad Man.

Mayukansa masu mugun ƙamshi kaɗai ya shafe jikinsa da su. Ko bi ta kan sumar kansa be yi ba. Sumar da ko da ze ɗauki tsawon sati ba tare da ya taɓata ba babu wanda ze fahimta, saboda yanda take a gyare, a kwance tsaff tsaff. Towel ɗin da ke kan ƙugunsa ya zame ya maida shi ma'ajinsa kafin ya dawo cikin ɗakin inda ya ajje abubuwansa da ɗazun bayan rabuwarsa da su Hero ya taho da su cikin takatsantsan ɗin nan dai da ya saba ba tare da an gan shi ba. Saboda shi ya fi so ko da kwalɓewar ze yi ya yi a gida ba se ya je wani wajen ba, ballantana ma wasu su gan shi. Idan kuma ya yi a wajen toh kamawa ta yi, amma dai ta fi ganewa a dan. Kwata kwata ya ma manta da wani kulle ƙofa idan ze kwalɓe. Ya nemi waje ya zauna. Hannu ya kai ya ɗauka kwalbar ya shiga juyata cikin hannunsa. Be san wace kala ba ce, shi dai kawai yana buƙata ne shi ya sa ya siya duk da be taɓa shan kalarta ba. A cikin ɗan ƙaramin cup ɗin nan ya zuba ya kai bakinsa. Lumshe jiƙaƙƙun idanunsa ya yi lokacin da ya ji ta cikin bakinsa. Se ya buɗe idanunsa ya cigaba da kwankwaɗa kamar babu gobe. Se da ya gama tsaff sannan ya miƙe yana ɗan wawwara madaidaitan idanunsa, ya maida su mazauninsu inda babu wanda ze iya ganinsu. A hankali ya shiga takawa zuwa kan gado dan ya baje ya yi baccinsa. Se dai me? Sam be saba jin komai ba bayan ya sha. Be saba jinsa kamar ba shi ba. Se dai yau ɗin gaba ɗaya se yake ji kamar ba shi ba. Idanunsa har wani ƙanƙancewa suke yi. Cikin lokaci ƙanƙani ya ji kansa ya wani irin sara masa. Ya kai hannunsa da sauri ya dafe kan nasa idanunsa a lumshe. Idanunsa na a rufen ya shiga takawa dan ƙarasawa kan gadon, se sai yanda yake ji kamar ana daƙire shi ne. Kamar ba tafiya yake yi ba. Hannunsa ya sake dafewa saboda yanda ya cigaba da sara masa. Zuwa yanzu ma ji ya yi ya masa wani gingirin kamar wanda ya ɗora wani ƙaton gini a kan nasa. Tilas ya dakata daga inda yake dan hatta ɗakin ya soma juya masa. Daidai lokacin Didi ta turo ƙofar ɗakin kamar yanda ta saba dan zuwa ta ajje abin da ke hannunta. Kanta na ƙasa Allah Allah take ta ajje ta fice daga ɗakin. Se dai me? Tana cigaba da takawa zuwa wajen ta ɗan ɗaga kanta da niyyar kallan gabanta. Se ta hange shi tsaye hannunsa riƙe da kansa idanunsa a kulle. Kamar wadda aka dakatar, se ta dakata a inda take tsaye. Ta cigaba da kallansa cike da mamakin yanda ta gan shi a tsayen nan haka kamar ba shi ba. Kafin ta ida tunanin Bad Man ya yi iya ƙoƙarinsa, cike da dauriya ya shiga takawa. Se kuwa ya yi taga taga kamar ze faɗi, alamar dai mutumin da ke cikin maye. Ba ta san lokacin da ta watsar da abin da ke hannunta ba. Ƙirjinta na bugawa ta yi inda yake. Motsin da ya ji ne ya sanya shi soma buɗe idanunsa da zuwa yanzu sun yi jaa kamar ba na shi ba. Da ƙyar ya iya buɗe su shi ma ba duka ba. Kamar ma wanda be buɗe idanun ba saboda yanda suke wani irin lumshewa. Be taɓa tsammanin ganinta ba. Be taɓa zaton buɗe idanunsa ya ganta ba. Se ga ta tsaye a nesa kaɗan da shi.

"Fita!" Ya yi maganar cikin ƙarfin hali a kuma dake daidai lokacin da ya runtse idanunsa yana ɗan girgiza kai saboda tsananin yanda yake sara masa. Girgiza kai ta yi na tare da ta motsa a inda take ɗin ba. Dan kuwa haka nan kawai ta ji ta tsorata da yanda ta gan shi. Be daddara ba ya sake ɗaga ƙafarsa ya cigaba da takawa. Na en sakanni kan ya sakar masa, dan haka ya ƙarasa ya zube kan gadon a wata irin kwanciya ta rigingine. Kansa na kusan ƙasa zan iya cewa dan kuwa har hannuwansa duk sun zubo ƙasa ne.

"Fi..ta!" Ya sake faɗa yanzun ma a ɗan rarrabe se dai a daken dai. Hannuwansa da ba sa kan gadon ya ɗaga ya maida su kansa da yanzun ma ya sara masa yana mamakin abin da yake faruwa da kan nasa haka. Da sauri Didi ta matsa wajen gadon ba tare da ta lura da abin da yace mata ba har lokacin tana jin wata muguwar faɗuwar gaba. Duk kuma da kasancewar daga gajeren wandon nan babu wani abu a jikinsa ita ba ma ta lura ba dan hankalinta na kan yanda yake cigaba da riƙe kansa ne kamar wanda wani abin ya same shi a kan nasa. Ji take kamar ta kai hannunta ta riƙe masa kan ta karanto masa addu'a ko ze ji sauƙi. Don kuwa yanzun har jijjiga kan yake cikin matuƙar azabar da shi kaɗai ya san abin da yake ji. Cigaba ta yi da kallansa zuwa lokacin narkakkiyar zuciyarta ta daɗe da karyewa har ta hawaye sun fara zubo mata. Ganin dai tsayawar da take yi ɗin ba mafita ba ce. Ya sanyata yin shahada a hankali ta soma matsar da hannunta da ke rawa. Cike da fata da addu'ar Allah ya sa kar ya ci mata mutunci ta kai hannun nata kan goshinsa. Ta runtse idanunta bugun zuciyarta na ƙaruwa. Babu ɓata lokaci ta shiga yi masa addu'a a zuciyarta. A nutse ya shiga buɗe idanunsa yana sauke numfashi da mugun sauri. Ya fahimci me ye a kan goshinsa. Dan haka da yake lokacin kan ya ɗan sakar masa se ya yi amfani da ƙarfin sa ya rage masa ya saka hannunsa ya riƙo nata hannun. Be yi wata wata ba se jan hannun da ya yi da niyyar ya turata ta bar kusa da shi, ta ma fice daga ɗakin gaba ɗaya. Se dai yana ƙoƙarin turatan wani irin jiri ya kwashe shi. Be san lokacin da ya saketa ba bayan ya koma baya. Cikin ƙankanin lokaci se ga ta a kan gadon kamar wadda aka jefo, yayin da shi kuma ya yi baya se ga kansa a kan cinyarta...

MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO50*

___ Cikin sauri zuciyarta na wani harbawa ta zo dan miƙewa. Se dai gaba ɗaya ƙarfinsu ba ɗaya ba. Maida dubanta ta yi kan fuskarsa da ya cigaba da runtse idanunsa. Gaba ɗaya se ta manta da batun tashin. Ta sake kama kan nasa duk da yanda hannunta ke rawa ta cigaba da yi masa addu'a. Kusan mintuna 10 ya ɗauka yana cigaba da murƙususun, se kuma cikin lokaci ƙanƙani wani wahalallen nannauyan bacci ya kwashe shi. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya ce ta suɓuce mata ba tare da ta sani ba. Ta lumshe idanunta tana jin wani sanyi har cikin ranta. A hankali kuma se ta soma ƙoƙarin zame ƙafafunta dan ficewa daga ɗakin tun da ya yi bacci. Se dai saboda yanda ya yi bacci, ga kuma yanayin ƙarfinsu ya sanya sam ta kasa motsa cinyar tata, ko da nan da can ne. Ba tare da sarewa ba ta cigaba da ƙoƙarin zamewa. Se dai duk iya ƙoƙarinta se ta kasa. Ta yi ta yi ta kasa janyewa. Idanunta da suka ciko da ƙwalla ta kai hannu ta ɗauke ƙwallar sannan ta dawo da dubanta kan kyakkyawar fuskarsa da cikin ƙanƙanin lokaci ta yi fayau kamar ta mara lafiya. Cigaba da zama Didi ta yi na tsawon mintuna masu yawa. Har kuma lokacin ba ta haƙura ba, ta cigaba da ƙoƙarin janye cinyar tata. Sam bata sani ba, ba kuma ta ankara ba wani bacci ya yi awon gaba da ita.

Bayan shuɗewar wasu awanni.. A hankali ya shiga buɗe iidanunsa da suka yi mugun nauyi kamar wanda suka gama masa ciwo, ko kuma wani abu mara daɗi ya same su. Daidai lokacin da Didi ma ta buɗe nata idanun. Se kuwa ya yi daidai da lokacin da ya ida buɗe nasa kuma a kan Didin. A take idanunsu suka sarƙe cikin na juna. Didi ta yi ƙarfin halin yin baya da sauri dan sauka daga kan gadon se dai i zuwa lokacin ma se ya zamana kusan rabin jikinsa gaba ɗaya yana kanta ne. Hakan ne ya sanya kamar jiyan yanzu ma ta kaasa. Da sauri ya tashi daga inda yake kwancen, ita kuma ta yi maza ta yi amfani da wannan damar tana ƙoƙarin dira daga kan gadon. Ya yi saurin sanya hannunsa ya riƙo nata hannun ya dawo da ita baya. Da yake shi kansa be gama tashi zaune ba se ya yi baya kan gadon ya yin da ita kuma ta biyo bayansu se ga shi a kan gadon ita kuma Didi ta faɗa kansa. Ba tare da ta ɓata lokaci ba ta miƙe jikinta na wani irin karkarwa. Kafin ta ida miƙewa ya sanya hannunsa ya sake riƙo tsintsiyar hannunta ya dawo da ita tana kallansa se dai bata hau kan jikinsa ba. Amma fa dab take da shi dan kuwa hatta yanda numfashinta ke fita da bugun gaske yana iya ji.
Chapter 48 · 0% Book details