← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 122

Sashe 62

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Runtse idanunsa Kaseem ya yi lokacin da ya ga hannun Bad Man a kan na Didi. Shi kenan ashe da gaske yake kenan? Ya aka yi hakan ya faru? Me ya sa aka hana shi auren Didin aka kuma aurawa Bad Man? Ko dan ya fi shi arziƙi ne mahaifinsa sananne ne cikin garin Kano? Ko kuwa Areef ɗin ya fi shi wani abun ne da ake buƙata a wajen namiji? Me ya sa aka masa haka? Shin ba su san waye Areef ba? Ko kuwa sun ɗauka yanda mahaifinsa yake haka shi ma yake? Ashe da ma auren da kwanaki Bad Man ɗin ya yi Afrah aka aura masa? Ta yaya hakan ta faru? Ya dai san Areef ɗin ya fi shi kyau, arziƙi da wasu abubuwan da dama. Se dai kuma a wannan fannin yana ganin shi ne ya dace a ce ya samu Didi ba Bad Man ba. Dan kuwa idan dai har hali ne na gari ya san ya fi Bad Man ɗin. Ɓacin rai da baƙin ciki babu abin da ba su sanya zuciyarsa ta kawo ba. Ya kasa haƙura, ya kuma kasa dannewa. Gani yake kamar amanar shi aka ci. Aka raba shi da wadda yake so aka ɗauka aka bawa wanda sam be cancanta ba. Ba tare da Bad Man ya kalle shi ba ya soma ƙoƙarin buɗe ƙofar mota.

"Malam ka tsaya ka min bayanin abin da ke faruwa mana.. Ya aka yi haka? Zuciyata na dab da bugawa." Kaseem ya ƙare yana kallan Bad Man. Kallan Little Bad Man ya yi ya miƙa masa hannu a hankali yace

"Let's go.." Babu musu Little ya tafi da sauri wajen nasa. Ganin da gasken motar ze shige ba tare da ya tanka masa ba ya sanya shi faɗin

"Ka ƙi ce min komai.. Hakan na nufin ba ka da gaskiya kenan.." Se a lokacin sannan Bad ya dakata. A nutse ya ɗaga kansa ya dubi Kaseem. "Me yake nufi da ba shi da gaskiya?" Ya tambayi kansa. A fili kuma se cewa ya yi

"Duk yadda ka ɗauka haka ne.." Kansa Kaseem ya dafe. Da ma ya san halin Bad Man ɗin, ba lallai ne ya samu amsar tambayar da ya masa ba. Se dai kuma har ga Allah ze so ya ji yanda aka haihu a ragaya. Ta yadda hakan ta kasance. Wai Areef shi ne mijin Afrah. Kawai se ya juya a matuƙar fusace ya haye motarsa ya figeta da ƙarfin gaske. Ba tare da ya kalli inda Bad Man da Little ke tsaye ba ya sake baiwa motar gudu ya bar wajen. Taɓe baki Bad Man ya yi daidai lokacin da ya kalli Little da ke faɗin

"Me aka yi wa Uncle?" Se da ya ɗan yi murmushin gefen baki kafin yace

"Ba shi da lafiya.." Rashin sanin amsar da ze bayar ne ya sanya shi yin shiru kawai. Daga haka suka faɗa cikin motar. Kai tsaye Bad ya tashi motar suka fice daga gidan kamar ko yaushe ba tare da ya bi ta kan mutanen Daddy ba.

... Tun da ya ji labarin rufe gidan Ladi hankalinsa ya ƙi kwanciya. Musamman idan ya tuna tona mata asiri da ya yi ya san idan ta ɓaɓe mata za ta iya ambatar sunansa. Haɗa kayansa yake yi cikin wata bagco dan kuwa ko me ze faru yau ba se gobe ba ba ze sake kwana cikin garin Kano ba. Daidai yana ida haɗa kayan aka turo ƙofar ɗakin. Ya ɗaga kai da sauri abinka da mara gaskiya.

"Huuu Bad.. Ashe kai ne.." ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya.

"Za ka iya kama shi.." Bad Man ya faɗa yana yin nuni da Hero. Babu ɓata lokaci wanda suka shigo tare da Bad Man ya saka hannu ya riƙo Hero. Waro ido Hero ya yi. Kar fa ya je har ta kwaɓe da shi tun kafin ya bar cikin garin nan? Ya tambayi kansa. A fili kuma se ya kalli Bad Man yace

"Haka za mu yi da kai Abokina? Me na maka? Na ɗauka ko me ye ya shiga tsakanina da kai kai me iya rufa min asiri ne?" Ko nuna ya ji abin da ya faɗa ma be yi ba se ficewa daga cikin ɗakin da ya yi. Hero ya yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya ƙwace kansa, se dai da yake mutumin ƙwararre ne wajen kama masu laifi kuma kakkaura ya sa ko gezau be yi ba, a haka har ya fitar da Hero daga cikin ɗakin.

.. Ɗaga kai Little ya yi ya kalli Bad Man lokacin da ya shigo cikin motar. Murmushi kawai ya sakar masa ya maida dubansa kan wayar Bad ɗin da ke hannunsa ya cigaba da dannawa. Yana shirin tayar da motar wayarsa ta soma ruri. Se ya dakata ba tare da ya kalli wayar ba. Kamar ba ze kulata ba se kuma a nutse ya saka hannu ya karɓi wayar da Little ɗin ke miƙo masa yana faɗin

"Ana kiranka.." Kai tsaye duba me kiran ya yi. Sam be yi tsammanin ganin kiran Mom ɗin ba. Se dai kuma numberta ke yawo a saman screen ɗin wayar tasa.

"Mom..!" Ya faɗa yana dafe kansa dan ya san zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi..

Asslm.

A cigaba da min uzuri kar ku ga ba kwa samun Update kullum. Ba ni da lafiya ne. Kawai dai daurewa nake yi a hakan nake samu na yi. Toh ranar kuma da jikin ya ƙi min daɗi shi ne ranar da za ku ga ban yi Update ba. Saboda haka a yi manage da wannan dan wallahi da ƙyar na yi.

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO57*

___Daga can ɓangaren Mom tace

"Ina ta kiranka ba ka ɗauka ba?"

"Ba na kusa ne Mom." Ya faɗi hakan kansa na kallan waje.

"Ohk toh yanzu ka na ina ne? Ka taho nan ɗin ne? Ko kuwa ka zaɓi inda za ka je." Numfashi ya ɗan zuƙa kana ya fesar da shi a lokaci guda. Yace

"Mun yi magana da Daddy.. Ya ce babu inda zan je."

"Oh my goodness! Wai kenan ni yanzu ba zan iya saka ɗana ya yi wani abu ba? Fisalillahi.. iyeee??" Ta ƙare a zafafe, dan babu ƙarya ta fusata. Shiru ya yi dan be san me ze ce mata ba. Se dai kuma ba ya so ta sake masa magana a kan barin ƙasar, dan haka yace

"Amm kar ki damu Mom, zan shawo kansa. Ba se kin sake kirana ba. Ina isa ko ma ina ne zan kira ki." Sauke ajiyar zuciya Mom ta yi sannan tace

"Toh shi kenan. Ka kula da kanka dai tun da ba na kusa."

"Umhum." Ya amsa da hakan yana ajje wayar. Daga haka ya tayar da motar suka bar wajen.

... Fitowarta kenan daga ɗakin Abeey, hannunta ɗauke da flask me nutsatstsen kyau. Se ta ji an yi sallama. Ta ɗaga kai ta kalli me sallamar daidai lokacin da take amsawa. Murmushi Fatima ta yi tana ƙarasawa inda Ummeeyn take. Cikin girmamawa tace

"Barka da wannan lokaci Umma.."

"Barkanki dai yarinya.. Kin zo lafiya?" Ta tambaya bayan ta maida mata da martanin murmushin.

"Ehh Alhamdulillah.."

"Toh madallah.." Daga haka se shiru ya wanzu na en wasu sakanni. Kafin Fatima ta katse shirun da faɗin

"Umma Afaaf na nan?" Se a lokacin sannan Ummeeyn ta gane wace Fatiman. Don kuwa tun ɗazu take ƙoƙarin lalubo wace ce ita ta kaasa.

"Tana ciki.." Ummeey ta faɗa har lokacin da murmushi kan fuskarta. Se ta miƙe daidai lokacin da take furta

"Yawwah na gode.." Daga haka ta wuce ɗakin Lulun. Kasancewar ƙofar a ɗan tokare take kawai ya sanya ba ta tsaya ƙwankwasawa ba, kai tsaye ta tura ƙofar ta shige bakinta ɗauke da sallama. Kamar daga sama ta jiyo muryar Masoyiyarta. Se kuwa zumbur ta yi saurin tashi zaune.

"Oyoyo Masoyiya.." ta faɗa har cikin ranta tana jin wani irin farin ciki. Ƙarasawa Fatima ta yi ta rungumeta tana faɗin

"Masoyiyatah matar aure.." Ta faɗa tana murmushi. Hannu Lulu ta saka ta ture hannunta bayan ta jefa mata harara tace

"Ke dai haka za ki ƙare.."

"Oho dai.." Fatima ta faɗa tana dariya. Neman waje ta yi ta zauna gefen Lulun.

"Ya mu'allim ba ya nan ne..?" A niyyarta ta buɗe baki tace "Oho masa" Se dai kuma a karo na farko ta ji be kamata har yanzu ta din ga bari Fatiman ta san yanda zamansu da Gwanin ke kasancewa ba. Don haka se ta jefa mata harara tace

"A'ah ga shi a bayana.." Dariya Fatima ta yi sosai har da tsintsirawa.

"Wai Masoyiya me ye haka ne? Wannan maganganu da ki ke ta yaɓa min. Ko dai ba ki yi farin cikin zuwana ba..?" Ta ƙare tana langaɓar da kai gefe.

"Ke Allah kuwa a'ah Masoyiya.. Na ji daɗi fiye da yanda ki ke tsammani."

"Shi ya sa ma na ga har kin kawo min ruwa." Fatima ta faɗa tana jefa mata harara.

"Toh yi haƙuri.." Ba tare da ta jira amsar Fatiman ba ta miƙe cike da takatsantsan gudun kar Fatiman ta fahimci wani abun. Ta wuce wannan ƙaramin ɗakin ta ɗauko ɗaya daga cikin jug ɗinta me shegen kyau. Fita ta yi daga ɗakin zuwa tsakar gida. A nan ta samu Ummeeey. Ta yi ƙasa da kai dan har yanzu ba ta dena jin kunyarta ba. Se dai ta maaze kawai tace cike da nutsuwar da tafi wadda ta sameta a kwanakin baya.

"Ummeey.."

"Na'am Afaaf.. kin samu kin fito kenan?" Se kawai ta yi yaƙe ba tare da tace komai ba. Ganin da Ummeeyn ta yi idan dai har ta tambayi Lulun jikinta kunya take bata ya sanyata ƙin tambayarta a yanzun.

"Ruwa za ki ɗiba ne?" Ummeey ta tambaya tana kallan jug ɗin hannunta. Se ta jinjina kai tana faɗin

"Ehh baƙuwa na yi."

"Kawo na ɗibar miki cikin randa dan na san yanzu haka ya yi sanyi." Da ma ita ma abin da ya fito da itan kenan, don ta san randar Ummeeyn akwai ɗaukar sanyi. Har tana shirin miƙa mata jug ɗin se kuma ta ga kamar hakan be dace ba. Dan haka se kawai ta yi murmushi tace
Chapter 62 · 0% Book details