← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 122

Sashe 53

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rungume yake da ita cikin ƙirjinsa kamar wanda ze maidata ciki. Wata kalar soyayya da tarin tausayinta yake ji. Se a yanzun yake jin haushin kansa da ya gaza haƙuri ya ƙyaleta bayan yanda tarin tsoro da kuma firgici suka gama bayyana kansu tattare da Lulun. Hawaye kawai ke zubowa daga cikin idanunta, babu sauti ko kaɗan. Hatta numfashi da ƙyar take ajjewa. Jikinta kuwa ko hannunta ba ta iya motsawa saboda yanda take ji kamar an tsatstsaga mata ilahirin jikinta ne. Kawai se ya ƙurawa fuskar tata ido yana cigaba da kallanta. Gaba ɗaya ya ma rasa da wanne irin baki ze yi amfani wajen ba ta haƙuri da kuma kwantar mata da hankali. Dan ko ba a faɗa ba ya san ita kaɗai ta san me take ji a jikinta. Dan kuwa ko daga yanayin yanda take sauke numfashi ya isa ya nuna maka yanda ta galabaita. Wajen minti 10 a haka be yi ƙoƙarin yin komai ba dan shi kansa ya gaza aikata komai. Duk da yanda yake jin wani irin farin ciki na mamaye shi, amma tausayinta da yake ji ya danne komai. Hakan ne ya sa shi kansa jikinsa a matuƙar sanyaye yake. Hannu ya kai kan fuskarta ya share mata hawayen da suka ƙi tsayawa da zubowa. Karo na farko ya buɗe baki a nutse yace

"Ki yi haƙuri.." Idanunta a rufe suke gam, se dai ba bacci take yi ba. Tsananin azaba ne kawai ya sanya hakan. A nutse ya ɗaga kanta ya ajje kan pillow har lokacin ya kasa janye idanunsa daga kanta. Kai tsaye banɗaki ya faɗa duk da har lokacin be dena jin zazzaɓin ba amma a haka ya yi wanka da ruwan sanyi. Bayan shuɗewar wasu mintuna ya fito. Ya ɗauki wata jallabiyya mara nauyi ya saka sannan ya dawo kan gadon. Abin da ya ba shi mamaki har lokacin hawayen be tsaya ba, ba kuma ta buɗe idanunta ba. Ba kuma ta motsa daga inda ya barta ba. Wani sabon tausayinta ya sake kama shi. Ya runtse idanunsa yana sake jin haushin kansa. Kai tsaye inda flask ɗin da suke ajje ruwan zafi yake ya nufa. Cikin sa'a kuwa akwai ruwa, ya ɗauka ya wuce da shi banɗakin ya sirka shi daidai misali sannan ya sake fitowa. A hankali ya ƙarasa kan gadon idanunsa na kanta. Ya saka hannunsa da niyyar ɗagata gaba ɗayanta se ta miƙa hannunta da shi kansa take ji ya mata nauyi ta ɗaga shi alamar kar ya matso inda take. Ya ɗan lumshe idanunsa yana buɗewa still a kanta. Se ya sake matsawa ɗin se dai ya sauke hannunsa. Ya sunkuyar da kansa saitin kanta cikin lallashi yace

"Ki yi haƙuri na miki wanka.. Za ki ji daɗin jikinki.." Wasu sabbin hawayen ne suka sake zubowa a kan kuncinta. Se ta shiga girgiza kai. Cikin ƙarfin hali ta buɗe baki da ƙyar tace

"Ka ƙyale ni.. Ka ƙyale ni.. Ka ƙyale ni.." Hannu ya kai ya shafi sumar kansa cikin rashin sanin abin yi. Bayan duk abin da ya faru kuma ba ya son sake zama silar sakata kuka. Se dai da za ta daure ta yi wankan ko da kanta ne za ta ji daɗin jikinta ko yaya ne. A hankali ta shiga buɗe idanunta da suka yi jaajir suka kuma kukkunbura saboda kukan da ta sha. A kansa idanunta suka sauka. Ta yi saurin rufe nata idanun kamar wadda ta ga wani dodo.

"Ka matsa ba na san ganinka." Ta sake faɗa da muryarta da ke a dashe. Se da ya sauke numfashi sannan yace

"Don Allah ki yi haƙuri ki dena wannan kukan.." Ya san ta ji shi, amma kuma ya san ba amsawa za ta yi ba. Ya san idan har ya ƙyaletan cigaba za ta yi da zama ba za ta tashi ba. Hakan ne ya sanya shi matsawa inda take ɗin ya sake saka hannunsa ya ɗagota ya sanyata cikin jikinsa. Ya lulluɓeta da duka hannayensa biyu. Duk wani ragowar kuzarinta ta saka dan tashi daga jikinsa, se sai ko kaɗan ta kasa. Da dai ta fahimci ba abin da za ta iya se kawai ta haƙura ta cigaba da kukanta da babu sauti se hawaye kawai. Wajen minti 20 suka ɗauka a hakan yana jin yanda take sauke numfashi a hankali. Tausayinta na sake ratsa shi, ji yake tamkar ya maidata ciki. Se dai da hakan ba ze yiwu ba se ya sake yi mata kyakkyawan masauki a jikin nasa. Se da ya tabbatar ta nutsu ta haƙura da ƙoƙarin tashin da take yi sannan ya miƙe. Ba tare da saninta ba ya ɗauketa kawai gaba ɗayanta se bandaki.

"Ni ka sauke ni.." Shi ne abin da take faɗa a hankali. Be kulata ba har se da ya kaita ciki. Ya kalleta a nutse lokacin da ta buɗe lumsassun idanunta dake cike da bacci. Ya san a yanzu ba ta buƙatar komai se bacci, idan kuma yace ze tsaya taimaka mata dan ta ji daɗin jikinta za a ɗauki lokaci, dan haka cikin taushin murya yace

"Ki yi wanka ki zo ki yi bacci.." Ita dai tana tsugunne kanta kife a kan cinyarta tana jin yanda gaba ɗaya jikinta ke amsa mata. Fita ya yi daga banɗakin ya nemi waje ya tsaya dan jiranta ta gama. Se dai har wajen minti 10 be ji motsin ruwa ba ko wani abu da ze nuna ta soma wankan ba.

"Ya ilahy.." ya faɗa yana dafe goshinsa. Har ga Allah ba ya so ya sake sakata kuka, ko kuma abin da ze sanya ta sake jin tsoronsa. Amma kuma ya ga alama dole se ya yi hakan, idan ba haka ba su shekara a wajen ba tare da ta yi komai ba. Kai tsaye toilet ɗin ya faɗa tana nan kuwa a inda ya barta. Babu ɓata lokaci ya saka hannunsa ya ɗagota a hankali ka da ya je ya jangwalowa kansa. Da ma ya lafiyar kura bare ta yi zawo. Be ɓata lokaci ba ya shiga yi mata wankan. Ita kam yau Lulu haukacewa ne kawai ba ta yi ba. Ga shi bakin tsiwa ya mutu, ga babu ƙarfin ƙwatar kanta. Se dai duk da haka wani ƙaramin yaƙin ma aka yi a wajen nan, duka dai ya jure ya kuma daure. Haka tana ji tana gani ya wanketa tass sannan suka fito. Zuwa lokacin babu laifi ta ɗan ji jikinta ya saki ba kamar ɗazun ba. Se dai har yanzun ji take kamar ba ita ba. Wata doguwar riga mara nauyi ya ɗakko mata ya ƙaraso inda take da niyyar sanya mata. Ta girgiza kai ba tare da ta ɗaga ido ta kalle shi ba. Hawayenta suka zuba a kan tawul ɗin dake ɗaure a jikinta. Cikin rawar murya tace

"Ka ba ni zan saka.." Babu musu ya miƙa mata. Gaba ɗaya ma se ya bar wajen dan ya ba ta damar sakawa a nutse. Se kuwa a lokacin ta iya saka rigar daidai lokacin da ta lumshe idanunta wasu sabbin hawaye na kawowa a kan fuskarta saboda yanda take jin jikinta. Tana gama sakawa ta kwantar da kanta kan gadon. Lura da hakan ne ya sanya shi ƙarasowa dan gyara mata kwanciyar. Tana ganinsa ta yi saurin tashi zaune a tsorace. Da tana da ƙarfi da tashi za ta yi ta bar wajen. Se dai ba za ta iya ba.

"Yi kwanciyarki.. Babu abin da zan miki.." Ita dai ba ta kwanta ba, ba kuma ta ɗaga ido ta kalle shi ba. Ganin da ya yi idan be bar wajen ba ba za ta kwanta ba ya sanya shi matsawa daga wajen. Se da ta dena jin motsinsa sannan ta ɗaga kumburarrun idanunta ta kalli wajen. Ganin da ta yi ba ya wajen ne ya sanyata jan jikinta da ƙyar ta haye kan gadon, ta kwanta duk da a tsorace take.. Duk da jikinta babu daɗi amma da yake baccin na kanta cikin ƙanƙanin lokaci kuwa ya yi awon gaba da ita. Se a lokacin Gwani ya sauke wata ƙatuwar ajiyar zuciya yana faɗin

"Alhamdulillah.." Ya ƙare yana fesar da iska daga bakinsa. Se ya ƙarasa ya lulluɓa mata sabon bargon da aka zo mata da shi cikin kayanta. Dan ya san za ta ji daɗinsa. Ya yin da ya koma gefe ya zauna kawai yana kallanta cike da tausayi, da kuma wata irin ƙauna.

... A nutse take takowa cikin ɗakin kai se ka rantse tana sane take irin wannan takun. Se dai sam ba haka ba ne, tsananin yanda nutsuwa da kuma tarin kamala wanda ya kasance a tare da ita tuntuni shi ne ya haifar da hakan. Ko wannan kaɗai na ɗaya daga cikin abin da ya sa Mom ke kishi da Mommahn. Musamman idan suka shiga taro, yanda Mommahn ke kereta a kan kowacce kalar shiga ta yi. Duk kuwa da yanda za ta aro wata uwar izza ta yafawa kanta, hakan ba ya hana mutane nuna sun fi yin Mommahn ba. Saboda ita tana yin komai nata ne very classy. Babu garaje kuma babu nuna ita wata ce. Yau ɗin ma tun da ta ɗaga ido ta mata kallo ɗaya ba ta sake kallan inda take ba. Saboda yanda wani kishi ya zo ya tirniƙe mata ƙirji. Haushin Mommahn na sake kamata. Ta wani haɗe rai tana maida dubanta kan Dad dake zaune kan kujerar dake kusa da tata. Cikin ladabi Mommah ta kalli Daddy bayan ta sakar masa murmushi tace

"Barka da wannan lokaci Yallaɓai"

"Yawwah Barka dai Rankiyadaɗe."

"Barka da wannan lokaci.." ta ƙare tana kallan Mom. Se da Mom ta wani ɗauke kai kamar wadda wata er aiki ta gaisar sannan tace a yatsine

"Barka.." Sarai Daddy ya lura da yanda ta amsa ɗin amma ya share. Dan ba ya so ya taso da wata matsalar kuma a yanzu haka. Mommah ba ta damu da yanda Mom ɗin ta amsa ba ta nemi waje ta zauna ba tare da ta sake kallan inda Mom take ba. Se a lokacin sannan Daddy ya buɗe baki yace

"Toh kin ji Abokiyar zamanki za ta je ganin likita? Ina fatan dai kun yi sallama?" Daddy ya ƙare maganar yana kallan Mommah. Se ta girgiza kai tana murmushi tace
Chapter 53 · 0% Book details