← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 122

Sashe 30

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ka ƙi ka saurare ni.. Zuciyata na dab da tarwatsewa wallahi" ta faɗa da iya gaskiyarta saboda ita kaɗai ta san abin da take ji a gaba ɗaya jikinta. Ɗan lumshe idanunsa ya yi yana ji a karo na farko tausayinta ya kama shi. Duk wannan rashin kunyar babu ita, duk wannan ji ji da kan babu shi, ta koma wata abar tausayi, gaba ɗaya ta zama kamar ba ita ba, se kace an chanjata.

"Shi kenan, ya isa haka.. Faɗa min waye a cikin hoton nan?" Ganin tana ƙoƙarin fara magana duk da kukan take yi ya sanya shi girgiza kai yace

"Kukan ya isa haka. Idan kuma cigaba za ki yi in tashi in tafi." Ya yi maganar yana ƙoƙarin miƙewa. Da sauri tace

"Na dena don Allah.." ta faɗa tana kai hannunta fuskarta ta shiga share hawayen fuskar tata. Se da ta gama gogewa sannan ta shiga sauke ajiyar zuciya kafin da kukan ya tsaya ta soma faɗin

"Ban san waye shi ba, mun zo wucewa kawai ya rungume ni.. A lokacin kuma se da na mare shi saboda ganewar da na yi ba mutumin arziƙi ba ne.. Wallahi ban taɓa ganinsa ba, ban taɓa sanin waye shi ba.. ba kuma ni da masaniya a kan hoton da aka ɗauka. Ni ba haka nake ba wallahi, ko waye za ka tambaya.." Shiru ya yi yana nazarin maganganun nata, yana kuma cigaba da kallanta kamar me son gano gaskiyar abin da ta faɗa daga cikin fuskarta. Yanayinta kaɗai ya isa ya nuna masa abin da take faɗa gaskiya ne, musamman yanda ta gama ruɗewa cikin mintuna kaɗan. Gaba ɗaya kuma ta fita a hayyacinta kamar ba ita ba. Har kuma ta zauna tana neman da ya saurareta, shi ɗin da ko magana ba ƙauna take ta haɗa su ba. Kenan idan dai har ya fahimci zancenta da kyau akwai wani abun a ƙasa. Se dai duk da haka akwai wani abun shi ma da yake so ya ji amsar daga bakinta ba a bakin wani ba. Se dai kafin nan se ya fara da

"Za ki iya shaida fuskarsa?" Tun kafin ya dire tambayar ta shiga jinjina kai, tana jin wani sanyi na ratsata. Ko babu komai ta samu ya fahimceta ko da ba duka ba ne..

.✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO39*

__Shi kenan.." ya faɗa yana miƙewa. Se ta bi shi da kallo kamar wata sokuwa, daidai lokacin da ya sake komawa ya zauna yace yana kallanta

"An taɓa ganinki za ki shiga wani gida, gidan da mutane da dama sun san na su waye. Wanda mutane kaɗan me ba su sani ba saboda rufesun da ake yi.. Me ya kai ki gidan?" Ya tambaya yana kafeta da idanunsa. Kallan nasa dai take yi ta kasa furta komai. Se da ya kai ƙarshen maganar tasa sannan tace

"Wanne gida?" Ta tambaya da muryarta dake a dusashe. Shiru ya yi still dai yana kallanta. Kamar wanda ke bata haske da kallan da yake mata haka ta ji, tabbas idan dai har ta fahimci inda tambayarsa ta dosa wannan gidan da Abida ta kaita yake nufi. Ta riga ta san ba ta taɓa sanin wani gida makamancinsa ba ballantana ta tsaya dogon tunani wajen bambance wanda yake nufi. Dan haka tunda ta tsaya ta yi nazari se ta fuskanci abin da yake nufi. Se ta ɗaga kai da sauri ta kalle shi tace

"Wallahi ja na ta yi tace in rakata, bani da masaniya a kan gidan, na ɗauka gidan en uwansu ne.." ta faɗa tana jin wani sabon kukan na taho mata.

"Gaskiya za ki faɗa min, kar ki ɓoye min komai.." ya katseta da fadin hakan. Jinjina kai ta yi babu musu ta shiga ba shi labarin yanda komai ya faru tiryan_tiryan. Tsananin mamaki ya kama shi, ya ma kasa furta komai tun bayan da ta ƙare bayar da labarin ta yi shiru. Ashe har yanzu akwai irin waɗannan mutanen? ya zama dole ya ɗauki mataki a karo na biyu ko da hakan ba ze yi aiki ba a wannan karon ma ze jarraba. Abin da kuma ya sake kashe shi a zaune shi ne ambatar sunan Abida da ta yi a matsayin wadda ta jata zuwa gidan. Duk da ita ɗin sabuwar ɗaliba ce, amma ya shaida sunan nata. Be kuma taɓa tsammatar wannan ɗin halinta ba ne.

"Ya salaam.." ya faɗa yana ɗan dafe kansa idanunsa a lumshe. Ya shafe wajen minti 2 a haka ba tare da yace komai ba, se zuwa can yace a nutse

"Ki kwanta ki yi bacci.. Za mu yi maganar gobe" Daga haka ya miƙe be jira cewarta ba ya fice daga wajen zuwa inda shimfiɗarsa take. A ranar dai daga shi har ita babu wanda ya rintsa, kowa da abin da yake tunani.

Juyawa ya yi ya kalli gadon da take kai, ga mamakinsa se ya hangi idanunta masu sheƙi a buɗe, alamar ba bacci take yi ba. Ya ɗan lumshe idanunsa sannan ya ɗan matsa kusa da gadon yace

"Ki tashi.." ya faɗa a nutse kuma a hankali. Abin da ya sake tabbatar masa da ba ta yi bacci ba shi ne yanda da ya yi mata maganar tafarar ɗaya ta miƙe zaune a kan gadon. Ya ɗan fesar da iska daga bakinsa yana shigewa cikin toilet ɗin dan ɗauro alwala.

Wajen ƙarfe 6 ne suka shigo gidan daga masallaci, kai tsaye ɗakin Ummeey ya wuce, ya yin da Abeey ya wuce nasa ɗakin dan ya samu ya ga ko ze iya baccin da be yi ba saboda kwana biyu da yake fama da matsanancin bugun zuciya, wanda ya ƙi faɗawa Gwani har yanzu, duk da ya san ba shi da lafiya amma ba ya son ɗagawa kowa hankali shi ya sa ya ƙi faɗawa ko da Ummeey ce.

Ummeyn na zaune a kan dadduma tana lazumi tun bayan idar da Sallahr da ta yi. Ya shiga ya nemi waje ya zauna, se da ta ida addu'ar da take sannan suka gaisa.

"Ya kasuwar?"

"Alhamdulillah.."

"Toh Allah ya daɗa dafawa" Ummeey ta faɗa

"Ameen Ameen.."

"Ni kam Affan Allah yasa dai lafiya. Tun jiya ban ga ɗiyata ba, ko jikin ne?" Ɗan lumshe idanunsa Gwani ya yi, ya gyara zamansa kafin yace

"Jikin da sauƙi kam Ummeey, zan faɗa mata kin tambayeta.. zuwa anjima za ki ganta."

"Toh Alhamdulillah.. Allah ya ƙara lafiya. Don Allah Affan ka cigaba da kulawa da yarinyar nan, sam ba ta da saurin sabo ballantana mu saba. Har yanzu ta kasa sakin jiki da ni. Ka yi ƙoƙarin janta a jiki sosai In Sha Allah komai ze yi daidai.. Har wannan rashin son cin abincin, ka yi ƙoƙarin ganin ko da ci ne ku dinga yi tare duk dai dan a samu ta dinga ci ɗin." Ya lumshe idanunsa yana sake yabawa da ƙoƙarin da Ummeey take yi, yana kuma sake godewa Allah da ya ba shi uwa kamar Ummeey.

"Toh Ummeey.. An gode, Allah ya saka da alkhairi.." Murmushi kawai Ummeey ta yi a ranta tana cigaba da musu addu'ar daidautawarsu cikin ƙanƙanin lokaci.

... Babu daɗewa ta ida, ta juye shi cikin wani hamshaƙin cup da ya matuƙar haɗuwa. Kai tsaye ɗaukar cup ɗin ta yi ta wuce zuwa inda ɗakin nasa yake. A nutse ta shiga knocking na ƙofar, kamar yanda take yi da, tana jin motsi ta soma ƙoƙarin ajjewa dan barin wajen. Se dai kafin ta kai ga aiwatar da hakan ya gama buɗe ƙofar. Ya maka mata wani kallo yana kallan abin da take ƙoƙarin yi

"Wace irin er qauye ce ke ne? A ko ina se kin nuna shi?" Ya ja tsaki yana yin baya kaɗan.

"Wuce.. ki ajje shi a wajensa.." ya yi maganar yana nuna mata wani keɓantaccen waje dake cikin ɗakin nasa, wanda da alama dama an tanadi wajen ne dan shan Coffee ɗin. Ko kallansa ba ta yi ba ta soma tafiya, duk da jikinta na rawa. Haka ta ƙarasa ta ajje Coffee ɗin duk a tsorace kamar wadda za a ce kett ta gudu. Ko bi ta kansa ba ta yi ba, duk da ma tun lokacin da ya mata maganar ba ta sake ganinsa ba. Ita dai hakan ba damuwarta ba ce, dan haka ta ɗaga en matan ƙafafunta ta fice daga ɗakin. Se da ya gama abin da ze yi sannan ya ƙaraso ya nemi waje ya zauna yana kallan Coffee ɗin. Babu ɓata lokaci ya ja shi ya shiga kaiwa bakinsa a nutse. Har wani lumshe idanu yake yi ba tare da ya sani ba. Har ya gama sha ji ya yi shi ya ma yi masa kaɗan, da so samu ne ya dinga samun ko da 2cups ne, se dai kuma ba ya buƙatar wata maganar ta sake shiga tsakaninsa da ita. Hakan ne ya sanya shi ɗaukar abin da ze ɗauka ya fice daga ɗakin.
Chapter 30 · 0% Book details