← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 122

Sashe 72

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke ni kwata kwata haihuwar ce ba na so ta yi. Ni kaɗai nake so na haihu da Alhaji Matawalle, ba na son kowacce mace ta haihu da shi bayan ni." Mom ta faɗa cikin er ɗaga murya a kuma fusace. Sauke ajiyar zuciya Maimuna ta yi tana tunanin me kuma za ta cewa Mom ɗin ta haƙura. Se dai iya tunaninta ta kasa. Se kawai ta haƙura ta barta ta gama fushin kafin ta zo ta sake lallashinta ko za ta haƙura. Aikuwa ba Mom ce ta saurari Maimuna ba se washegari bayan ta soma dawowa hayyacinta. Da ƙyar da kuma saka bakin Aunt Makiyy suka haɗu suka tausheta sannan ta haƙura. Se dai duk da haka tun daga ranar se ya kasance zaman nasu ma ya chanja. Hatta magana se da Mom ta denawa Mommah, dan idan dai har tace za ta cigaba da mata magana, toh tabbas wataran za a wayi gari a tsinci gawarta saboda baƙin ciki. Ita kam a wajen Mommah hakan ba ƙaramin yi mata ya yi ba. Ko babu komai ta rage mugun iri, ta kuma huta da jin haushin Mom ɗin da kullum ba ta gajiya da shi.

A kwana a tashi, kwanaki na cigaba da tafiya haka zalika kuma cikin kowaccensu na daɗa girma, kwanakinsa na ƙaruwa. I zuwa lokacin duk yanda Mommah ba ta san er aiki se da Yaya Amina ta saka aka nemo mata wata bazawara da mijinta ya rasu ba ta sake aure ba. Ba wata babba ba ce dan ma dai an yi mata auren wuri ne. Baba Atine ita ce wadda Yaya Amina ta samowa Mommah a matsayin wadda za ta din ga tayata aiki, dan kuwa a lokacin Mommah ƙarfin hali kawai take yi. Daddy ma har magana yake mata a kan ayyukan da take yi. Shi ya sa da Yaya Amina ta sanar da shi zancen samar mata er aiki ya yi na'am da hakan ɗari bisa ɗari. Tun daga wannan lokaci Baba Atine ta soma taya Mommah ayyuka waɗanda ba su shafi mijinta ba. Dan kuwa har yanzu duk wani abu da ya shafi Daddy ita ce ke yi, duk da yanda nauyin jiki ya ƙaru. Amma haka take daurewa ta yi komai. Cikin ƙanƙanin lokaci Mommah ta fahimci halin Baba Atinen, mace ce me tsafta da kuma takatsantsan, uwa uba kuma amana. Se ya zamana ba ta wani daɗe cikin gidan ba suka saba, se suka zama tamkar wasu en uwa. Mommah babu ruwanta da cewar Baba Atinen er aikinta ce, janta take yi a jiki kamar er uwatta. Abin da ya janyo shaƙuwa kenan a tsakaninsu. Ta gefe ɗaya kuma Baba Atine ba ta daɗe cikin gidan ba ta fahimci wace ce Maimuna da kuma uwar ɗakinta. Mommah ba ta taɓa mata magana a kansu ba, amma ita da kanta ta ga dacewar ta yi nesa nesa da su kar su ɓata mata aiki. Dalili kenan da ya sanya kodayaushe tana sashen Mommah.

... A nutse take takowa zuwa palourn, hannunta dafe da ƙugunta, tana ɗan yamutsa fuska lokaci zuwa lokaci, saboda yanda mararta ke mata ciwo tun ba yanzun ba. Tun ɗazu take jin ciwo, se dai idan ya zo se kuma ya tafi. Haka dai take cigaba da daurewa, kai ba za ka ce akwai abin da ke damunta ba idan ba ganin lokacin da ciwon ya motso mata ka yi ba. A palourn ta tarar da Baba Atine shirye cikin doguwar rigar atamfa da hijabi. Se da ta nemi waje ta zauna a kan kujera a hankali sannan ta miƙa mata ledar hannunta tace

"Ga abin da za ki kai mata nan.. ki ce na gode." Mommah ta faɗa. Hannun Baba Atine ta saka ta karɓa tana faɗin

"Toh shi kenan Hajiya.. Shi kenan?" Jinjina kai Mommah ta yi lokaci ɗaya tana faɗin

"Ehh.."

"Toh bari na wuce." In ji Baba Atine tana ficewa daga ɗakin. Da addu'a Mommahn ta bita da ita tana miƙewa ta shige ɗakin da ta fito. Wayarta ta ɗauko a karo na barkatai tana ƙoƙarin kiran number Yaya Amina, se dai kuma yanzun da yake ta ɗauki mintuna ba ta ji wani ciwo ba ya sanyata ajiye wayar da nufin idan ciwon ya ƙaru se ta kirata, dan yanzu ba ta son ɗaga mata hankali. Se kawai ta cigaba da zama cikin ɗakin tana maimaita sunan Allah a zuciyarta, idanunta a lumshe kamar me jin bacci..

Daidai ta fito daga sashen suka yi kaciɓus da Mom.

"Barka da wannan lokacin.." Ta faɗa tana shirin wucewa, kasancewar kusan kodayaushe gaisuwa ce kaɗai ke haɗata da ita. Bayan ita babu wani abu. Kamar ko yaushe yau ɗin ma dai fuskarta babu yabo babu fallasa tace

"Barka.. Ina za ki je?" Mom ta tambaya tana kallanta. Mamakin tambayar ne ya sanya Baba Atine kallanta, se kuma ta sunkuyar da kanta tana faɗin

"Hajiya ce ta aike ni."

"Toh ya yi.. Da ma ni ma aiken nake so na yi.. kuma ga shi Maimuna ba ta nan. Ko za ki taimaka ki wuce ki siyo min?"

"Toh Hajiya.. Se dai kuma.."

"Se dai kuma me? Idan zuwan ne ba za ki yi ba gwara ki faɗa min tun yanzu na aiki wani." Se ta girgiza kai da sauri tana faɗin

"A'ah ba haka ba ne.. Kawo." Ta yi maganar tana miƙa hannu ta karɓi aiken da Mom ɗin ke faɗin za ta mata. Se da ta kwatanta mata inda za ta je da abin da za ta mata sannan Baba Atine ta yi hanyar fita, ya yin da Mom ta yi cikin gida. Se da ta tabbatar Baba Atinen ta fita sannan ta dawo a hankali cike da takatsantsan ta shige sashen Mommah. Duk da yanda take ji a jikinta kamar ba ƙalau take ba, hakan be hanata jefa idanunta ko za ta hangi Mommah ba. Se dai har ta gama hangenta ba ta gano kowa ba. "Toh tana ina?" Ta tambayi kanta. Se ta cigaba da takawa a hankali yanda ta san ba za a ji takunta ba ta ƙarasa har ƙofar bedroom ɗin Mommah, ta saka hannu ta tura shi a hankali. Cikin sa'a kuwa se ga shi ƙofar a buɗe take. Se ta soma leƙa idanunta dan ganin Mommahn na ciki ko kuwa ba ta ciki? Sauke numfashin da ta ji an yi ne ya sanyata sake buɗe ƙofar sosai yanda za ta iya ganin komai. Mommahn na kwance kan gadon bayan tahowar ciwon da take tunanin ze tafi kamar yanda yake mata ɗazun, se dai har yanzu shiru, babu abin da yake se ƙaruwa. I zuwa lokacin gaba ɗaya ba ta da kuzarin da za ta iya kiran waya. Ilahirin jikinta rawa yake yi, wayar da ke hannunta tuni ta kama gabanta ta yi nata wajen. Hannunta na riƙe da ƙugunta tana cigaba da kiran sunan Allah a hankali, ban da gumi babu abin da ke tsatstsafowa a kan goshinta. Mom ba ta san lokacin da ta saki ƙofar ba har tana neman yin tuntuɓe garin son shiga cikin ɗakin. Se kuma ta dakata kamar wadda aka tsayar. Idan ta shiga an ya ba ta yi hauka ba? Shin Sa'adahn haihuwa za ta yi ko kuma yaya? Me ya kamata ta aikata a irin wannan lokacin da ya fi kama da na ɗaukar fansa? Wannan lokacin da ya fi kama da lokacin cikar burinta? Duk ita kaɗai take lodawa kanta waɗannan uban tambayoyin da ko shakka babu babu wanda ze amsa mata a yanzu dai kam. Cigaba da murƙususun da ta lura Mommah na yi ne ya sanyata dawowa cikin hayyacinta, ta yi shiru tana sake nazarin abin da ya kamata ta yi. Zuciyarta babu ko ɗigon tausayin Mommahn da ke juyi a kan gado ita ɗaya tana neman agaji. Duk kuma da yanda ita kanta take jin ɗan cikinta na juyawa yana dunƙulewa waje ɗaya ba ta bi ta kan hakan ba. Burinta kawai rayuwar Sa'adah da abin da ke cikinta su wuce inda ba a dawowa a yau ɗin nan. Ta saki wani murmushi tana jan ƙofar ta rufe, ta yi amfani da mukullin jikin ƙofar ta kulle ɓam, sannan ta zare mukullin. Murmushin ta sake saki tana dafe cikinta. Ta riga ta san Sa'adah kam ta ƙare mata a yau ɗin nan. Babu wanda ze yi tunanin tana ciki, ko da ma an ji motsinta tana da tabbacin kafin a kai ga taimaka mata rai ya yi halinsa. Ɗaga mukkulin ta yi tana juyawa tana kalla da idanunta, murmushi ya ƙi barin fuskarta. A fili ta furta

"Allah Ya ji ƙanki Yallaɓiya." Daga haka ta ja jikinta ta fice daga cikin ɗakin, duk da yanda take cigaba da jiyo motsi da kuma sautin maganar Mommah. Kai tsaye nata ɗakin ta wuce har lokacin dafe da cikinta. Maimuna da ke kallanta tace

"Hajiya lafiya kuwa?" Se da ta ɗan yi shiru tana runtse idanunta kafin can ta buɗe tace

"Ba na tunanin haka.. Ina ga haihuwa zan yi."

"Toh Hajiya kawo a kirawo Alhaji a sanar da shi. A kuma kira Hajiya Makiyya a sanar da ita." Girgiza kai Mom ta yi kafin tace

"Ba na buƙata.." Daga haka ta wuce nata ɗakin. Maimuna ta bi ta da kallo cike da mamaki da tausayawa, dan ta lura da yanda uwar ɗakin nata ke cigaba da yamutsa fuska. Amma ba ta san dalilin da ya sa tace ba ta so a kira kowa ba.
Chapter 72 · 0% Book details