← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 122

Sashe 92

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tana nan.." Daga yanda ya yi maganar kaɗai ya isa ta fahimci kamar be so ya faɗi hakan ba. Se dai ba ya so ya sake yin wani laifin da ze sa Mommahn ta ji haushinsa bayan rannan. Ba tare da ta bi ta kan yanda ya yi maganar ba tace

"Toh ka yi maza ka dawo min da ɗiyata yanzun nan ba se an jima ba. Idan kuma ba haka ba ranka ze ɓaci Areef." Daga haka Mommah ta katse wayar tana lumshe idanunta.

"Allah Ka ƙara daidaita tsakaninsu gaba ɗaya.." Ta faɗi hakan har cikin ranta tana jin daɗin yanda wannan ranar da suke ta jira ta zo..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO73*

____An ɗauki wajen minti 1 bayan kashe wayar Mommah amma be sauketa daga kunnensa ba. Se can kuma ya sauke a hankali yana sake maida dubansa kan Didi da har lokacin jikinta be dena rawa ba. Ya ɗan lumshe idanunsa a hankali zuciyarsa na hasaso masa abubuwa da dama. Musamman kwanaki kaɗan da suka wuce cikin gidan nan. A karo na barkatai ya sake sauke ajiyar zuciya kafin a hankali ya saka hannunsa ya zame Didin daga jikinsa, tun kafin ya saketa ta yi ƙoƙarin tashi gaba ɗaya. Ya yi amfani da hannunsa wajen sake riƙeta sosai ya zuba mata lumsassun idanunsa. Haka nan kawai yau ɗin ya ji wani tausayinta na kama shi, abin da be taɓa ba ji ba kenan tun zuwanta gidan.

"Don Allah.." ta faɗa tana girgiza kai tana sake yunƙurin tashi. Ya buɗe idanunsa sosai a kanta kamar me karantar wani abu daga cikin fuskar tata. A hankali kuma se ya saketa yana miƙewa ma gaba ɗaya daga kan gadon. Hijab ɗinta ya miƙa mata muryarsa can ciki yace

"Saka.." Da sauri ta ɗauka jikinta har rawa yake yi. Idanunta kuma sun yi ja. Sam ta kasa haɗa ido da shi, dan haka ko kallan fuskarsa ma ba ta yi ba. Yin gaba ya yi yana tafiya a hankali, se dai saboda yanda jikinsa yake babu ƙwari, ya sanya tafiyar tasa ta zama wata iri. Har wani ɗan layi yake kamar wanda ya sha wani abun. Ba tare da ya lura da hakan ba ya cigaba da tafiya. Binsa take yi a baya ƙirjinta na bugawa, tsoro take ji kar yace ɗaki ze maidata. Yanzu idan Mommah ta ganta da wane ido za ta kalleta? Me za tace mata? Dab da za su shiga sashen Mommahn ta dakata, lokacin da idanunta suka cika taff da ƙwalla. Har lokacin ta kasa kallansa tace muryarta na rawa.

"Don Allah ka juya.." Dakatawa ya yi jin abin da tace. A hankali ya ɗan cije laɓɓansa kafin ya saki. Kamar ba shi ba, dan hatta muryarsa a cunkushe take yace

"Ki yi haƙuri.." Wallahi ba ta san lokacin da ta ɗaga ido ta kalle shi ba. Haƙuri? Shi ɗin? Kuma ita yake bawa? Dukka ta jerawa kanta waɗannan tambayoyin. Ba ta taɓa zaton jin kalmar haƙuri daga bakinsa ba. Ba ma ita ba, duk wata tattausar kalma daga gare shi. Ban da ma a kwana biyun nan da ya chanja da abubuwa da dama ba ta yi tsammaninsu daga gare shi ba. Kawai se ta cigaba da binsa har ɗakin Mommahn. Fakar idanunsa ta yi tai wuff ta faɗa ɗakin da suke kwana ita da Lulu. Murmushin gefen baki ya yi kafin ya girgiza kai yana kai hannu ya shafa sumar kansa sannan ya juya dan ficewa daga ɗakin.

"Areef.." Mommah ta faɗa tana ƙarasowa cikin palourn. Sam be yi tsammanin Mommahn za ta fito a wannan lokacin ba. Abin da ya sa ya shigo har ciki kenan. A sukwane ya juyo yana ɗan cigaba da shafa kansa, kansa a ƙasa ba tare da ya kalleta ba. Tamke fuska Mommah ta yi dan ka da ma ya ɗauka abun da wasa.

"Ka ƙyale min 'ya na faɗa maka Areef.. Ban son rashin kunya.. Wallahi kar na sake ganin ka ɗaukar min 'ya zuwa wani wajen, idan ba haka ba zan saɓa maka."

"Mom..mah.." Ya faɗa a rarrabe. Ɗaga masa hannu ta yi kafin tace

"Na dai faɗa maka.. Wuce ka tafi." Kamar ya yi me, haka dai ya ja jiki ya fice daga ɗakin jiki a sanyaye.

"Kaii!! Didi yaushe kika shigo?" Lulu ta faɗa tana kallan Didi dake kwance kan gadon lulluɓe cikin bargo kamar me jin sanyi. Shiru ta yi ba tace komai ba, dan ba ta so Lulun ta fahimci komai. Neman waje Lulu ta yi ta zauna tana kai hannunta tace

"Didi.." ta yi maganar lokacin da ta yaye bargon. Riƙewa Didi ta yi da sauri ta sake rufe kanta.

"Ohh na gane.. Ai dole ki ji kunyata. Ni wallahi Didi ban san lokacin da kika zama haka ba. Shi ne ke ga me miji har da binsa ɗaki a gidan surukai." Ba ta san lokacin da ta yi saurin yaye bargon gaba ɗaya ba, ta ɗaga kai tana kallan Lulu cike da mamakin abin da ke fitowa daga bakinta. Kallan juna suka shiga yi. Kafin can Didi tace

"Ke ma haka kike tunani?"

"Aou se waye na biyu me irin tunanin nan?" Hannu Didi ta kai duk da a sanyaye jikinta yake ta buge hannun Lulu tace

"Da gaske fa nake don Allah."

"Da gaske nake fa Didi." Lulu ta faɗa tana ɓata fuska.

"Na shiga 3." Didi ta faɗa tana ji kamar ta fasa ihu. Gefe guda kuma tana ji tamkar ƙasa ta tsage kawai ta shige, ko kuma wani abun makamancin hakan. Kamar wadda ke a gaban alƙali tace

"Wallahi Lulu ba kai kaina na yi ba, shi ne ya ja ni.. Don Allah kar ki min irin wannan fassarar. Idan ke kin ce haka saura kuma me za su ce?" Didi ta faɗa kamar za ta yi kuka.

"Toh shi kenan, na yadda da ke. Amma me ye kike kuka?" Kawai se ta rungumeta ba tare da tace komai ba tana jin wata ƙwalla na taho mata tuna abin da ya faru. Murmushi Lulu ta yi ita ma tana rungume Didin da har lokacin jikinta be dena rawa ba. Ranar dai haka ta kwana duk a kunyace. Ba kuma ta fita ko nan da can ba saboda kar ta haɗu da Mommah. Har washegari kaasa fita ta yi gaida Mommah, dan gani take kamar tana zuwa Mommahn za ta fahimci abin da ya faru. Hakan ne ya sanyata cigaba da zama cikin ɗakin. Ita ma kuma Mommah ba ta takura ba, har cikin ɗakin ta saka aka kai musu hamshaƙin breakfast nasu.

... Kallanta Didi ta cigaba da yi cike da mamaki da kuma tausayin yanda take ajje numfashi kamar wadda ta yi tsere.

"Mene ne?" Ta sake tambaya a karo na barkatai. Lulu ba ta iya amsawa ba, se tashi da ta yi da gudu ta faɗa toilet ta shiga kwara amai. Da ma tun da ta ji ƙamshin abincin be mata ba. Dan dai Didi ta dage se ta ci ne, shi ne dalilin da ya sanyata ci. Se ga shi yanzu gaba ɗaya ya dawo duk da da ma kaɗan ne ta ci.

"Sannu.." Shi ne abin da Didi ke ta sauke mata kamar ba ta gajiya. Tausayin er uwar tata na sake rufeta. Ita da ma idan ta fara rashin lafiya ba sarki sai Allah. Daidai lokacin Mommah ta shigo cikin ɗakin. Ta kalli Didi da ke sake jerawa Lulu sannu kamar ba gobe. Tana kuma yi amfani da towel ɗin hannunta wajen saka mata wajen wuyanta.

"Subhanallahi me ya faru ne?" Mommah ta faɗa tana kallansu su duka. Sam mantawa ma ta yi da abin da ya faru jiya saboda halin da er uwatta ke ciki tace da muryarta da tafi kama da ta masu shirin yin kuka.

"Lulu ce ba ta da lafiya Mommah.. Yanzu ma Amai ta gama."

"Ya salaam.." Mommah ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin. Hakan ne ya sanya Didi neman waje ta zauna a gefen Lulu.

"Da ma tuntuni ki na aman ne?" Ta tambaya tana kallan Lulu. Se ta girgiza kai tana jin wata kasala na rufeta.

"Ni dai tun da muka zo gidan nan ban ga ta yi ba. Tana dai cewa tana jin tashin zuciya, ina ga ko zazzaɓi ne.." Didi ta faɗa tana kallan Lulu cike da tausayawa. Cigaba da kallanta Mommah ta yi na en wasu sakanni kafin ta miƙe.

"Maza ki shirya ku je asibiti.. Abun ya yi yawa." Jinjina kai Lulu ta yi a sanyaye ta amsa da

"Toh." Kai tsaye Mommah Gwani ta kira ta sanar da shi abin da ke faruwa. Babu jimawa ya zo cikin palourn. Zuwa lokacin Lulun ma ta shirya. Kai tsaye suka hau mota driver ya ɗauke su zuwa asibitin da en gidan ke zuwa.

Cikin sa'a lokacin da suka je asibitin ba su tarar da layi ba. Dan haka kai tsaye wajen ganin likita suka shiga. Se aka yi sa'a suka sami mace. Cikin ƙanƙanin lokaci Lulu ta mata bayanin abin da ke faruwa. Abu na farko da likitar ta soma faɗa shi ne gwajin ciki Lulun za ta yi. Daga ita har shi kallan juna suka yi kamar waɗanda suka ji an yi saɓo. Lulu ce ta soma janye idanunta lokacin da ilahirin jikinta ya ɗauki rawa. Ya yin da Gwani ya lumshe idanunsa yana fatan tabbatuwar hakan. Ya san ko babu komai idan cikin ne ze taimaka masa ainun wajen shawo kan matsalarsu da Lulu. Gefe guda kuma idan haka ɗin ne dab yake da zama uba kenan? Ya sake lumshe idanunsa, ji yake yi kamar ma an riga an tabbatar da haka ɗin ne.
Chapter 92 · 0% Book details