Sashe 90
A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Toh idan aka siyo miki za ki ci?" Ba dan tana da tabbacin hakan ba, se dan yanda ta ga Mommahn ta damu ne ya sanyata faɗin
"Eh."
"Toh ku fito palour yanzun nan. Ai ba a zauna haka da yunwa ba.. Ku je ko ma me kike so a nemo yanzun nan ki zo ki ci." Ta yi maganar tana ficewa daga ɗakin.
Neman waje suka yi suka zauna bayan sun fito daga ɗakin. Ba su daɗe da zama ba se ga sallamarsu Gwani cikin ɗakin. Se dai saɓanin kwana biyu da Gwani kan yi shiga irinta Bad Man yau ya fito a Gwaninsa sakk, ya yi shigarsa irin wadda ya saba, ya yi kyau abinsa. Ba su san yanda aka yi tun shigowarsu kowanne ya fahimci ga matarsa nan ba. Duk da ba gaba ɗaya fuskokinsu ne ke a waje ba. Amma kallan farko kowanne ya gano matarsa.
"Affan, ka ɗauki Afaaf ka je ka yi maza ka nemo mata abin da za ta iya ci. Ta kaasa cin wannan ɗin, kuma yunwa take ji." Mommah ta faɗa tana kallan Gwani.
"Tohm.." Ya ƙarasa faɗa yana satar kallan Lulu da ke zaune kamar mara lafiya, ta yi zuru zuru da ita. "Me ke damunta?" Ya tambayi kansa duk da ya san babu me ba shi amsa. Ɗan sosa kai Bad Man ya yi yana fakar idon Mommah ya kalli Didi, duk da yanda yake ƙoƙarin kama kansa ya ƙi kallanta ko kuma ya ƙi furta abin da yake son furtawa ya kasa daurewa. Ya kalli Mommah yace
"Amm Mommah bari mu je tare.. Idan tana buƙatar wani abun se ta ɗauka ita ma."
"Wace..?" Mommah ta faɗa tana kafe shi da ido duk da ta fahimci wadda yake nufi. Se ya basar yana ɗauke idanunsa. Runtse idanunta Didi ta yi kamar me bacci, daidai lokacin da yake faɗin
"Mommah.."
"Uhmm.." Tana girgiza kai. Da so samu ne, da kuma su kaɗai ne a wajen cewa za ta yi ashe ya san matarsa ce da ma yake ta yanƙwanasu tuntuni? Se dai ba ta faɗa ɗin ba. Ta kalli Didi tace
"Afrah ta shi ku je.. Idan kun dawo se ki yi baccin." Ji ta yi kamar tace ita babu abin da take buƙata, se dai ta yi shiru kawai ta miƙe.
"Ban ce ku daɗe ba.. Siyowa kawai za ku yi ku dawo sa ci a gida."
"Toh Mommah.." Daga haka duk suka fice daga ɗakin. Lulu ce ta soma fara hawa gidan baya ta shiga, Didi na shirin ƙarasowa ta shiga Gwani ya yi fuska ya shige bayan. Yi ta yi kamar ba ta gan shi ba, se dai ta so Didinta ce ta zauna a gidan bayan ba shi ba. Kamar ta fasa ihu haka ta ji, se ta ƙarasa kawai ta tsaya a wajen me zaman banza da ta san nan suke nufi ta zauna. Ba ta yi kankanbar buɗewa ba, dan ba ta sani ba ko har yanzu akwai ragowar halinsan nan. Ya kalleta ta cikin glass. Ya girgiza kai yana miƙa hannunsa ya buɗe ƙofar. Se kuma ya maida dubansa kan shirin tada motar da yake yi. Se a lokacin sannan ta shiga, ta saka hannu ta rufe murfin motar. Tun da suka fara tafiya babu wanda yace komai. Ba su yi wani nisa ba ya sanya hannunsa ya kunna waƙa, da yake volume ɗin a kusan ƙarshe yake se ya kasance waƙar ta soma tashi da ƙarfi ne. Soma bin waƙar ya yi a nutse kuma a hankali yana cigaba da driving. Ita dai Didi ta kame waje ɗaya dan gudun ma kar ta yi laifi. Duk da driving yake, gefe guda kuma yana bin waƙar hakan be hana shi yin amfani da damar da ya samu ba wajen satar kallan Didin ba. A karo na biyu Gwani ya kalli Bad yana jira ya ji tsawon wane lokaci ze ɗauka yana saurarar waƙar, se ya ga abun na shi ba na ƙare ba ne. Hakan ne ya sanya shi faɗin
"Ka ɗan cire mana wannan waƙar."
"Me ka ce?" Ya faɗa da ɗan ɗaga murya saboda waƙar da ta cika motar. Sake maimaita abin da ya faɗa Gwani ya yi. Bad Man ji ya yi kamar ya share shi, se kuma ya kasa. Cikin sa'a ma kuma lokacin inda yake so a waƙar ya ƙare, dan haka se ya kasheta ma gaba ɗaya ya cigaba da driving. A haka har suka ƙarasa wajen.
.. "Ki fito mu je se ki zaɓi abin da ya miki.." Girgiza kai ta yi dan haka kawai ta ji ba ta sha'awar komai na wajen. Ji take kamar ta fasa ihu, ita har ga Allah abun ya fara damunta. Me ke damunta ne haka? Allah ma ya gani abincin gidan Ummeey take son ci.
"Lulu me za ki ci ne?" Didi ta faɗa tana kallanta. Muryarta a sanyaye tace
"A siyo ko me ye."
"Kin tabbatar za ki ci?" Didi ta sake tambaya dan tabbatarwa. Se ta jinjina kai ba tare da tace komai ba. Komawa Gwani ya yi cikin wajen, ya duba wainar shinkafa ya siyo mata. Shi dai Bad Man kawai rakiya ya yi, be kuma tambayi Didi ita me take so ba kawai suka fito daga wajen. Motar ya tasa suka bar wajen. Kai tsaye gida ya nufa. Tun da ta ga inda suka nufa se ta ji gaba ɗaya zuciyarta ta karye. Tun tana tunanin daurewa se ta kasa, ba ta san lokacin da hawaye suka soma zubowa a kan kuncinta ba. Kamar an ce ya kalleta, se kuwa idanunsa suka sauka a kan hawayen da ke saukowa daga idanunta zuwa kan fuskarta.
"Subhanallahi.. Me ya faru?" Ya yi maganar yana ɗan matsawa kusa da ita. Ba ta ce komai ba hawayen kuma ba su dena zuba ba. Ganin haka ne ya sanya shi ƙarasa matsawa, ya saka hannunsa ya kamo nata hannun cikin sanyin murya yace
"Me ya faru Uhmm?" Zame hannunta ta yi tana ƙoƙarin kwantar da kanta a kan ƙofar motar. Ya yi saurin riƙota ta dawo jikinsa. Ya riƙeta gamm yana jin hawayen na sauka a jikinsa.
"Faɗa min me ya faru?" Ya faɗa yana ɗora kansa a kan fuskarta da ke jikinsa. Sam ya ma manta ba su kaɗai ne a motar ba. Dan kukan da ta soma tuni ya ruɗa shi.
"Ni abincin gidan Ummeey nake so." Ta faɗa kamar a shagwaɓe, se dai ba ta san a hakan ta yi maganar ba. Ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗe. A ransa yana mamakin wannan soyayyar da ke tsakaninta da girkin Ummeey. Jin ya yi shiru ne ya sanyata ƙoƙarin tashi. Ya sake riƙota cikin rarrashi yace
"Shi kenan.. bari mu wuce gidan." Daga haka ya ɗaga kai ya kalli Bad Man. Se a lokacin ya tuna inda suke, ba dan son ransa ba ya saketa sannan yace yana kallansa
"Ɗan uwa taimaka ka juya da mu zuwa gidanmu." Cike da mamaki Bad yace
"Wanne?"
"Gidanmu.. gidan Abeey.." Ya faɗa yanda ya san ze fahimta. Cike da mamakin dai ya sake furta
"Me ze kai mu gidan kuma a yanzu?" Ya yi maganar saboda dab suke da isa gida.
"Ba za ka taimaka ba..?" Gwani ya faɗa bayan ya kalli Lulu da ta yi shiru kamar marainiya. Se raba ido take yi kamar mara gaskiya. Be sake cewa komai ba Bad ya juya da motar zuwa gidan Ummeeyn. Se a lokacin ta sauke ajiyar zuciya, har ba ta san lokacin da murmushi ya ƙwace mata ba. Gwani ya yi murmushi yana jin daɗin murmushin da ya gani a kan fuskarta.
.. "Ba za ka shiga ba?" Gwani ya tambaya yana kallan Bad Man.
"Sorry bro.. Bari na jiraku kawai.." Ya yi maganar yana ɗan kallan Didi. Hannu ta saka ta ɓalle murfin motar ta fice, ya bita da kallo kamar wani dolo.
"Ahh.." Ya faɗa yana cigaba da binta da kallo. Ya zauna ne fa saboda ya ɗauka ita ma zama za ta yi, se ga shi ta fice ta bar shi. Toh me ze zauna yi kam. Se kawai ya fito shi ma daga cikin motar yana faɗin
"Mu je.." Tare suka shiga gidan. Se dai su Lulu na gaba ya yin da su suke baya. Sosai Ummeey ta ji daɗin zuwansu, nan take ta shiga nan nan da su. Ta ajje musu abinci da ruwa sannan ta dawo ta zauna suka sake gaisawa. Da ma har ga Allah ita dai Lulu abin da take jira kenan, dan haka babu ɓata lokaci ta zuba abincin da tun shaƙar ƙamshinsa na farko ta ji ya mata, aikuwa ta shiga cin abinta hankali kwance. Kallanta Didi da Gwani kawai suke yi cike da mamaki. Ita dai haka ta ci abincinta ta yi nakk sannan ta sha ruwa.
"Kin ƙoshi ɗiyata?" Ummeeey ta faɗa tana kallan Lulun. Se ta jinjina kai tana murmushi tace
"Eh Ummeey.." Cigaba da zama suka yi na en mintuna kafin suka yi sallama suka fice daga gidan suka bar Gwani da Ummeeyn.
"Bari na ɗauki wannan Ummeey ko za ta nema zuwa an jima.. Wai ta kasa cin na can gidan ne, na nan ɗin take so." Shiru Ummeey ta yi tana nazarin maganar Gwanin. Se dai tace
"Bari na tashi na zuba mata cikin flask ɗin can.. Idan ma tana buƙata ne ko zuwa gobe ma ka zo se ka tafar mata da shi." Ummeeey ta faɗa tana miƙewa. A cikin ranta tana fatan a ce abin da ya fara zuwar mata cikin rai shi ne. Bayan shuɗewar wasu mintuna se ga shi ya fito hannunsa ɗauke da leda. Daga haka Bad Man ya ja motar suka wuce gida.