← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 122

Sashe 21

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Plss!!" Ya faɗa yana ɗaga hannunsa idanunsa a ƙanƙance. Be kuma ƙarasa faɗar abin da ya yi niyya ba ya fice daga ɗakin. Binsa da kallo Mommah ta yi tana sauke ajiyar zuciya. Ba ta yi tunanin hakan daga gare shi ba sam. Haƙiƙa ta san tana ƙaunar yaron, amma kuma tunda har ya yi mata warning kamar ya manta ita ɗin wace ce, ta san idan har ta cigaba da abin da ta ƙudurta zumuncinsu ka iya lalacewa a yanda ta ga Areef ɗin, tunda har ya iya buɗe baki ya faɗa mata magana ba tare da jin komai ba. Se dai koma mene ne za ta yi ƙoƙari wajen ganin ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen saita wannan ma'auratan. Ta sake girgiza kai a karo na barkatai tana sake mamakin wannan bauɗaɗɗen hali na Areef ɗin. Idan banda abinsa ma ai yarinyar da aka aura masa ita ce abar tausayi, ita ya kamata a lallaɓa, a kuma tausayawa saboda auren Areef ɗin da ta yi, wanda ba shi da alƙibla ko kaɗan.

Tura ƙofar ɗakin ta yi a hankali ta shiga da sallama a bakinta. Didi dake zaune gefen gado ta amsa mata sallamar, tana faɗaɗa fuskarta da murmushi sanda ta fahimci wace ce.

"Sannu da zuwa.." Shi ne abin da Didi ta faɗa tana zamewa ƙasa daga kan gadon. Hannu Mommah ta saka ta kamota tana faɗin

"Yawwah daughter.." Se da ta zaunar da ita kan gadon sannan suka gaisa kafin Mommah tace

"Ya kuma haƙuri da zaman gidan nan?" Murmushin yaƙe Didi ta yi kawai ba tace komai ba. A kodayaushe hankalin Didi sake burge Mommah yake yi, komai nata yinsa take cikin sanyi.

"Ki cigaba da haƙuri kin ji? In Sha Allah komai ze wuce kamar be taɓa faruwa ba Uhmm?" Ta ƙare tana kallanta. Se ta jinjina kai sannan a hankali ta buɗe bakinta tace

"Tohm.."

"Yawwah.. Akwai wata matsalar ne kuma?" Mommah ta sake tambaya. Da sauri ta girgiza kai har cikin ranta tana jin daɗin kulawar mutanen nan biyu a cikin gidan nan. Har kuma yanzu ta kasa amincewa ba Mommah ce sirikarta ba.

"Tohm shi kenan bari na koma.." Mommah ta faɗa tana miƙewa. Ɗaga manyan kyawawan idanunta Didi ta yi tace a sanyaye

"Don Allah ina son in kira Ammina.." Murmushi Mommah ta yi ta koma ta zauna a kan gadon, ta miƙa mata tsadaddar wayar hannunta tace

"Saka number ki kira.. Idan kun gama ki ajje min Atine se ta taho min da ita.." Cikin jin daɗi Didi tace

"Toh na gode sosai.." Girgiza kai Mommah ta yi tace

"Babu wannan tsakaninmu.. Ki ɗauke ni a matsayin mahaifiyarki shi ne kawai.." Wani murmushin dai Didi ta sake yi daidai lokacin da Mommah tace

"Aff.. Idan an ɗan kwana biyu, wato abubuwa sun ɗan sake lafawa za ki soma shiga sashen Hajiya Salma kina gaidata." Haka kawai ta ji ƙirjinta ya buga, duk da ba ta san wace ce Hajiya Salman ba, amma se take ji kamar ita ce mahaifiyar mijin nata.

"Toh" kawai ta amsa da shi. Hakan ya bawa Mommah damar ficewa daga ɗakin dan bata waje ta samu ta yi wayar cikin nutsuwa.

Tun kafin wayar ta gama ringing take murmushi, burinta kawai ta ji Ammin ta ɗaga. Babu daɗewa kuwa Ammin ta ɗaga da sallama ɗauke a kan bakinta. Ai ko iya amsa sallamar Didi ba ta yi ba se miƙewa da ta yi tana jin wani irin sanyi na ratsata, ta buɗe bakinta da ƙyar tace

"Amminmu.."

"Didi.." Ammi ta faɗa ita ma cike da farin cikin jin muryar ɗiyar tata.

"Na'am Ammi ni ce.. Na yi kewarku sosai Ammi.. Ina jin gaba ɗaya babu daɗi Ammi.." Tsoro ne ya ziyarci Ammi jin abin da Didin ta faɗa, cikin sanyi tace

"Akwai matsala ne a nan gidan?" Ta san Ammin daga lokacin da ta ji akwai wani abun za ta tayar da hankalinta ne, hakan ne ya sanyata girgiza kai tace

"A'ah Ammi babu komai fa.."

"Kin tabbatar?" A hankali ta amsa da

"Ehh.." Se a lokacin Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta nemi waje ta zauna, suka sake gaisawa da Ammin sannan Didi tace

"Ammi ina ɗan uwa?" Murmushi Ammi ta yi tace

"Yana gidan Lulu.."

"Kai Ammi.. Ni fa?" Ta faɗa a shagwaɓe. Girgiza kai Ammi ta yi tace

"Ke baki san kin girma ba koh? Toh maza cigaba.. Za a kawo miki shi ki kwantar da hankalinki kin ji?" Turo baki ta yi sannan tace

"Toh.." Daga haka suka cigaba da hira, Ammi na yin amfani da wannan damar wajen yi wa ɗiyar tata faɗa sosai.

... Zaune yake a kan kujera hannunsa ɗauke da remote yana kamo wata channel. Sanye cikin wata shegiyar dakakkiyar shadda da ta matuƙar karɓar jikinsa. A cikin wayoyinsa dake zube a gefensa ɗaya ta shiga ruri, kamar ba ze kula ba, se da ya kamo channel ɗin sannan ya dubi wayar. Da mamaki yake bin number da kallo, a ransa yana tunanin ko lafiya? Kawai dai se ya ɗaga wayar, ya kara a kunnensa. Daga can ɓangaren cike da girmamawa aka gaishe shi. Ya amsa yana gyara zamansa, dan ya san tunda ya ga wannan kiran akwai wata a ƙasa.

"Yallaɓai ka yi haƙuri na kira ka ba tare da sanin dalilin kiran ba.."

"Babu damuwa.." Dad ya amsa da hakan. Ajiyar zuciya na can ɓangaren ya sauke kafin ya soma faɗin

"Rankayadaɗe idan babu damuwa ko da na minti biyar ne ka ba mu dama mu yi wata magana. Kwanaki wata magana na ta yawo, amma ni ban bi ta kanta ba saboda na ɗauka ko irin ana yaɗawa ne haka kawai. Se kuma daga baya na fahimci lallai mutanen da gaske suke yi, abin da ya sanya ni yin bincike kenan. Se dai ban samu wani ƙwaƙwƙwaran dalili da zan iya kare Areef Matawalle ba. Hakan ne ya sa na yi wannan gangancin. Na yi wannan kasadar, na yi wannan tsaurin idon na kira ka dan ka bayyanawa mutane gaskiyar al'amari a kan abin da ya faru.." Daga haka ya kora masa bayani a kan kai Bad Man da Didi asibiti da aka yi. Shiru Daddy ya yi na en wasu sakanni. Shi dama ya san za a zo wajen, ya riga ya fahimci hakan za ta faru saboda munafukai da suka musu yawa. Murmushi ya yi me sauti sannan ya soma faɗin

"Ba na buƙatar wata hira da zan wanke ɗana ko ni kaina. Dama wannan ɗin halayyar ɗan adam ce. Zargi! Saboda haka abin da kawai zance mutane su dena zargi a kan abin da basu da tabbaci a kai, dan kuwa ita wannan ɗin matar Areef Matawalle ce.." Shi kansa da ya ji abin da Daddy ya faɗa se da mamaki ya kusa kashe shi. Ashe dama Areef ɗin yana da aure amma babu wanda ya taɓa sani? Lallai kam wannan rahoto ne babba. Bayan sanin gaskiyar al'amarin da ya faru, ga kuma ƙarin wani information ɗin da suka samu. Ba ya so ya fusata Alhaji Matawallen da tambayoyinsa, hakan ne ya sanya shi faɗin

"Godiya nake rankayadaɗe.. Allah ya ƙara girma.." Daga haka Daddy ya katse wayarsa yana girgiza kai yana sake mamakin al'amarin mutanen duniya. Kallan da be yi ba kenan, se miƙewa kawai da ya yi ya bar ɗakin ma gaba ɗaya.

.. A ɓangaren su Lulu kuwa tun lokacin da ta baje a ƙasan nan tana cigaba da kukanta, ba ta yi tunanin kuma ze sake dawowa ma cikin ɗakin ba. Se dai bayan wajen minti 15 se ga shi ya shigo ɗakin hannunsa ɗauke da plate dake ɗauke da shinkafa da taliya da miya. Ƙarasawa ya yi ya zauna a gefen gadon yana kallan yanda har lokacin take a wajen, zuwa lokacin ta gama kukan se wasu uban ajiyar zuciya da take saukewa kamar za ta haɗiyi zuciya. Shiru ya yi na tsawon sakanni yana tunanin ta inda ze fara kuma. Dan har ga Allah ya gaji da jin wannan kukan, banda ciwon kai babu abin da yake saka masa. A hankali ya buɗe bakinsa yace

"Tashi ki ci abinci.." Idan gadon da yake kai ya kalle shi toh Lulu ta kalle shi. Ba ta ma nuna alamar ta san da wanzuwar wani a wajen ba, ballantana ta nuna ta ji abin da ya faɗa. A karo na biyu ya sake maimaita abin da ya faɗa ɗin. Nan ma dai shiru, izuwa lokacin ransa ya gama ɓaci, dan kuwa ya san rashin kirki ne kawai ya hanata amsawa. Ban da haka ya san tana jinsa. Ajiye plate ɗin ya yi, ya miƙe kyakkyawar fuskar nan tasa a haɗe kamar me shirin yin dambe, dan babu ƙarya zuwa yanzu ya gaji da wannan iskancin nata. Se ya shiga tattare hannun rigarsa dan ya ji daɗin yi mata ɗurar.

"Za ki ci ko na yi miki ɗura?" Ya sake faɗa yana kallanta. Nan ma dai ba ta amsa ba. Jin shiru be sake cewa komai ba ne, ya sanyata ɗan ɗaga idanunta a sace dan ganin abin da yake yi. Se ganinsa ta yi yana ƙoƙarin zuwa inda take. A miliyan ta zabura ta sake yin baya tana fashewa da sabon kuka da dashashshiyar muryarta.

"Wai ni ina ruwanka da ni? Ai dai cikina ne ba na wani ba.. ka rabu da ni mana na ce maka.." ta faɗa ɗin dai da dashashshiyar muryarta. Numfashi ya ɗan fitar daga cikin hancinsa sannan ya cigaba da takawa zuwa inda take.

"Ka dena taɓa ni ni ba er iska ba ce. Kar ka kuma taɓa ni wallahi.. Ni don Allah ka ƙyale ni ba na ci.." ta ƙarashe maganar a raunane. Dan izuwa yanzu a tsorace take da Gwanin matuƙa. Burinta kawai ta dena ganinsa a kusa da ita. Be san sanda wani murmushin gefen baki ya suɓuce masa a kan laɓɓansa ba. Ya kai hannunsa ya ɗan shafa sumar kansa dake a buɗe. Wato ita wannan taɓatan da ya yi duk shi ne ya tsoratar da ita. Ya sa ta yi laushi haka.

"Wallahi ko ki ci ko na saɓa miki.." ya yi maganar a kaurare kuma a ɗan zafafe bayan ya maida fuskarsa yanda take ɗazun.
Chapter 21 · 0% Book details