← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 122

Sashe 5

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba ni da wani zaɓi da nake son haɗa ki da shi bayan Malam Affan.. Saboda haka ki karɓe shi a matsayin miji.. Allah ya yi wa rayuwarku albarka, ya saka albarka a rayuwar aurenku, ya kaɗe duk wata fitina. Ya kuma saka muku da alkhairi bisa biyayyar da zaku yi na karɓar wannan auren, yasa nan gaba ku gane gata na muku.." Daga haka Abba ya miƙe ya bar ɗakin. Ammi ta bi shi da kallo cike da tausayinsu su duka. Sabon kukan da Lulu ta fashe da shi me ƙarfi shi ne ya dawo da Ammi ta juya ta kalleta. A wajen ta zube ta shiga dirzar kukanta cikin rashin sanin mafita. Kuka take kamar ranta ze fita, ji take inama Allah ya ɗauki ranta ta huta da wannan masifar. Ji take inama ba tazo duniyar ba ballantana har wannan abu ya faru. Me yasa Abba ze mata haka? Me yasa Abba ya shammaceta haka? Laifin me ta aikatawa Abban da ya hukuntata da wannan mummunan hukuncin?

"Allah ka kawo mana mafita cikin al'amarin nan.." Ammi ta faɗa sanda ta ɗora kanta a kan kujera har lokacin kukan Lulu na cigaba da tashi cikin ɗakin. Kallanta kawai Didi take yi, se dai itama duk yadda taso ta daure se ta kasa, se kawai ta shiga taya er uwar tata kukan se dai ita nata a hankali take yi dan har kanta ma yana cikin hijab ne. Da dai Ammi ta ji kukan Lulun bana ƙare bane, se ta shiga rarrashinta cike da tausayawa, tana bata baki, amma ina, kukan ta cigaba da yi kamar ma turata take yi. A wannan dare, idan nace wani daga cikin en gidan nan ya runtsa toh Little ne.

... Washegari tun da safe gidan ya fara karɓar baƙin kusa. Dan Abba yace baya son wani taro, waɗanda zasu ɗauki amare kawai ake buƙata. Tun safe Mami da Jadwa suka yiwa gidan dirar mikiya. Farin ciki a wajen Mami abin ba a cewa komai. Burinta na son haɗa Kaseem da Jadwa ta san ze cika, tunda ga shi cikin sauƙi yanzu babu shi babu Didi. Se da ta gaisa da waɗanda ke cikin parlourn sannan tace

"Ina 'ya'yana?"

"Suna ɗaki.." Ammi ta faɗa. Miƙewa Mamin har ma da Jadwa suka yi zuwa ɗakinsu Twins. Da sauri Mami ta ƙarasa zuwa kan gadon tana faɗin

"Daughter.." Shiru babu amsa, duk da kuma idanun Lulun a buɗe suke, se dai ta kafe waje ɗaya da idanun nata ne kamar me kallan wani abu.

"Daughterna.." ta sake faɗa sanda ta ƙarasa dab da ita. Ta saka hannu ta riƙota, motsi da jajayen luhu_luhu ɗin idanunta Lulu ta yi har lokacin ba tace komai ba. Tun jiyan bayan ta gama kukan ta godewa Allah se ya zamana kawai ta koma waje ɗaya ta yi shiru kamar me tunanin wani abu, ta riga ta fuskanci komai ya riga ya faru, aikin gama ya riga ya gama. Ta rasa mafita, ta rasa abin yi, ta rasa me bata shawarar abin da za ta yi, ta rasa me faɗa mata abin da ya dace ta aikata, se rarrashi kawai da sake bata baki a kan maganar auren. Gaba ɗaya kanta ya kwance, ji take kamar ba ita ba, jinta take kamar an sauyata, ta kasa magana, ta kasa cewa komai, ta kasa aikata komai, se tunani kawai. Har gwara Didi baiwar Allah da ta riga da ta fawwala Allah komai, ta yi addu'ar Allah yasa hakanne mafi alkhairi, ta kuma cigaba da janyo duk wata addu'a da tazo mata a zuciya. Daga baya ma se ta ɗauki Qur'an ta shiga karantawa ko zata samu zuciyarta ta yi sanyi. Cikin mintuna kaɗan kuwa ta soma ji komai na sauya mata, se kawai ta cigaba da yi cikin nutsuwa duk da yanda tunani ke son yi mata shamaki. Har Mami ta gama surutanta Lulu ba ta tanka mata ba, ba tace da ita ko uffan ba. Daga ƙarshe da ta gaji se kawai ta jata jikinta ta rungume tana rarrashinta. Se a lokacin hawayen da a yanzun ba sa mata wahala suka soma zubowa a kan fuskarta.

"Ki yi haƙuri kin ji daughter.. Kukan ya isa haka, kada ki yi wa kanki illa.." ta faɗa cikin rarrashi.

Tun safe dama Abba ya fice daga gidan shi da Little, ya kuma faɗawa Ammi ko da kai yaran aka tashi yi kada ta tsaya yi musu faɗa ko kuma nuna yanda za ta yi kewarsu saboda kada ta kuma kwaɓa al'amarin. Dan haka tun lokacin da Ammi ta fahimci lokaci na ta ƙaratowa, se ta shiga ɗakin nasu, cikin rarrashi ta samu ta soma yiwa Didi jagora zuwa toilet dan yin wanka. Zuwa lokacin zuciyar Didi ta gama karyewa, haka dai ta shiga wankan tana yi tana sharɓar kukanta. Se bayan ta fito ne sannan ta sake wani sabon lalen na saka Lulu shiga wanka.

"Don Allah Lulu, don Allah kar ki yi abin da be dace ba. Idanun kowa a kanmu suke, saboda haka ki yi ƙoƙarin ɓoye duk wasu halayenki ko da na yau ne a gama taron nan lafiya.. Kada ki bar mana abin faɗa.." Da wannan maganganun Ammi ta samu Lulun ta shiga wankan. Se da ta shafe fiye da 1hour sannan ta fito har lokacin hawayen fuskarta kamar ana kunnosu. Ammin da kanta ta shirya kowaccensu cikin riga da zani na atamfa sabuwa dall me kyau da tsada, ta feshe su da turare me ƙamshi sannan ta yane musu kansu da mayafi shi ma iri ɗaya. Rungumesu ta yi tana jin wata iriyar kewarsu na kamata, se dai ta yi ƙoƙari wajen saita kanta dan saboda kada ta sake karyar musu da gwuiwa. Se a lokacin kowaccensu ta fiddo da kukan nata fili, suka shiga yin kukansu cikin rashin sanin abin yi. Lulu kam kukanta cike yake da abubuwa da dama, ga an dakeka an hanaka kuka. Ta rasa abin da ya kamata ta yi, ji take inama ace wannan ɗin shirin film ne da ta ɗauki ƙafa ta gudu daga garin. Ji take inama zata iya kallan Abba da Ammin ta faɗa musu ko me zasu yi ba zata taɓa zama da Gwani ba. Se dai ta ma kasa buɗe baki tace wani abu, dan ta san kome zata faɗa ba ze chanja komai ba, kome za tace ba ze hana abin da su Ammi suka yi niyya ba. A yanzu dai ba zata iya hana kanta kuka ba, gwara ta yi iya yinta. Idan ya so bayan gama abin da suka so se ta yi tunanin abin da ya dace ta yi. Dan a yanzu dai kam kanta a kulle yake kamar da mukulli. Sanar da zuwan en ɗaukar amarya daga gidansu Gwani ne ya sanya Mami da wata cousin sister ɗin Ammi shiga ɗakin dan ɗakko amaren. Kafin ma su kai ga fitowa dasu se ga waɗanda Daddy ya aiko dan ɗaukar Didi. Waɗanda en uwansa ne kawai, dan kuwa har lokacin Mom ta ƙi yadda da batun auren, dama kuma jira kawai take yau ɗin ta yi, idan da gasken ne se ta san matakin da za ta ɗauka.

Cikin mota ɗaya aka ɗauki Lulu da Didi, yayar Mamansu Ammi ta shiga cikin motar, Mami ma haka. Se wata cousin ɗin Ammin itama ta shiga. Didi babu abin da take se kukan da yanzu sautinsa ya dena fita. Yayin da Lulu gaba ɗaya ma ta dena kukan, ta yi shiru ne kawai tana samawa kanta mafita, tunda dai ta fahimci dole auren an ɗaura, kuma gidan Gwanin ake ƙoƙarin kaita. Kukan nata ba shi da wani amfani, face zurfafa tunani da samarwa kanta mafita cikin kwanciyar hankali. Motar en uwan Bad Man na baya kasancewar Lulu za a fara kaiwa ya sanya motar en uwansu Gwani na gaba. A haka suka fice daga cikin gidan, duk iya ƙoƙarin Ammi ta kasa riƙe kanta se da ta yi kuka saboda kewar 'ya'yan nata da ta soma ji tun yanzun. Tafiyar mintuna marasa yawa aka yi, motar en uwan Gwani ta fara sauka daga kan titi. Duka suka bi bayanta, tunda babu wanda ya san gidan. Cikin wani ƙaramin layi suka shiga, suka soma tafiya a ciki, tafiyar sakanni kaɗan se motar ta dakata a ƙofar gidansu Gwani. Mami ta ɗauka kawai sun yi shortcut ne, se kuma ta ga sun tsaya, kamar basu da niyyar fita daga cikin layin.

"Wai me ye haka ne? Me ya tsayar damu anan ɗin ? Dama tun farko ma me ya biyo damu ta wannan n ƙaramin layin, kamar ma fa ba ya ɓillewa.." Mami ta faɗa tana leƙa waje. Ganin dai babu me bata amsa ya sanyata kallan driver tace

"Fita ka tambayi dalilinsu na tsayawa. Wannan ai ba yi bane.." Babu musu ya fita daga cikin motar zuwa inda motar da en uwan Gwani suke. Wajen second 30 se ga shi ya dawo ya buɗe motar yace yana kallan Mami

"Wai anzo gidan.."

"What..?" Mami ta faɗa tana buɗe idanunta kuma cikin ɗaga murya. Se ya jinjina kai yace

"Haka suka ce.." Da sauri Mami ta saka hannu ta buɗe side ɗin da take ta fita jikinta har wani rawa yake yi. Idanunta kamar zasu faɗo take bin gidajen layin da kallo. Duka ƙananun gidaje ne, babu wani gida da za a iya kallansa a kira shi da fitacce, kowanne yafi kama da na yaku bayi a idanun Mamin.

"Ina ne gidan..?" Ta tambaya kamar a ɗan tsorace. Nuna gidan da suka nuna masa ya yi lokaci ɗaya yana faɗin

"Gashi nan.." Da wani wulaƙantaccen kallo ta bi gidan da shi, tun daga sama har ƙasa, se kuma ta koma daga ƙasa zuwa sama kamar wadda ta ga bushashshen tutu.

"Ƙarya ne wallahi.. Wannan akurkin ne gidan amarya? Amaryar ma kuma Lulu? Ka san me kake faɗa kuwa? Ko kana hauka ne?.." Mami ta faɗa a fusace kuma zafafe kamar za ta kaiwa duk drivern duka..

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO26*

___"Haka dai suka ce.." ya faɗa cikin girmamawa. A zafafe Mami ta yi gaba zuwa inda en uwansu Gwani suka fara fitowa daga cikin motar.
Chapter 5 · 0% Book details