← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 122

Sashe 77

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Da ma a kan maganar Areef ne na zo in ji ko ka yanke shawarar barinsa ya fita ƙasar wajen. Ka ga dai haka na so ya fita tun a secondary amma ba ka amince ba. Toh a wannan karon ina roƙonka da Allah da ka amince ya fita.." Ajiyar zuciya Daddy ya sauke, shi kam sam ya rasa dalilin Mom ɗin na dagewa a kan fitar Areef ɗin waje karatu. Ko da yake ya san hakan na da nasaba da ganin da take 'ya'yan abokansa duk a wajen suke karatu.

"Shi kenan.. Amma ki sani duk wani tsari da na fito da shi za ki bi shi matuƙar ki na so na yadda Areef ya bar ƙasar nan."

"Babu damuwa.. Na amince ma." Ta faɗa tana murmushi cike da farin ciki da jin daɗi. Abu na farko da ya fara faɗo mata shi ne nisa da Areef ɗin ze yi da Mommah, ta san tabbas ze mantata kafin ya dawo. Abu na biyu kuma da ma burinta kenan kar ya yi karatu a ƙasar nan dan tana ganin a matsayinsa na ɗan gidan hamshaƙin me kuɗi kamar Alhaji Matawalle be dace a ce ya yi karatu a ƙasar nan ba. Haka dai bayan gama shirye shirye aka tura Areef U.S bayan dogon gargaɗin da Daddy ya gindaya masa. Be kuma bar shi ya tafi ba se da ya haɗa shi da waɗanda za su din ga kula da shi. A lokacin Mommah ji ta yi ina ma tana da ƙarfin faɗa a jin da za ta iya hana Areef tafiya ƙasar waje. Sanin da ta yi ba ta da shi ne ya sanyata kama bakinta. Ta bi shi da addu'a lokacin da ze tafi ɗin.

Duk da yanda Daddy ya tsaya tsayin daka wajen tarbiyyar Areef ɗin duk da ba ya ƙasar nan, amma hakan be yi wa Mom ba, ita se take gani ma kamar wannan ɗin ai takura ce. A bar yaro mana ya wataya ko dan kasancewarsa ɗan me kuɗi mana. Amma kullum yana tare da masu ba shi kariya da tsaro ai wannan ma takura ce da rashin yadda da shi. Shi kam Daddy ko a jikinsa, idan ma tana irin waɗannan maganganun ko kallanta ba ya yi. Dan kuwa be taɓa yadda da abin da take faɗa ba. Abin da ya sani kawai shi ne tun da Areef ɗin ya bar gabansu ya bar gabansu kenan, babu wani me kwaɓarsa a can ɗin. Dan haka tura masa masu kula da shi shi ne kaɗai mafita. Duk da ya san Allah ne kaɗai me karewa, amma ko babu komai hakan ze taimaka ainun.

_CIGABAN LABARI_

✨MHIZ INNOCENT✨
*AJTICHAPTERTWO66*

___ Shiru ɗakin ya ɗauka na fiye da tsawon minti 5, babu wanda yace komai tun bayan da Maimuna ta gama faɗar abin da suka aikata ita da Mom. Bad Man dake zaune a gefen side chair yanzun haka yana zaune ne a kanta gaba ɗaya, hannunsa na kan goshinsa idanunsa a lumshe, ba za ka iya fahimtar yanayin da yake ciki ba. Se dai za ka iya ganin yanda jijiyoyin kansa suka tashi, suka fito raɗa raɗa har a kan goshinsa. Zuciyarsa babu abin da take yi se wani irin harbawa da ya wuce na misali. Ya ma rasa abin da ya kamata ya yi. Tunanin me ze yi? Me ya kamata yace? Me ya kamata ya aikata? Gaba ɗaya kansa ya kulle, ƙwaƙwalwarsa ta toshe, ta yadda ya kasa ko da yunƙurin yin wani tunanin ne. Daddy kam hular da ke kansa ɗazun yanzun tana gefensa, kansa yana kallan ƙasa lokaci zuwa lokaci yana bubbuga ƙafarsa a ƙasa, se dai shi ma har zuwa shuɗewar waɗannan mintunan be ce komai ba. Ammi da Talatuwa da basu san da zaman labarin ba su kansu sun jijjiga bayan da suka ji abin da Maimunan da Mom suka aikata. Kuka kawai Talatuwa ta fashe da shi, dan ba ta taɓa tunanin rashin imanin Maimunan ya kai har ta yadda a haɗa baki da ita su aikata wannan mummunan aikin ba. Mom da tun ɗazu take yunƙurin magana Daddy na hanata, a karo na barkatai ta sake buɗe baki jikinta na wani mugun karkarwa, ba ma ta taɓa tunanin idan ta buɗe baki za ta iya magana ba. Se dai cikin ƙarfin hali ta buɗe bakin da ƙyar ta soma faɗin

"Wallahi ƙarya take yi, ƙarya take yi. Sharrin Sa'adatu ne kawai. Duk yadda aka yi nauyinta ta ɗauka dan ta zo ta ƙala min wannan sharrin. Da ma tun da na sallameta a aiki na lura ta ƙullace ni ashe abin da suka shirya kenan. Kar ka yadda da ita, kar ka yadda da ita.. ƙarya take min.." Ta ƙare muryarta na karkarwa. Se a lokacin sannan Daddy ya ɗaga idanunsa da shi kansa suka sauya kala ya sauke su a kan Mom, wata irin tsanarta na zuwa ta mamaye zuciyarsa. Haushi, takaici da kuma tsananin mamaki sun ƙi barinsa. A karo na farko tun bayan gama bayar da labarin da Maimuna ta yi yace

"Kin gama?" Ya faɗa muryarsa a wani irin kaurare. Se ta yi maza ta jijjjiga kai a tunaninta ko ya yadda da abin da ta faɗa ne, tace

"Ehh wallahi ƙarya take min.." Ta sake wallacewa ba tare da damuwa ba, a cewaeta ai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba. Se da Maimuna ta goge hawayen da ya ƙi tsayawa a kan fuskarta saboda danasani da nadama sannan tace

"Ina me rantsewa da girman Allah abin da na faɗa gaskiya ne. Ban ƙara ba kuma ban rage ba. Idan dai har ƙarya na yi mata Allah ya wulaƙanta ni tun kafin na bar gidan nan.. Za kuma ku iya zuwa ku yi gwaji dan tabbatar da abin da na faɗa.." Se a lokacin Mommah da tun da aka fara maganar ba ta iya ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ba ne. Illah kafe Maimuna da ta yi da ido tana jin abin da take faɗa ɗin kamar almara. Lokacin da ta kai ƙarshe kuwa tuni jikinta ya ɗauki rawa, har ta numfashinta se da ya soma yi mata barazanar ɗaukewa, dalili kenan da ya saka bugun zuciyarta ya ƙaru, ta shiga fuzgo shi da ƙyar idanunta a lumshe. Har lokacin babu abin da kunnuwanta ke jiye mata se maganar Maimunan. Kamar wadda kunnanta ya yi recording haka take ji. Cikin lokaci ƙanƙani ta ji wani jiri na ɗibarta duk da kasancewarta a zaune. Ba tare da ta shirya ba kuwa ta yi maza ta riƙe kanta da ya mugun sara mata, a take a gun kuma ta zube kan kujerar sumammiya.

"Sa'adah.." Daddy da ke lura da ita ya faɗa yana miƙewa da sauri. A karo na farko ya buɗe idanunsa da ƙyar kuma da sauri, sun yi wani irin ja kamar gauta. I zuwa lokacin ban da zafi babu abin da numfashinsa ke fitarwa. Be san lokacin da ya miƙe ba kai tsaye ya wuce kujerar da Mommah ke kai.

"Areef ɗorata kan waccan kujerar.." Daddy ya faɗa duk da yanda yake jin wani tsoro na kama shi. Se dai ta gefe ɗaya ya san dole ne Mommah ta shiga irin wannan yanayi, jin abin da ba ta taɓa tsammani ba. Shi kansa ya rasa a wanne yanayi ze saka wannan al'amari, ballantana kuma ita da ta haifa. Babu musu Bad Man ya saka hannunsa ya ɗauki Mommahn ya soma takawa dan kwantar da ita kan wata kujera da ke cikin palourn wadda ta yi shigen kama da gado, se dai ita ma irin yadin kujerun gareta.

"Ka sauketa Areef.. Ka da ka yadda da abin da suke faɗa.. Sharri ne.." Mom ta yi ƙarfin halin faɗin hakan, dan kuwa a lokacin ita kaɗai ta san tsoron da take ji. Kawai dai tana yin magana ne dan kar zargin ya yi yawa. Wani kallo da ya watsa mata da gigitattun idanunsa shi ne ya sanyata saurin sauke kanta ƙasa hantar cikinta na kaɗawa. Kaddai har ya amince da abin da aka faɗa? Yau kam ta shiga uku idan haka ɗin ne.

Kai tsaye kwantar da ita ya yi a nutse. Be jira Daddy ya ce komai ba ya ɗauko ruwa da kansa ya ƙaraso ya shiga shafawa Mommahn a fuskarta. Cikin ƙanƙanin lokaci ta ja wani gauron numfashi kafin ta sauke ajiyar zuciya, se ta shiga buɗe idanunta kamar me neman wani abu. Ba ta jira komai ba ta miƙe zaune da kanta a kan kujerar. Hawaye ne suka shiga zubowa a kan fuskar Mommahn, ranta babu daɗi sam, ta rasa me ya kamata ta yi. Cikin kulawa Daddy ya kamo hannunta idanunsa a kan fuskarta yace

"Ki na lafiya?" Jinjina kai ta yi daidai lokacin da wasu hawayen suka zubo a kan kuncinta. Da ƙyar ta buɗe baki tace

"Da gaske en biyu na haifa? Da gaske Areef ɗana ne? Da gaske ne Yallaɓai?" Mommah ta yi maganar gwanin ban tausayi. Rufe idanunsa Daddy ya yi yana jin wani mugun tausayin Mommahn na ratsa shi. Kaff cikin ɗakin cike da tausayawa suke kallan Mommah, idan ka cire Mom da Aunt Makiyy da suke tsoron kar asirinsu ya tonu. Juyawa Daddy ya yi ya kalli Mom da har lokacin su take kalla, ban da gumi babu abin da ke tsatstsafowa daga jikinta.

"Za ki buɗe baki ki faɗi gaskiya ko kuma se na yi miki abin da har ki mutu ba za ki manta da shi ba?" Ya yi maganar a kaurare yana kafeta da idanunsa. Shiru Mom ta yi a ranta tana ji kamar ta buɗe baki ta sake maimaita ƙarya Maimunan take yi. Se dai gefe guda kuma tana tsoro kar ya gano ƙarya take ya yi mata abin da yake iqrari, dan ta san tabbas ba ze wuce saki yake nufi ba. Kai amma duk da haka ba za ta bari asirinta ya tonu ba, dan haka ta buɗe baki da niyyar sake ƙaryata Maimuna a karo na barkatai se jin muryar Aunt Makiyy dake gefenta ta yi tace
Chapter 77 · 0% Book details