Sashe 121
A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kamar.." Kafin ta sake cewa komai wayarsa ta ƙara yin ƙara. Ya kalla ya ga Areef ɗin ne dai. Ya miƙe yana faɗin
"Bari ki ga na je, idan ba haka ba mutumin nan ba ze ƙyale ni ba.." Ƙarasawa ya yi ya ba ta side hug a nutse saboda sanin yanayinta a halin yanzu. Ya ƙarasa ya buɗe inda yaran ke ciki, a hankali ya sumbaci goshin kowannensu kana ya ɗaga kai ya sake kallan Lulu. Suka sakarwa junansu sanyayyen murmushi kafin ya miƙe ya fice daga cikin ɗakin.
Suna haɗa ido Gwani ya watsa masa wani kallo. Ya ɗauke kai yana murmushi, oho dai shi ko a jikinsa. Tun da dai ya rabo shi da matarsa kamar yadda shi ma ya haƙura ai shi kenan. Haka yana ji yana gani ya baro jariran nan, dan haka shi ma kawai ya haƙura haka nan. Haka duk suka tafi gida jiki a sanyaye, kowanne na tunanin kwana 40 ɗin da ze yi ba tare da matarsa ba.
Sosai masu jegon ke samun kulawa ta ɓangare da dama. Bayan ɓangaren Ammi da kullum ke tare da su, Ummeey kanta ba a barta a baya ba, haka Mommah ma da Yaya Amina. In taƙaice muku labari dai har da Mami (Mamin Jadwa) wadda yanzu ta yi laushi sosai, kai ba zaka ce ita ba ce. Kafin kuma Abba ya yadda ta cigaba da mu'amalantar iyalinsa se da ya tabbatar da gasken ta gyaru kamar yadda ta faɗa masa. Se dai ita kanta Lulu da a da suke ɗasawa, se ya zamana ma yanzu sun fi zama tamkar baƙi idan suka haɗu. Dan yanzu ta kama kanta, tun da ta gane Mamin ba ƙaunarta take ba. Ta ɓangaren Masoyiya kanta ta taka rawar gani, babbar ƙawa ta haihu. Haka ta din ga zuwa gidan tun washegarin ranar da aka yi haihuwar. Duk lokacin da ta zo kuwa haka za ta wuni yaron nan a hannunta suna hira da Lulu da jiki ya yi kyau sosai Alhamdulillah.
Ranar suna ta zagayo dukka jariran suka ci suna ABUBAKAR, ɗan gidan Didi da Areef sunan Daddy ya ci. Ya yin da ɗan gidan Lulu da Gwani ya ci sunan Abeey har ma da Daddyn. Duk da ba taron suna aka yi ba, amma en uwa da abokanan arziƙi nata zuwa ganin jarirai. Tun daga kan en uwansu Ammi, na su Abba har zuwa kan na su Mommah da Daddy. Haka zalika ma daga ɓangarensu Abeey da Ummeey gaba ɗaya en uwansu se zuwa suke yi barka. Abokan Daddy kansu se da suka je suka ga jikokin nasu. Kowa kuma da kalar abin da yake kaiwa. Daddy kam kowanne jariri manyan akwati ya cika masa shaƙe da kaya masu tsada, da shegen kyau. Ita kanta Mommah ba a barta a baya ba wajen gwangwaje jikokin nata. Abeey da Ummeey na kansu sun taka muhimmiyar rawa a kan yaran, dan yanzu komai se dai su ce Alhamdulillah, dan Ummeey yanzu haka sana'a take yi. Abeey kuma tuni shagon da Daddy ya buɗe masa yake cigaba da albarka, kullum cigaba ake samu. Don haka su ma kansu se da suka gwangwaje jikokin nasu da kaya masu kyau. Se da suka yi kwanaki 40 ɗin kuwa ciff kafin kowacce ta koma gidanta. Zuwa lokacin sun sake yin kyau, sun sake murjewa. ARYAAN da AYAAN kyawunsu ya ƙara fitowa sosai. Sun yi ɓulɓul abinsu. Zuwa lokacin ma hatta girman Ayaan (Ɗan Didi) ya yi daidai da na Aryan (Ɗan Lulu). Idan ma ba ka sani ba ba za ka ce be kai watannin haihuwarsa aka haife shi ba. Ranar da suka koma ɗin se ta zamana wata rana ta musamman a wajensu gaba ɗaya.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, cikin farin ciki da ƙaunar junansu. Cikin ikon Allah kullum cigaba ake samu a rayuwarsu. Aryan da Ayaan na ta ƙara girma da wayo. Suna kuma ƙara girma kyawunsu na ƙara fitowa. Kamanninsu da iyayensu kuma na ƙara bayyana. Zuwa lokacin Didi da Lulu sun koma makaranta. Suka soma karatunsu cike da ɗumbin nasara, musamman da abun ya zo da duk mazajen nasu sun ba su goyon baya ɗari bisa ɗari. Ta ɓangaren Aryan da Ayaan kuwa kullum shaƙuwarsu ƙaruwa take, sun zama tamkar en biyu musamman da ya kasance suna kama. Komai nasu iri ɗaya ne, komai za su yi tare suke yi. Ba a bambanta musu komai, dan kuwa a cikin iyayen ko me ɗaya ya tashi siya ba ya taɓa siyar ɗaya se dai biyu. Yadda suke ƙaunar junansu ya sa masu musu kallan en biyu kullum ƙaruwa suke yi. Tsayinsu ɗaya, haka zalika girmansu ɗaya. Hatta da halayensu kaɗan ne suka bambanta.
_BAYAN WASU SHEKARU_
.. A cikin shekarun abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa hadda auren da Kaseem ya yi. Wanda ya auri Masoyiya (Fatima Kabeer), bayan haɗuwar da suka yi ya je wajen Areef, ita kuma ta je wajen Lulu, ta zo tafiya ta biya ta yi wa Didi sallama a nan suka haɗu. Daga nan dai soyayya ta ƙullu har ta kai ga aure. Jadwa ma ta yi aure, se dai duk burinsu na auran me kuɗin be cika ba, ta dai samu wani me rufin asiri ta aura. Ita ma kuma dama Mami burinta ya yo ƙasa tuntubi. Ladi (Jakadiya) ta rasu a cikin shekarun bayan wani hatsari da suka yi a kan hanyarsu ta zuwa Kaduna. Hatsarin ne Abban ya yi sanadiyyar rasuwar mutane har 5, ciki kuma har da Ladi. Ɓangaren Lulu da Didi kuwa karatunsu ya yi nisa sosai. A ɓangaren zamantakewarsu kuwa kullum shaƙuwa, zaman lafiya da ƙaunar juna ke ƙaruwa a tsakaninsu.
.. Wasu kyawawan yara na hango sanye cikin Uniform iri ɗaya, takalmi iri ɗaya maƙale da jaka a bayansu kala ɗaya, haka basket ɗin ma da ke a hannun kowannensu iri ɗaya ne. Farare tass kyawawa kamar yaran larabawa.
"Laa!! Aryan Abbu yace za mu je gidan Granny yau.." Ɗaya daga cikin yaran ya faɗa yana kallan ɗan uwan nasa. Buɗe idanunsa Aryan ya yi kamar wani babba. Yace bayan ya ajje basket ɗin hannunsa.
"Toh mu zaɓi wace za ta shirya mu." Shiru duk suka yi. Dukkansu suka ɗaga kai suna kallan sama kamar masu nazari. Shi Aryan hadda ɗaga kai hannunsa na kan kumatunsa yana faɗin
"Uhmmm!!" Irin ya zurfafa tunanin nan. Can Ayaan yace
"Ko a yi er rige-rige."
"Ehh kuwa." Aryan ya faɗa yana jinjina kai fuskarsa ɗauke da murmushi. Se da ya ɗauki basket ɗinsa sannan yace
"Kuma se na riga ka.." Yana gama faɗa ya yi sashensu a guje. Da gudu shi ma Ayaan ya tafi yana faɗin
"Na rantse se na riga ka." Ya faɗa shi ma yana wucewa sashensu.
Tun kafin ya ida shiga cikin ɗakin ya soma jefar da basket da jakar bayansa. Da ƙarfi yake kiran
"Maami.. Maami.."
"Toh Babana ya dawo kenan.." Gwani da ke zaune cikin ƙananan kaya ya faɗa yana kallan Lulu. Ya yi matuƙar kyau, ya sake zama babban mutum. Kwanciyar hankali kuwa da kanta ta ke bayyana kanta a jikinsa. Lulun na tsaye bakin mirror tana buɗe drawer jikinsa alamar abu take nema. Gwani na kai ƙarshen maganarsa Aryan ya shigo ɗakin a guje.
"Mami ki sauri ki shirya ni, Mami ki shirya ni kin ji?" Abin da yake faɗa kenan har wani numfashi yake saukewa. Da sauri ta rufe drawer tana juyowa. Cikin sauri ya ƙaraso ya rungumeta yana faɗin
"Mamina.."
"Na'am yaron Maminsa." Ta faɗa tana rungume shi gam.
"Mami ki shirya ni." Ya sake faɗa.
"A'ah, wai ina za ka je ne?" Lulu ta faɗa tana kallansa. Turo ƙaramin bakinsa ya yi kafin yace
"Unguwar da Abbu yace za mu je." Ya ƙare a shagwaɓe
"Toh da alama dai ba ka ga Abbun ba koh?" Lulu ta faɗa tana kallansa kafin ta maida dubanta inda Gwani yake. Da gaske sam be lura da shi ba sabosa hankalinsa gaba ɗaya na kan ya zo Mami ta shirya shi kar Ayaan ya riga shi shiryawa. Se kuwa ya tafi a guje yana faɗin
"Abbu.."
"Na'am yarona.." Ya faɗa yana rungume shi fuskarsa ɗauke da murmushi.
"Abbu ai ka ce za mu je unguwa koh?" Ya faɗa yana kallan Gwani. Murmushi Gwani ya yi dan ya san da ma a wayon yaron nan ba ze manta da zancen unguwar nan ba.
"Ehh na ce.."
"Toh ka ce Mami ta shirya ni." Ya ƙare yana kallan Lulu. Miƙewa ta yi tana faɗin
"Se an jima toh.." Take fuskarsa ta sauya, kamar ze fashe da kuka yace
"Abbu Ayaan fa ze riga ni shiryawa."
"In ji wa?" In ji Gwani. Se da ya sake turo baki yana ƙiƙƙifta ido kafin yace
"Shi! Abbu ka ce Mami ta shirya ni."
"Ohh Ya Allah!" Gwani ya faɗa yana miƙewa. Ya san halin Aryan ɗin, idan dai har ba a yi hakan ba toh ba ze taɓa barinsu su samu sukuni ba. Hakan ne ya sanya shi faɗawa toilet ɗin da kansa ya cuɗe shi tass kafin suka fito. Kaya ya saka masa Lulu na zaune tana kallansu gwanin burgewa. Ana shirin yana ta hirarsa yana bawa baban labarin abubuwan da suka faru a makaranta, shi kam yana ta biye masa. Lulun ce ta ƙarasa shirya shi, se ga shi ya fito tass da shi ya yi matuƙar kyau.
"Toh a zauna a ci abinci." Lulu ta ƙare maganar tana murmushi. Girgiza kai ya yi kafin yace bayan ya maƙe kafaɗarsa
"Uhmm uhmm.." Harara Lulu ta jefa masa kafin tace
"Toh na ga inda za ka fita a haka." Ta ƙare maganar tana gyara zamanta. Take hawaye suka taru a idanun Aryan, ya koma wajen Gwani yace muryarsa kamar wanda ya gama yin kuka
"Abbu.." Abin da ya faɗa kenan. Gwani ya kalli Lulu da ta haɗe rai ita a lallai dole tana nufin abin da ta faɗa. Wato su ba sa gajiya kullum se sun yi faɗa.
"Kamar yadda Mami ta faɗa zauna ka ci abinci."
"Abbu zan ci a gidan Maama." Ya faɗa yana ɗaga kai ya kalli Gwani, haka nan kawai yake ji ya samu mafita. Ganin Gwanin ya girgiza kai ne ya sanya shi sake faɗin
"Allah da gaske Abbu."