← Book details A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 122

Sashe 70

A Jini Take Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka ga tun yanzu wai har yaron nan ya fara wahalar da ni." Ta faɗa tana sake riƙe ƙugu lokaci ɗaya tana satar kallan Mommah dan tabbatar da ta ji abin da ta faɗa, dan kuwa ta yi hakan ne dan Mommahn ta fahimci abin da take ɗauke da shi, ko za ta kama kanta, ta san ita ɗin ba sa'arta ba ce yanzu, ta fita ta kowanne ɓangare. Dan ta san ba lallai ne Daddy ya sanar da ita tana ɗauke da juna biyu ba. Kallanta Daddy ya yi jin ta ambaci jinsi a maganar tata tun yanzun. Se ya yi murmushi kawai yana faɗin

"Ya kamata ki dinga kula dai kam."

"Ai dole na ma.. Duk da dai ka san yanzu ba zan iya aiki ni ɗaya ba saboda yaron nan.. Dole se dai a samar min yarinyar da za ta dinga taya ni."

"Yallaɓai se ka shigo." Mommah ta faɗa tana murmushi dan sarai ta fahimci maganganun da Mom ɗin take tana sane take ta yinsu duk dan ta ɗarsawa Mommahn wani abun cikin zuciyarta.

"Olright.." Daddy ya faɗa. Wata banzar harara Mom ta bita da ita a kan laɓɓanta tana furta

"Se dai baƙin ciki ya kashe ki.. Haihuwa kuwa se dai ki ga ina ta yi In Allah Ya yarda."

"Magana kike ne?" Daddy ya tambaya yana kallanta. Se ta yi saurin girgiza kai tana faɗin

"A'ah.." Daga haka suka wuce.

Daga wannan rana Mom ta shiga zuba rashin kirki kala kala, taɓara kuwa ba a magana. Kuma ba ta tashi yi se ta gansu a gaban Mommah. Ita kuwa Mommah ba ta taɓa nuna ta ga wani abun. Rayuwarta take cigaba da yi babu takura, babu ɗorawa kai damuwa wai dan kishiyarta ta samu ciki ita ba ta samu ba. Musamman kuma a lokacin da dududu ba su wuce watanni ba. A cikin wannan tsukun ne wata mata me samarwa da gidajen masu kuɗi en aiki ta samowa Mom Maimunatu, wadda aiki ne ya kawota Kano. Ta fara aikin gidan wani me kuɗi ya nemi ya lalata mata rayuwa. Daga nan ba ta sake zama ba, ta gudu. Shi ne aka samarwa Mom ita. A lokacin tana budurwa, da ma kuma Mom ba son babbar mace take yi ba, dan kuwa so take ta mallaka mata komai na aiki da ke cikin gidan. Ita kuma ba za ta bawa wata babba ta mata girki ba. A karon farko da ta soma ganin Maimunatu ta kwanta mata a rai. Dan haka babu ɓata lokaci ta karɓeta. Daga wannan lokaci Maimuna ta fara aiki a cikin gidan. Mom na cigaba da lura da take_takenta. Komai sakar mata shi ta yi, kama daga girki ne, wanke_wanke ne, shara, gyaran ɗaki, kai ba na Mom kaɗai ba. Hatta na Daddy idan ranar girkinta ce ita take turawa ta je ta gyara. Se daga baya da Daddy ya lura da hakan ya taka mata birki, yace idan ba za ta gyara da kanta ba ya bari Mommah ta gyara. Haushi ya cikata, se dai ta san tun da Daddyn ya faɗi hakan yana nufin haka ɗin. Hakan ne ya sanyata haƙura ta dena saka Maimunan gyaran ɗakin. Idan ranarta ce haka take haƙura ta yi da kanta gudun fushin Daddyn.

Cikin ƙankanin lokaci Mom da Maimuna suka yi mugun sabo. Har ta kai ga Mom ɗin kan zama su yi wata maganar ta sirri da ita, idan ta gaza samun Aunt Makiyya da lokacin take en matanci. Wani abu da ya ƙara saka alaƙarsu ta yi ƙarko shi ne yanda Maimunan ta kasance guntsi fetsi ce, wato ma'ana dai er gurmi ce. Da gangan ta tsiri cusa kanta wajen Mommah ko dan ta samu wani abun ta je ta faɗawa Mom. Se dai da yake Mommahn akwai tsare gida, da kuma kama kai, ya sanya ba ta samu wannan damar ba. Daga ƙarshe ma se kama kanta ta yi ta dena zuwa sashen.

... A karo na barkatai ta sake danna number, yanzu kam babu wani tunani ta danna number ta kira. Ringing ɗaya biyu aka ɗaga. Daga can ɓangaren aka ce

"Sa'adah.."

"Na'am Yaya ina kwana?.." Mommah ta amsa tana ɗorawa da tambaya.

"Lafiya ƙalau nake.. Ke fa?"

"Ni ma haka." Mommah ta faɗa tana dakatawa. Shiru na tsawon sakanni ba ta sake cewa komai ba. So take ta san ta ina za ta fara yi wa yayar tata magana. Duk da kasancewarta Yayarta da suke uwa ɗaya uba ɗaya. Yayar da ta zame mata tamkar mahaifiya tun bayan mutuwar mahaifiyarsu.

"Me ya faru ne Sa'adah?" Yaya Amina ta tambaya jin Mommahn ta yi shiru. Se a lokacin sannan Mommah tace

"Kin ga Yaya da ma so nake na faɗa miki, yau kwana 4 kenan ina amai. Duk abin da na ci se ya dawo, ga kuma kasala ina fama da ita. Tashin zuciya kuma shi ke sa in kaasa cin abinci. Kuma.." Se kuma ta yi shiru. Murmushi Yaya ta yi har tana miƙewa daga zaunen da take tace

"Ina Abubakar ɗin?"

"Ba ya nan.. Kwanansa 3 ba ya ƙasar." Sauke ajiyar zuciya Yaya Amina ta yi kafin tace

"Zuwa yaushe ze dawo?"

"Sati 1 ze yi." Mommah ta bata amsa.

"Toh shi kenan.. yana dawowa ki sanar da shi abin da ke faruwa. Ko kuma ma dai ki kira shi kawai ki sanar da shi zan zo in ɗauke ki mu je asibiti a duba ki."

"Yaya.." Mommah ta faɗa.

"Ehh haka na ce." Yaya Amina ta katseta da faɗin hakan.

"Tohm." Ta amsa da hakan. Daga haka suka yi sallama.

A ranar kuwa Yaya Amina ta zo ta ɗauketa suka tafi asibiti, a ranta tana fatan Allah Ya sa abin da take tunani ne. Aikuwa cikin yardar Allah suna zuwa aka tabbatar musu da Mommahn na ɗauke da juna biyu. Farin ciki a wajen Yaya Amina abin ba a cewa komai. Ita kam Mommah lumshe idanunta ta yi tana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa. Se ta rasa da wanne baki za ta yi amfani wajen godewa Allah da wannan ni'ima da ya mata.

"Bari na zama ta farko wajen yi wa Abubakar albishir." Hannunta Mommah ta kai ta dafe na Yaya Amina jin abin da tace

"A'ah Yaya Amina ni kam kar ki faɗa masa don Allah." Dakatawa Yaya Amina ta yi tana kallanta cike da mamakin jin furucinta. Se ta jinjina kai tana ɗorawa da faɗin

"Ni ba na so Salma ta sani ne Yaya. Ba ki ga rashin kirkin fa da take min ba. Na san da wuya idan ya ji be sanar da ita ba. Ni kuma na fi so kawai ta gan shi da idonta." Ta ƙare tana murmushi.

"Allah koh?" Yaya Amina ta tambaya tana kallanta. Se ta jinjina kai jin ta amince da abin da ta faɗa. Girgiza kai Yaya Amina ta yi tace

"Ba ki da wayo Sa'adah.. Yanzu saboda shiritita irin taki Sa'adah ta yaya dan kar kishiyarki ta san da zaman ciki a jikinki za a ƙi sanarwa da me shi? Idan na yi hakan ma ai ban kyauta ba."

"Kai Yaya.." Mommah ta faɗa tana kallanta.

"Ki bari na kira na sanar da shi. Ina ma da tabbacin ba ze faɗa mata ba, tun da dai shi ba mutum ne me surutu ba. Ke nata cikin a bakinsa kika ji?" Girgiza kai Mommah ta yi. Yaya Amina tace

"Toh kin gani." Yaya Amina ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kiran Daddy ta sanar da shi abin da ke faruwa. A lokacin Daddy ji ya yi tamkar ya fi kowanne namiji dace, ya kuma fi kowanne mutum samun abun alkhairi. A lokaci ɗaya Allah na neman azurta shi da haihuwa biyu. Haka dai ya yi farin cikinsa shi ɗaya, farin cikin da ya kasa ɓoyuwa har a kan fuskar shi.

Lokacin da su Mommah suka dawo cikin gidan, ya yi daidai da lokacin da Mom ke fitowa daga cikin mota ita da Aunt Makiyy da suka dawo daga unguwa. Tuni Maimuna ta iso wajen ta soma yi musu sannu da zuwa. Lura da waɗanda ke kusa da su ne ya sanya Aunt Makiyy saka hannunta ta riƙo hannun Mom cikin er ɗaga murya yanda ta san za su ji ta tace

"Ki yi a hankali Yaya.. kar ki illata uban masu gida." Wani murmushi Mom ta saki jin abin da Aunt Makiyy ɗin ta faɗa, tace tana riƙo ƙugu, gami da tunkuɗo ciki gaba.

"Uhmm ai kam dai.." Ta yi maganar tana satar kallansu Mommah. Idan motar da suka sauka daga ciki ta ɗaga kai ta kalli su Mom, toh su Mommah ma sun kalle su. Baƙin ciki, takaici duk suka haɗu suka dirarwa Mom, ta ji kamar ta je ta kama Mommahn da er uwar tata ta yi ta jibga ko za ta ji sauƙin abin da take ji a ranta.
Se a lokacin ta fahimci wannan izzar Sa'adahn ba ara ta yi ta yafa ba. Da alama a jininsu take. Dan kuwa hatta Yaya Amina ma wani mugun kwarjini ta mata. Ga kuma komai nasu kamar iri ɗaya ne da na Sa'adahn. Wani abun baƙin ciki ma shi ne yanda suka nuna kamar ba su san da wanzuwarsu a wajen ba. Aikuwa ta ƙara shaƙa, ta ƙulu ta ƙulu.

"Ki kwantar da hankalinki Yaya.. Kwana nawa ne ya rage ki koma juya gidan a hannunki.." Aunt Makiyy ta faɗa dan kwantarwa da Mom ɗin hankali.

"Wallahi Hajiya kar ki damu. Da ma fa da gani wannan ƙatuwar matar ke zuga Sa'adahn. Ba dan haka ba ni kaina yanda na yi ƙoƙarin shiga jikinta ko wacce irin zuciya ce da ita ai ya ci a ce ta saki jiki da ni." Maimuna da ke gefe ta faɗa.

"Yoh ba tana tare da munafuka ba.. shegiya." In ji Aunt Makiyy tana bin bayansu da harara.

"Ni dai don Allah ku mu wuce kafin raina ya ida ɓaci." Mom ta faɗa tana yin gaba a fusace. Dan duk da maganar da suka gwaɓawa Mommahn da ta tabbatar ta ji zafinta, (amma fa a ganinta) ƙin tankawar da ta yi ya fi komai yi mata zafi.
Chapter 70 · 0% Book details