Sashe 99
Tukuicin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya kuwa suna gama magana da mm ta walawa mai aikin ta kira ta ce taje ta cewa Ado driver ya fiddo da mota za su tafi gidan Abba, kafin ta dawo har ta mi e ta je ta auko mayafin ta, tana fita Ado na fiddo motar ta fa a suka fice gidan tana fa "Ubangiji ALLAH ka shiryi al'ummar Annabi, da tsufanka amma a baza su bari ka zauna ka huta ba, wannan wace irin rayuwa ce haka muke ciki da bata banbanta banbancin dake tsakanin an goye da kuma manyan Ado driver dake saurarar maganganun da Hajiya keyi a zuciya suka fito fili ba tare data sani ba ya ce, "Ai Hajiya kuskuren bana rayuwa bace, na iyaye ne da basa tunanin tan wasa yara tun suna anana, a wautar su ai yara ne sunyi anta da hukunta wa ko ladabtar wa ko kuma nuna masu tausayi a wajajen da bai kamata ba, sai a wayi gari yaran sun girma suna son nuna masu daidai ha e da hukun tasu bisa kura-kuran da aka kasa gyarawa tun farko, su kuma yaran na nuna masu basu isa ba, wasu ma su saka su kuka tare da tarin nadama mai yawa" Duk da kalaman Ado sun daki zuciyar Hajiya, kasa cewa komai tayi don tasan gaskiya ce ya fa a, ita kuma gaskiya dama aci ne da ita, sai dai kawai ta sauke ajiyar zuciya a hankali ha e da cewa, "ALLAH ya kyauta kuma ya sawa e mana duk abunda ya fi arfin mu" Ado ya amsa da amin tare da tura kan motar cikin gidan na Baffa da tun kafin su ara so ya wangale kansa, suna yin parking Abba na fitowa tare da wasu abokanan sa su biyu, aya daga cikin ma cousin brother in Abba ne don dashi da Abba an ya da ane ne, cikin girmama wa suka ara so wajen suna gaida Hajiya lokacin data fito, shi kuma Abba na can baya yana waya, "A'ah, Alhaji Sadeeq yaushe a gari?" Hajiya ta fa a tana takawa zuwa cikin gidan, sai da ya yi dariya yana sinne kai asa alamun girmamawa sannan ya ce, "Jiya na dawo Hajiya, yanzu nake cewa idan muka dawo meeting zan je na gaida ki" "ALLAH sarki, kai dai ko don ka ganni shi yasa kace hakan, sharabon ka da wajena tun shekarar data wuce, sai dai naji labarin cewa ka je Austaraliya agun mahaifin ka" "Ayi ha uri Hajiya, yanayin kasuwancin ne a haka" "Kai dai kassa ni, yaran yanzu kun auki zumunci ba abakin komai ba, bayan ALLAH da kansa ya ce a sada zumun ta domin la e take a igiyar al-arshi" "In Sha ALLAH Hajiya za gyara" "ALLAH yasa, ya mahaifin naku da iyalan naka duk suna lafiya?" "Lafiya klw Hajiya" "Madall a ALLAH yayi albarka" ya amsa da "Amin" dai dai lokacin Abba ya gama waya shima, cikin girmamawa ya ce, "Hajiya sannu da zuwa" "Yawwa Usman, ina zuwa haka kuma?" "Meeting zamu je Hajiya tare dasu Alhaji Sadiq" ya fa a yana nuna su, "Ikon ALLAH, to ba in naka da ka ce kana jira?" "To Hajiya, na ce su zo kafin sallar azzahar amma har yanzu ban gansu ba, gashi har arfe biyu ta wuce basu zo ba wanda hakan ya nuna mani ba da gaske suke yi ba" "Assha, kasani ko wani abun ya hana su arasowa da wuri, halama arfe nawa zaku shiga meeting in?" arfe hu "To alhamdulillah, ka ga sai kayi masu uzuri tunda ko uku bata yi ba, na tabbata suna nan arasowa yanzu" ta are zancen ha e da juyowa tana kallon su Alhaji Sadiq dake tsaye jingina a jikin mota suna latsar wayoyin hannunsu tare da yi masu bayanin cewa su an jira suma su koma ciki ba i ne za su zo dake neman auren ar su Janan kafin lokacin shigar su meeting yayi, Ba yanda suka iya dole suka koma daga ciki Abba naji kamar ya fasa ihu, part in Hajiya zee ta fara shiga suka gaisa ta sanar da ita cewa za a yi ba i da zasu zo neman auren Janan kuma tasan babu abunda Abba ya tana da daza a tarbe su dashi, don haka in akwai abunda zata iya ha awa da sauri don kar aji kunya ta an ha a masu, Dama Hajiya zee ma'abociya son snacks ce ba ta rabuwa dasu akoda yaushe, don haka tana jin haka ta tashi tayi warming in samosa da cake da take dasu ajiye cikin fridge data yi jiya, sannan ta zuba su a cikin try tayi rafin in su da foilpaper, dama ko da Hajiya tazo tana suyar kaji, don haka suma ta zube su gaba aya cikin try tayi rafin in su kamar yanda ta yiwa snacks ta kawo gaban Hajiya ta ajiye tana fa "Hajiya wu annan ka ai ne akwai, sai kuma in abinci za a ora kafin su ara so" "Me nene anan" ta nuna try in kaji, Hajiya Zainab tayi murmushi ha e da cewa, "Wannan kaji ne aciki soyayyi, shi kuma wannan snacks ne, samosa da kuma cake" "To agaisheki ALLAH yayi albarka, ai nasan baza a rasa lemuna acan ba ko?" "Eh Hajiya" "To ki gyara, duk da naga a gyaren ki kike tubarkallah, in yaso in suka ara so sai akawo masu, ni bara na shiga can" "To Hajiya" ta fa a tare da rakkota har bakin part in, suna fitowa Jabir da mm na fito da kayan da suka zo dashi, wani irin fa uwa gaban Hajiya zee ya yi lokacin da idanuwan ta suka sauka akan fuskar mm daya zagayo ta baya ya fiddo da goro da dabino, sak fuskar tsohon mijin ta da kuma an ta Ahfan dake India wajen karatu, wanda jiya-jiya suka gama maganar sa ita da Hajiya har take cema ta sai nan da wata uku zai dawo, dafa Hajiya tayi tana nuna mm da yatsa ha e da cewa, "Hajiya wancan bawan ALLAH dawa ya yi maki kama" "Wa kenan" Hajiya ta fa a daidai lokacin da mm ya bu e motar ya shiga ha e da tayarwa ya bar gidan don ba dashi za a shiga ba, asalima ya yi waya da Janan zai same ta acan makaran ta, Jabir kawai ne da Baffa da amininsa zasu je nema masa auren, murmushi Hajiya tayi lokacin da idon ta suka sauka ga wanda take nufin don shi bai ma lura da Hajiyar ba sannan ta ce, "Wai Muhammadu kike nufi?, Ai shine wanda Janan ke so kuma shi zata aura" dama su Baffa tuni sun wuce ciki don haka sai Hajiya zee bata kawo komai aranta ba sai dai ta ce, "Wlh kama yake yi da mahaifin su Ahfan, sai ma naga kamar su aya da Ahfan Juyowa Hajiya tayi don ta ara tabbatar da zancen ta amma inaa.., tuni mm ya fice daga gidan, shiru tayi kamar mai wani tunani kafin can tace, "Tabbas sunyi kama da Ahfan in, mahaifinsa dai ne kin san ba wani wayuwar juna mukayi dashi ba" "Ai Hajiya Ahfan gaba aya fuskar mahaifin sa ce dashi, ALLAH dai ya ji ansa da rahama yasa aljannah ta zamo wajen hutu agaresa" "Amin ya rabbi, kinga bari na koma ciki tunda sun arfi" Hajiya ta fa a tare da juyawa ta koma cikin part in Hajiya zee, ita kuma tayi tsaye tana kallon gate in da mm ya fice cike da tunani kala-kala a zuciyar ta jima a tsaye kafin ta juya ta koma ciki itama tare da shiga kitchen ta fara arin ha a abincin da bazai auki lokaci ba kafin su tafi, hakan ya sa ta kunna gida uku na gas kowane ta aza masa abinda zata ha awa a jellop in ta ta priderice with vegetables da tayi tunanin orawa Jabir kuwa ya shiga kwashe kayan yana shiga dasu daga ciki ba tare daya damu da sai gate man in dake tsaron wajen dake kallonsa ya ri a masa ba, a mayar arshe da zai auko akwatunan kayan da suka zo dashi ya ci karo da Nihal na fitowa daga cikin guiden kunnen ta la e da earpiece, kallo aya ya yi mata ya auke kai tare da arin shiga daga ciki, ganin ayar jikkar daya ri on na arin fa uwa ya sa ya du a yana arin gyarata yanda zai iya ri e ta har ya ara sa daga ciki, Nihal na zuwa ta bingije sa har sai daya fa asa tunda ya riga ya du a ne bai sarar ba bingije sa in, kuma ta wuce abunta ba tare dako kallon sa tayi ba, cikin zafin rai ya ago kai ha e da mi ewa, yana taku aya ya ya dam o gashin kanta da tayi parking ha e da janyo ta baya, tana juyowa ya auke ta da wani zazzafan mari da sai da duk wanda ke falon ya ago kai yana kallon su, ba tare daya damu ba ya ce, "Ke wace irin jaka ce, da iya, dabba da bata san darajar mutane ba, ko an fa a maki cewa mu bayin gidan ku ne da zaki bin gujeni kuma ki wuce abunki ki kasa bani ha uri?" Cike da zafin rai abokin Abba ya mi e zai yi magana Abba dake zaune ya shige can cikin kujera tare da aza afarsa aya akan aya ya ri e baki da hannu yana kallon su ya dakatar dashi, komawa ya yi ya zauna yana kallon Jabir daya nuna ta da yatsa yana fa "Idan kika ci gaba da rayuwa haka saboda ganin wannan dau ar duniya to tabbas rayuwar ki zata zama abun tausayi nan gaba, wawiyar yarinya kawai, fice daga gabana kafin nayi ball dake" ya are zancen cike da yimata garga i sannan ya koma ya auko jikku nan ya shigo daga ciki ya ajiye sannan ya fice ransa a ace, Nihal kuwa kallon Abba tayi taga ya kauda kai gefe, upstairs in ta nufa tare da fashewa da kuka ta haye da sauri da sauri tana ji kamar ta nutse asa, Runtse idanuwa ya yi saboda jin zafin kukan da take yi tare da bu e wa a hankali ya saukar