Sashe 77
Tukuicin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
raye ko kuma ALLAH yayi nasa iko akanta don sam ba muda labarin ta" "Kamar ya Baffa" ya fa a tare da matsowa kusa dashi ya ri e hannunsa, wani yanayi yaji ya tsinci kansa a ciki yanzu, shi ba farinciki ba kuma shi ba ba in ciki ba, ganin yanda gan aya ya tashi hankalinsa yasa Baffa cewa, "Yi ha uri Muhammadu zan fa a maka komai, yanzu dai ka daure ka fara tashi ka watso ruwa kaci abinci sai muyi magana a tsanake kaji ko?" "Baffa dona ALLAH..." "Subhanallahi, kaddai kacemun har yanzu halin nan naka dana sani na kafiya da naci na nan" babu yanda mm ya iya dole ya ha ura Baffa ya ce su wuce dashi cikin gida ya watsa ruwa ya huta kafin yazo, don zai je gidan mai gari ya aiko kiransa azu kafin ayi Sallah, haka mm na ji na gani Baffa ya fice daga gidan ba tare daya basa labarin komai ba akan mahaifiyarsa, an uwa kuwa sai murna sukeyi da aka shiga dashi cikin gida ga an kawo Muhammadu daya ace ya dawo, babban gida ne sosai dake auke da angaren shiyoyi har guda biyar aciki, shiyar farko itace ta Baffa Ali da matan sa su biyu, indo da kuma Atika, sai shiya ta biyu da umma Mariya ke ciki ita da anta su bakwai, ita in yaya ce a wajen mahaifin mm da kuma Baffa Ali, ta dawo gidan da zamane sanadiyar mijinta da ALLAH yayiwa rasuwa, sai shiya ta ukku, talatu ce a ciki wato matar Baffa Bala, shima an kashesa lokacin da arayi suka shigo auyen, kasancewar an mata uku ne da ita alokacin yasa ita ka ai take zaune a ciki sai jikokin ta dake zuwo don gaba aya ta aurar da an nata da take dasu, sai shiya ta hu u ita kuma rufe take ba kowa aciki, wacce ta kasance shiyar Baffa sule ce, kasancewar shi mazaunin Katsina ne acan yake aiki, don shi ka ai yayi karatun boko acikin su shi yasa yayi aurensa acan tare da matar sa aya da yaran su biyu, macce da namiji, yasa baya zama ciki, saidai idan wata hidima ta tashi yazo da iyalinsa kuma ana gamawa zasu koma, shima ALLAH yayi masa rasu a ranar da arayin suka shigo auyen, ba tare da saninsa ba yazo ganin gida, yana shigowa sukayi arba da shi suka kashe sa, sai bayan anzo ana har ha a gawarwakin mutanen auye da aka kashe suka tsinci gawar sa aciki, sosai Baffa Ali ya so anso yaran alokacin amma karamci da mutuncin dangin mahaifiyar su yasa suka bar su acan, yanzu haka duk sun girma har ta farkon mai suna Ru ayya tayi aure shekaru biyu da suka wuce, shi kuma namijin mai suna Ahfan yana India wajen karatu, a shekarar nan ma zai arewa, don dangin mahifiyar tasu sukan kawo su lokaci lokaci tun suna anana shiyasa duk halin da suke ciki suka sani, ita kuma shiryar arshe wacce itace ta biyar autar su Baffa ce aciki umma luba, har wayau itama mijinta kashesa akayi a shekarun baya ya je gona, saidai aka dawo mata da gawarsa anyi masa yankan rago, shine dalilin da yasa itama ta dawo anan gidan da anta su biyar, kuma cikin taimakon ALLAH gaba aya familyn duka Baffa Ali ne ke auke da nuyin su yana kulawa dasu dai dai gwargwado iyawarsa saboda duk ankashe mazajen su, daga matan nasa har matar anensa da yayarsa da aunarsa shine da ba in kula dasu don shi ka ai ya rage masu na miji, sai kuma yanzu da ALLAH ya dawo masu da mm agaresu, wanda ko shakka babu dawowar tasa itace fassarar mafarkin Baffa, don shi zai kama masa wajen cigaba da kulawa da wanna ahalin nasu. (Wannan matsalar itace al'ummar auye harma dan birnin ke fuskanta a yanzu, sai kasamu macce sama da goma, amma namiji ne aya jigon dake kula dasu sanadiyar mazajen su da aka kashe, ya ALLAH ka kawo mana sassaucin wannan rayuwa, kasa mu canye wu an nan jarabawoyin) Kasancewar akwai gajiya sosai a tattare da mm yasa ko daya watso ruwa a shiyar umma Mariya yaci abinci bacci yayi awon gaba dashi, don ba ka an tafiya mai nisa ta mota ke jigata sa ba saboda sabon daya yi da tafiye tafiye cikin jiragen sama, bai farka ba sai da lokacin sallar la'asar yayi, umma Mariya ta tadasa bayan ta zuba masa ruwa a buta, wani irin bacci ne mai da i daya jima baiyi ba cike da da an mafarkai yayi, hakan yasa ko daya farka baccin ya ji kaso saba'in bisa ari na cikin damuwar daya kwanta da ita ta gushe, tare da fatar ALLAH ya tabbatar masa da abun daya gani cikin mafarkin nasa, Bayan ya dawo wajen Sallah indo ta bakka Maryam fura mai sanyi da nono ta kawo masa, lokcin yana zaune ofar gida yana jiran fitowar Baffan nasa, Baffa kuwa ana are Sallah ya juyo ya sanar da mutanen auye cewa ALLAH ya bayyana masa an wajen Malam Muhammadu yayan sa daya ata, yanzu haka yana nan yazo, wannan dalilin yasa ya jima bai fito ba saboda tsayawa tayasa murna da sukeyi, kallonsa Maryama data ajiye masa fura tayi ha e da cewa, an bunni wai gashi inji indo ta ce akawo maka" ka ai mata kai yayi sannan ta wuce ciki ha e da regowa tana kallonsa, sai ta kwashe da dariya ta koma ciki aguje, dariya abun ya bashi don haka tana sake regowa ya ce, "Zo nan mana" cikin jin kunya ta rufe fuskar ta da tafi ha e da zuwa gabansa tayi tsaye, sai daya girgiza kai sannan ya ce, "Ya akayi ne halan kike le ena" saida ta washe ha ora ha e dayin dariya sannan ta ce, "ALLAH irin ka muke gani a talabijin in umma luba" "Dagaske kike yi?" "ALLAH kuwa" "Ya sunan ki?" "Maryama.." tayi saurin rufe baki da komawa cikin gida aguje hango Baffa tafe shida mutane, dariya mm yayi ha e da mi ewa tsaye lokacin da suka araso wajen suka shiga mi a masa hannu ana gaisawa tare da sanya masa albarka, bayan duk sun wuce Baffa yayi masu godiya ha e da rakkiya sannan ya juyo yana kallon mm, "Ho malam Muhammadu, tun azu ka matsu na fito ko?" ya sosa gefen kunnensa ha e da sinne kai asa yana murmushi, cikin gida Baffa ya shiga ya auki tabarma ya sake shimfida masu anan soro sannan ya ce, "Bisimillah yayan Baffa" don yakan kirasa da hakan tun yana arami, aukar kwanon furar da Maryama ta kawo masa ya yi sannan ya wuce ciki shima ha e da cire takalmansa ya zauna akan tabarmar suna fuskantar juna shi da Baffa, kusan rige-rige sukayi wajen fara magana Baffa ya ce, "Fara aukar furar ka kasha tukuna sai na baka labarin ko" kasancewar shi mutumne da bai fiye son gardama ba da ata lokacinsa ya sa duk irin yanda ya matsu daya san labarin mahaifiyar tasa ya ha ura ya fara aukar furar ya sha, sai daya sha fin rabi sannan ya ajiye kwanon furar, "Ta isheka?" Baffa ya fa a yana murmushi tare dasa hannu ya goge masa gefen baki da ar furar ta ta a masa, "Na gode Baffa, amma nayi mamaki da ka ce mahaifiyar mu bata mutu ba Baffa, a gabana ta ara sa rasuwa kuma nasa hannu na shafeta" "To Muhammad, wannan al'amari ai na ALLAH ne, bana tunanin zaka iya sanin yanda mutuwa take daidai bayan a lokacin baka wuce shekaru goma sha biyar ba a duniya" "Kenan hakan na nufin doguwar suma ce ummatah tayi a lokacin?" "Sosai kuwa, don ko da hukumar an sanda ta kawo agaji bayan tafiyar arayin ana har ha a gawarwakin da suka kashe, tare da wu an da suka ji rauni an samu mahaifiyar ku kwance cikin jini itama kamar matarta, amma ana auko gawarta sai aka ga numfashin ta ya dawo, hakan yasa da sauri aka sanyata cikin motar asibiti wato ambulance aka wuce da ita general hospital dake can cikin gari, ganin taji rauni dole tana bu atar aikin gaggawa yasa aka wuce da ita babbar asibiti dake can cikin Katsina, babu wanda ya sa mata ran fita hatta likitoci saboda yanda dafin wu ar da aka da a mata ya shiga jikin ta sosai ya kuma yi nasarar yankewar gefen an hanjin ta, amma cikin ikon ALLAH da aka gwada yimata aiki tare da dasa mata gefen an hanjin daya yanke sai gashi anyi nasarar ceto rayuwar ta, ta sha jinya sosai don wata biyar tayi a asibiti kwance, kuma alhamdulillah ba laifi mun samu tallafi gwamnati a wancan lokacin, bayan ansallamota ne ta fara bijiro mana da zancen inda kuke, mu kuma bamu san amsar bata ba, kullum arin mu shine mukwantar mata da hankali, amma hakan ya cutara saboda kullum cikin unci kuka da kuma damuwa take tana ambaton sunan ku, wasa wasa abun ya fara zame mata sabbatu ta koma tamkar mai ta in hankali, ta sha wahala sosai saboda munyi tsammanin ko aljanu ne ke damunta kullum cikin ruquya da shan magunguna take yayin da wani likita aya ta a dubata ya ce mana babu abunda ke damunta sai tarin damuwa da kuma tunani kuma idan ba'a kula sosai ba zai iya ta a lafiyar ta, da muka ga abun sai ara arfi yakeyi yana nema yafi arfin mu sai muka yanke shawarar mi ata asibitin mahaukata domin sama mata lafiya, kwatsam daren da za'a zo a auke ta muka nemeta muka rasa, mun ji a ci sosai mun kuma yi ba in ciki da faruwar haka, kama daga jahar Katsina birni da auye har zuwa zagayen ta babu inda bamu je neman ta ba amma bamu ganta ba, dole muka ha ura muka barwa ALLAH lamarin tare dasa ran bayyanar ta agaremu indai tana raye ko don anta, amma har yanzu ba muda wani labari akanta, tana raye ko kuma akasin hakan ALLAH ka ai ya sani, " "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun" ka ai mm ya iya furtawa ha e da fashewa da wani irin kuka mai tsima zukatan wanda ke saurara, babu abunda