← Book details Tukuicin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 120

Sashe 6

Tukuicin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ingaski ya fad'a ba tare da ya juyo ba adaidai lokacin da take qoqarin aza qafarta ta shiga cikin aji, runtse idanuwanta tayi tare da komawa baya batare data aza qafar tata ba tana jin wani irin qunci da kuma sululi acikin zuciyarta, dama tasan za'a rina, mutumen daya takura rayuwarta ba tare da tayi masa komai ba balle yanzu data aikata laifin da tasan ko bashi bane hakan zata iya faruwa, ALLAH dai ya kyauta ta furta cikin zuciyarta had'e rolling idanuwanta tana furzar da iska abaki sannan takoma a gefen qofar ta tsaya,
"Sorry sir, I got an accident on my way coming that's way"
Ba tare daya damu da juyowa ya kalleta ba balle har ya saueari uzurin da take qoqarin kawo masa yaci gaba da yiwa d'alibbai lecture d'insu hankali kwance, saida ya kammala lecture d'insa tsaf sannan ya juyo yana qare mata kallo tun daga sama har qasa, hannayenta tasa ta jawo mayafin abayar dake jikinta tarufe qirjinta daya qurawa idanuwa tana turo baki, murmushin gefen baki ya sakar mata had'e da d'aukar teaching materials d'in daya shigo dasu yana fad'in, "meet me in my office Janan" sannan ya fice fuskarsa d'aure tamkar bashi bane yagama yimata kallon qurulla don kar d'alibbai suga damarsa, murgud'a baki tayi bayan ya wuce tare da qarasawarta cikin aji hankali kwance ba tare da tadamu da binsa baya ba kamar yanda ya buqata,
D'aure fuska tayi ganin yanda 'yan uwanta d'alibbai ke binta da kallo bakunansu d'auke da alamar tambaya akan qin bin bayan Dr ingaski da tayi,
"What?" Tafad'a tana zaro idanuwa tare da ware hannuwanta gefe gefe, alokacin d'aya daga cikin qawayenta da suke zama tare Amira ta samu damar yin ajiyar zuciya had'e da cewa,
"Janan bakiji me dr.

Ingaski yace ne ba?"
"Naji man, sai akaye me?" Tafad'a had'e da zaunawa,
"Sai akayi me ma kike tambaya Janan, halama kin manta ko waye shi?

"ALLAH ne shi?"
"Ko d'aya, mutum dai ne mai tsananin iko akan karatunku, don girman ALLAH kirufa mana asiri ki tashi kije kada kishafa mana kashin kaji awurinsa"
"Tab!

Wlh bazani ba, me zanje nayi masa bayan 'yar lecture d'in tasa da nake kwad'ayin samu da attendance don gudun matsalarsa ya hanani?, Kawai ki qyalesa na manta ne shiyasa banje ba, dt's zit"
"Hmm!

Gamu ga ALLAH" Amira tafad'a tana zabga wani uban tagumi,
Dariya janan tayi had'e da dukan
bayanta, "Amira kenan, dama ke a hannun Ingaski kike ba'a hannun ALLAH ba?"
"Mts...kidena don ALLAH, wlh gaba d'aya a tsorace nake, ban cika son kina shiga 18 d'in malamin nan ba" taqare maganar tare da cire hannun janan d'in daga bayanta.

"Matsoraciya kawai" Janan tafad'a tana jawo takardun dake gaban Amira da tayi jotting.

"Naji dai koma meye zakice, tsoro ai gaskiya ne, musamman na irin wud'annan malaman da basa fatan gamawa lafiya da dalibbansu"
"Kyaji dashi nidai, dame dame yayi maku ne?, pls help me and explain it for me"
"Bazan iya ba, jeki keda ba matsoraciya ba yayi maki, bama wannan ba, meya sakaki latti Janan keda bakya son abunda zai had'aki dashi?

"Bari kawai, ai daga yau angama don bansan meye amfanin da tsoron nasa ke haifarmun ba, kinafa ji nake fad'a masa accident nayi kafin naqaraso amma yayi banza dani, shiyasa nima nayi banza dashi saboda duk abunda yafaru yau shine silar dana aikata hakan, don haka wlh munsa qafar wando d'aya dashi kenan Amira"
"Tofah! meya farune?

Kuma kina ganin ke zaki iya dashi a matsayinki na d'aliba shi kuma malami?, Kinga ajiye duk wani mafarki ka kikayo da yasa kike neman maidashi gaskiya ki shafawa kanki lafiya"
Kallon gefen idanuwa Janan tayi mata had'e da harara kafin race,
"Naji, sai kuma meye?"
"Kitashi kije kiji meyake kira gareki saiki dawo nayi maki bayanin"
"ALLAH bazan je ba Amira kinji ma na fad'a maki, in zakiyimun bayanin nan kawai kiyimun in kuma bazakiyi ba naje pro (wani student a ajin) yayi mun"
"ALLAH ya baki haquri."
Amira ta fad'a tare da gyara zamanta ta shiga koyar da ita had'e da yimata bayanin abunda Dr.

Ingaski ya gama yimasu, har goma da rabi tayi bata gama mata ba kasancewar lecture da suke da ita gaba ta 10-12 malamin bai zo ba, basu suka gama ba sai 11 saura mintuna goma Janan ta kalleta had'e da cewa,
"Thanks qawata, gaskiya kanki na ja, wlh dama an had'a ki aure da Ingaski kinga shikenan ku kakarku ta yanke saqa, bakida wata matsala indai akan karatune hakama 'ya'yanku"
Tattare littafan Amira tayi kamar wacce ke shirin tafiya, aikuwa Janan bata sarar ba ta d'ima mata su abaya tana fad'in,
"Aniyar mod'a dai tabi randa Janan, ALLAH ya tsareni aurn sa'ar ubana tunda ba baki akayimun ba, sa'arsa ma d'in kuma ace wai Ingaski, godforbide wlh, in sha ALLAH over my died body bazakiga hakan ba Janan, wannan ai shi ake kira mugun tare tsakaninmu tunda kike yimun irin wannan muguwar fatan"
Taqare zancen in a serious tone kamar zatayi kuka, dariya Janan ta saka mata har tana riqe ciki saboda qeta kafin can tariqo hannunta ganin tana shirin tafiyarta tabar wajen,
"Sorry qawaliya romon jab'a, ai nima da wasa nakeyi bazan so hakan tafaru ba, muje ki rakani wajen MM tunda sai 12 zamu shiga"
"Kinga nifa yau tsoron ma tafiya nakeyi dake kar wancan bawan ALLAHn ya ganemu tare, me zakiyi awajen MM keda ba abun makarantar nan kike ci ba"
"Wlh shine kad'e da zan shigo kwanar department d'in nan da kikaji ina zancen nayi accident"
Kusan fad'uwa littafan hannun Amira sukayi jin me take fad'a da sauri ta tarosu tana fad'in,
"MM d'in kika kad'e Janan?

Garin Yaya?" Har idanuwanta na kawo qwalla,
"Tofah!

Meye haka Amira?, daga magana sai kiwani bi ki koma kalar tausayi, kodai kema kina cikin masu son nasa"
Kauda fuska Amira tayi ta goge 'yan guntayen hawayen da suka zubo mata agefen ido had'e da cewa,
"Tashi muje, hop dai baki jimasa ba ko?"
Mere baki Janan tayi don tana kallon abunda tayi had'e da cewa,
"Gaskiya ya d'an jimu a fuska, kuma duka kayansa sun zube"
"Kuma shine kika iya zuwa lecture Janan don rashin tausayi?, Kada fa kisa nafara zarginki da wulaqanta mutane don kin ganesa talaka" Amira da tajuyo rungume da littafanta fuska a d'aure ta fad'a tana nunata da yatsa, baki bud'e Janan ke kallonta kafin tace,
"To ke wai meye naki Amira?, mai qaya ya daure sai mai cira ke kuka?, Kinga, watch ur tongue, ni bana son kina jifata da irin wud'annan nan maganganun kuma kinfi kowa sani tunda ba haka bane"
"Ada ba, yanzu kam ai banada wannan tabbacin tunda kika aikata hakan"
Nan fa suka rikice da fad'a, ta fad'i itama ta fad'i sukayi baran baran da ita kowa ya kama gabansa, Kai tsaye Amira wajen dasu mm ke sana'a ta nufa acan nesa kad'an dasu inda zata iya hangosa a bayan wani iccen beji ta b'uya tana kallonsa, ganin babu wani serious enjury d'aya samesa sosai yasata juyawa ta jingina ajikin iccen tana sauke ajiyar zuciya tare runtse idanuwa ta furta, "Alhamdulillah" a hankali tana mai qara jin wata irin qaunarsa na zagaye lungu da saqo na zuciyarta,
Janan kuwa kai tsaye wajen motarta ta nufa ta fad'a ciki had'e da kife kanta ga jikin sitarin motar, "me yake faruwa da ita ne hakan da take faman cin karo da kalaman da tafi tsana arayuwarta yau?, meyasa abunda bata tab'a yiba yau take aikatasu, accident, fad'a da kuma kafiyar da tayiwa dr Ingaski ita sake matuqar tsoronsa, duka hakan fa ba halinta bane, meke faruwa ne da ita" ta shiga tambayar kanta cike dajin haushin fad'an da sukayi ita da qawarta Amira,
Janan kyakkyawa ce sosai dake da matsakaicin shekarun da bazasu wuce gama sha tara ba, tana da tsayi daidai gwargwado tare da kyakkyawar sigar data fidda shape din jikinta, farace sosai irin farin nan mai madara dake da 'ya fad'in fuska kad'an tare da tsawon hab'a, tanada idanuwa da dogon hanci irin mai d'an tsayi kad'an ba sosai ba, duk da bakinta ba d'an qarami bane haka bazaka kirasa da babba ba saboda yanda ALLAH ya tsaga labban da yake d'auke dasu daidai misali, tanada son wasa da tsokana amma fa duk da hakan bata son reni da kalaman aibatawa, ba kasafai take nuna gazawarta a lamurranta ba har sai abu yakai maqura saboda haaurinta, ataqaice dai zaka iya cewa tako ina tayi sai inda baka rasa ba, koshi d'in don d'an adam tara yake bai cika goma ba.
Chapter 6 · 0% Book details