Sashe 100
Tukuicin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
da idanuwa akan Baffa dake faman zuba bayani, cikin isa da gadara ya dakatar dashi ha e da cewa "Ba wa an nan maganganun nake son ji daga bakin ku ba, so kawai na keyi naji shin kun shirya aurar da an ku ne?" "Eh Alhaji, ai shine dalilin aya kawo nan" "Ya sanar daku cewa sati mai zuwa ne aurin aure?" "Eh ya sanar damu" "Kuma kun aminta da hakan?" "Eh mun amince tunda har suna son junan su" "Shikenan, mu ma mun amince, tare da fatan baza mu saida akuya ta dawo tana cin danga ba" "In sha ALLAH Alhaji, mungode ALLAH ya saka da alkhairi yabar zumunci..." ko rufe baki bai yi ba Abba ya mi e yana bin kayan da suka zo dashi da wani irin mugun kallo sannan ya wuce ba tare daya sake cewa dasu uffan ba, da abokin Baffa ma yayi masa zancen yanka sadaki cewa ya yi su je duk abunda suke da hali su kawo don basu da arzi in da zasu iya biyan sadakin arsa, kawai suje su ha a abunda ALLAH ya hore masu kafin ranar aurin auren su kawo, shi dai Baffa imani ne ya cikasa ha e da tsoron ALLAH ya bisu da kallo har suka fita, Suna kaiwa bakin ofa Jabir na kawowa zai shiga, gefe ya ra e har sai da suka wuce Abba na biye dasu a baya, kallon kallo suka shiga yi da Jabir sannan ya wuce yana jin wani tu i da ba in ciki aran sa, wanda ya tabbatar ba kowa ya jawo masa hakan ba sai Janan, "Alhaji Usman wai wane ne wancan yaron?" Alhaji Sadeeq ya fa a yana nuna Jabir daya shige cikin gidan, "Kaman ta da zancen za muyi magana idan mun dawo" "A gaskiya bai kamata ace kamar ka irin wancan yaron na rena maka da wayo ba, shin ba yaron gidan ne ba?" "Ku muje" kawai Abba ya fa a don baya son maganar, a halin yanzu sam baya da lokacin Jabir har sai ya gama da matsalar dake gabansa, abun da ma ya basa mamaki shine, meye ha in sa da iyayen yaron nan daya gansa tare dasu, zai iya yuyuwa yaron abokin sa ne ko kuma cikin dangin maman sa, wata zuciyar ta bashi amsa a ta aice, no bazai yuyu ace dangin mahaifiyar sa bane shi, idan kuma har haka ne kenan shima tubabbe zai aurar wa da arsa, impossible, ya fa a da arfi ba tare da yasan maganar da yake yi a zuciyar sa ta fito fili, Suna arin shiga motocin su Hajiya ta fito ha e da cewa, "A'ah, ya haka Alhaji Sadeeq?, Ina ba in naku ne har sun wuce?" "A'a Hajiya suna ciki mun gama magana ne, kinsan jiran mu akeyi" Girgiza kai kawai tayi ha e da cewa "To shikenan ALLAH ya kiyaye, shi dai girma sayen sa akeyi idan kuma aka gagara siya, tofa tabbas zai fa i" tana gama fa ar haka ta wuce part in tana jin acin rai a ranta, Ko data shiga ta samu har sun mi e suna arin fitowa su da Jabir, cikin sakin fuska suka shiga gaggaisawa tare da yimasu sannu da zuwa sannan ta fara basu ha uri ha e da cewa, "Kuyi ha uri fa, suna da meeting ne shi yasa kuka ga suna gaggawa haka, ya ce na baku ha uri kuma kusan tsaya kuci abinci kafin kuwuce" Mere baki Jabir ya yi yana kallonta kafin yayi asa asa da murya ya ce, "Ke dai ar tsohuwa fa i gaskiya, kice kawai kina kare an ki ne don kar aga rashin kyautawar sa" an duka ta kai masa a gefen hannu ha e da cewa, "Ja'iri, jeki ka kaisu wancan falon suci abinci kafin su wuce" "Wane falon?, Ni ina zan san yanda wannan gidan naku yake, kece dai ar gida jeki ki kaisu, wannan gida haka sai kace gidan family gaba aya, atunanina duka family in mu gidan nan zai auke su, amma an ki ya tara irin wannan dukiya kuma baya iya taimako an uwa da ita, sai yanda yake so yake yi da ita da shi da an sa, ba komai ALLAH ya bamu namu muma" are zancen tare da wucewa falon data nuna masa da hannu yana cewa su Baffa dake tsaye acan gaba su wucik ke" Hajiya kuwa jikin ta ne yayi sanyi da kalaman da Jabir ya fa a tare dajin tausayin sa aranta, wallan da suka zubo mata ta goge sannan ta walawa Nihal kira, ba a fi mintuna uku ba ta sauko tana tu uburi idanuwan ta sun yi jajir saboda kukan da tayi, kallon ta Hajiya tayi ha e da cewa, "Ke lafiya?" Har zata bu e baki tayi magana sai ga Jabir ya iso wajen, harar ta maka masa ha e da turo baki ta koma ta bayan Hajiya, "Kina yin magana zan sake zabga maki wani marin, da iya kawai" ya fa a shima yana maka mata harara, "Haba Jabir, meye amfanin wannan maganar haka, ar uwar ka face amma kake kiran ta da da iya, kalmar batayi da i ba" "To Hajiya kiyi ha uri na dena, amma wannan yarinyar da kike gani kan kifi ne da ita, kuma matu ar za muci gaba da ha uwa da ita sai na yi maganin ta" ya are zancen yana nuna Nihal da yatsa, "Ke jeki part in auntyn ki ki kar o masu abinci, dama nasan wannan rashin kunyar taki za a yi maganin ta duk ranar da kuka ha u dashi, don haka gaki gashi" ta are zancen tare da wucewa ta zauna akan kujera, ita kuma Nihal ta wuce part in Aunty zee tana sake turo baki cike da haushin su duka.