Sashe 7
Tukuicin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bata tafa fad'a da wani ko wata ba koda na fatar bakine tun tasowarta sai yau saboda kauda kanta ga abubuwan da basu fiye shafarta ba, sai gashi yau bata san meyasa ba tayi da qawarta, d'an tsaki tayi tare dasa key d'in motar ta tayar tabar wajen don taji gaba d'aya lectures d'in sun fice mata akai kawai bari taje gida, kamar ance ta d'ago kanta lokacin da take tafiya kan titin makarantar a hankali zata je gida idanuwanta suka sauka akan mm dake wajen sana'arsa da har ta soma mantawa da abunda ya faru tsakaninsu d'atsu, parking tayi a gefen titi tare da fitowa cikin motar ta nufi wajensu,
Kallo d'aya mm yayi mata ya kauda Kai saboda wani irin Abu da yakeji na tsirgo masa tun daga tsakiyar qafafuwansa har zuwa qwaqwalwarsa,
"Assalamu alaikum, sannu ko Mm, Ina kwana?" Yaji ta fad'a lokacin data qaraso wajen, kallon Jabir yayi daya murtuqe fuska ya juyar da kansa gefe ganinta sannan ya maido kallonsa gunta had'e da cewa,
"Lafiya klw Janan, har kin gama lectures d'in"
"A'ah, gida dai Zan je am not in the mood, don haka bazan iya sakawa kaina komai ba, ya jikin?" Tafad'a tana kallon goshinsa d'aya d'an kumburo kuma ya fad'a kad'an yayi ja, Saida yasa hannu ya shafo gurin ganin tana kallonsa sannan yace,
"Ai naji sauqi, kawai dai d'an ciwon kaine kad'an nake ji"
"Ayya sorry, kayi haquri don ALLAH, banji dad'in faruwar hakan ba ko kad'an"
"Karki damu, in sha ALLAH Zan koma normal zuwa anjima"
Tsakin da Jabir ne yayi ya d'an kauda murmushin data qaqaro a fuskarta tare da kallon Jabir tace,
"Jabir kadena jin haushi na, ita fa qaddara tana faruwane akan kowa kuma a sanadiyar kowa, saboda haka kayi haquri kaima don ALLAH bani ba"
Ganin bai amsata ba yasa mm yad'an taka qafarsa da sauri ya d'ago kai yace
"Shikenan"
"Nagode Jabir sosai, mm ko zakazo muje clinic d'in school tunda nafito da katina na clinic saina karb'a maka magani tunda kace kanka na ciwo ko kuwa Jabir?"
"A'a kibarshi angode" Jabir yafad'a a daqile had'e da miqawa wata student dabino data siya, d'an gyara tsayuwarta tayi tare da juyawa tana kallon yanda d'alibbai 'yan uwan nata ke kaida kawo acikin makarantar kafin ta maido kallonta garesa,
"Jabir kenan!
Har yanzu dai baka haqura da abunda nayiwa abokinka ba?, Fad'amun! me kake so nayi da zaisa kaima ka haqura, bana son kana yimun kallon tunanin da qwaqwalwarka keyi akaina"
Kallon mm yayi daya saki baki galala yana kallonta duk wani motsi nata burgesa yakeyi musamman yanda gefen chicks d'inta ke motsawa idan tana magana, yanda yayi masa d'azu ya taka masa qafa shima yayi
masa had'e da cewa,
"Kuje mana idan kana buqatar hakan tunda kace kanka na ciwo, amma gaskiya yakamata kiriqa kulawa kema ko ba'a cikin makarantar nan ba, Rai fa d'aya ne daga shi ba wani, idan yafita kuma shikenan" yakai qarshen zancen yana kallonta, murmushi ta d'an saki had'e da cewa,
"To shikenan angama, kuma in sha ALLAH zan kula, mm zamuje clinic d'in ne ko kuwa?"
Sai alokacin hankalinsa ya dawo gangar jikinsa da sauri yasa yatsa ya sosa gefen idonsa cike da kunya don tabbas ko shakka babu ta lura da irin kallon da yakeyi mata, ita kuwa bata kawo komai aranta ba na rashin maganar da yakeyi sosai saboda ta saba jin irin miskilancin da yake dashi a bakin student, wataqil hakan ALLAH yayisa shiyasa ya samu aboki mai shegen surutu da tsiwa atare dashi.
Ganin yayi shiru baice komai ba ya sata juyawa ta wuce gaba, kallon Jabir yayi suka had'a idanuwa yayi murmushi shi kuma ya mere masa baki had'e da cewa,
"ALLAH dai yafidda a'i ga rogo....wannan rawar qafar taka daqyar in zata tabari ka iya tafiyar da plan d'inka yanda ya kamata"
Juyowar da Janan tayi ganin har tana qoqarin tsallaka titin bai qaroso ba yasa mm rufe bakinsa ba tare daya tankasa ba yabi bayanta,
Kusan tare suka tsallaka titin da ita inda motarta take ta nuna masa can gefen motar da key d'in dake hannunta alamun ya zagaya ya shiga itama tana qoqarin bud'e gaban tashiga, murd'a marfin ya riqayi da qarfi kamar mai shirin kokuwa yana fizgarsa, ala tilas bai iya ba, dariya tayi had'e da miqa hannu bayan ta shiga ta bud'e masa gefen nasa ya shigo,
"Mm stop pretending, a yanda kake d'in nan babu ta yanda za'ace baka iya bud'e marfin motar ba, saidai ko kawai kace qilan baka tab'a shiga irinta ba" taqare zancen tare da murd'a sitarin motar tana dariya tabar wajen, gabansa ne ya fad'i kodai Janan ta sanshi tasan plan d'in da sukeyi?
Amma duk da hakan sai ya sake matsewa tare dasa hannayensa agefen kafad'unsa ya zagaye jiki dasu yana fad'in,
"Kai, ya akayi naji sanyi?
Gaskiya yayi yawa zan iyayin zazzab'i, ajeni nafita sai muhad'u acan, juyowa tayi ta kallesa sannan tasa hannu ta rage qarfin sanyin a.c daya mamaye motar don tasan a kanshi yake maganar ba tare da tasake cewa komai ba har suka isa bakin clinic d'in, yanayin parking ya fara qoqarin tura marfin motar da qarfin tuwo wai zai fita, dariya tayi ta sake cire lock d'in da tasawa motar gaba d'aya sannan tamiqa hannu ta sake bud'e masa,
Har zai fita tace, "mm, kai kuwa d'an wane gari ne don ALLAH"
"Ni?, Anan nake charanchi qauyen katsina"
"Anya mm, Aiko 'yan caranci baza suce basu iya bud'e mota ba, saidai ko kakumi ko?" ta qare zancen cike da zolaya tana dariya, dariyar yayi shima sannan yafita itama tafito ta kulle motar suka nufi cikin clininc d'in tare,
Suna kaiwa bakin qofar ya ja ya tsaya ta juyo had'e da cewa,
"Shigo man ka zauna anan reception bari nazo" tawuce kai tsaye office d'in consultant dr da aka tanada, ba'a jima ba tafito riqe da ledar magani har lokacin yana tsaye bakin qofa ya nad'e hannayensa a saman qirjinsa, yana ganinta yayi saurin sakin hannayen ta miqo masa leda tana fad'in,
"Au!
Wai dama baka nemi wajen
zaman ba tsaye kayi abinka?"
"Eh naga mutane sunyi yawa ne shiyasa"
"Kai kuma tsoronsu kakeyi ko?" Tafad'a cikin zolaya tare da wucewa abinta tamkar ba ita tayi maganar ba, bayanta yabi yana kallonta har ta tada motar ta juya tana qoqarin tafiya yayi kamar bai gani ba seda tayi masa horn sannan ya tako yazo ta gefen da zai shiga yayi tsaye, ganin yaqi shigowa yasa ta sauke glass d'in gefen nasa had'e da duqo kanta yanda zata ganshi tace,
"Muje ko mm?"
'Dan duqowar yayi shima tare da cewa
"A'a kitafi abunki ni sai naqarasa qasa"
"Haba!
Ai ba'ayi haka ba, indai baso kakeyi Jabir ya tatamun rashin mutunci ba, ai hannun ansa hannun mayarwa" taqare zancen tana bud'e masa marfin motar kamar d'azu, ba yanda ya iya dole ya bud'e ya shigo yana murmushi, tabbas Janan ta dace da rayuwarsa saboda yanayin halayyarta, akwaita da son barkwanci idan ta tashi duk da dai alamu sun nuna kamar tana yine saboda tsarguwar kanta da tayi akan abunda tayi masa, koma dai meye shi tayi masa haka kuma sai yaga abunda ya turewa buzu nad'i akanta.
Da wannan nan tunanin da yakeyi suka qaraso wajen sana'arsa ta sake rakasa har wajen tana fad'in,
"To malan Jabir, ga amininka nan na dawo maka dashi sai kuma gobe idan ALLAH ya kaimu, ALLAH yaqara sauqi"
"Amin ya rabbi, sai anjima mungode" Jabir ya bata amsa cikin d'an sakin fuska kad'an don shi har yanzu bata wani burgesa ba balle har yafidda ita sahun daya sakata, don ba'a yabon d'an kuturu sai ya shekara arba'in da yatsunsa.
"Mm, sai gobe ALLAH yaqara sauqi"
"Amin Janan, ngd sosai" yafad'a cikin sanyin murya yana kallonta, har taqarasa gaban motar ta bud'e ta shiga ta tayar idanuwansa na akanta saida yaji Jabir ya kece da dariya tukuna ya maido kallonsa akansa,
"Alqur'an Mm yarinyar nan na nema ta maida mana dakai wani tsohon maye, wai kaga yanda ka tsareta da idanuwa?, Tab kuma yasin ba qaramin kyau zakayi ba da zama mijin hajia ba"
"Mtsss..Kai fa d'an air ne Jabir, waya fad'a maka cewa har muyi aure ina nan a matsayin MAIDABINO, wuce nan guy" yaqare zancen yana cilla masa ledar maganin.
A b'angaren Janan kuwa tana kaiwa bakin gate d'in fita dr Ingaski na wajen zai fita, har zai taka wutar motarsa ya hangota ta madubi yayi saurin taka burki, wani irin ribas taja don kad'an ya rage ya bugi motarta da sauri itama ta taka nata birkin ta tsaya, murmushi yayi had'e da ficewa cike da takaici taja tata motar itama ta fice, tana fitowa taga har yayi parking d'in motarsa yana jiran fitowarta, tana kawowa saiti dashi ya maza ya fito tare da shan gabanta, wani wawan burki taja had'e da d'auke kanta gefe ganin yana tunkarota,
"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun" tafad'a cikin zuciyarta har ya qaraso wajen had'e da qwanqwasa mata glass d'in motar da take gefe, yi tayi kamar zata qyalesa can kuma ko me tatuna ta d'aure fuska tare da sauke glass d'in motar a hankali ba tare data kalli inda yake ba.
*Coment
*Like
*Share pls
*ALLAH KAJIQAN IYAYENMU
[8/17, 7:39 PM]
AR FARA KYAKKYAWA
: _Page 5_
*TUKUICIN SO*
*NA*
*BILLY S FARI*
*HASKE WRITTER'S ASS..
*Free Book*
_Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1228556252?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=mYrSfXopi0y3oPiu7GUqySjbsXBMVJX43kBOg04%2B5L0d0SbkVf0XnIXAWORHibq7vq5BIwk0Z%2FpKeoPXn9rPR8dsgzC65JLBGFgYtXScDzKTCbinX%2BGfHEnzWXNXigiJ_
*SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*
INA KUKE MAKARANTA??
INA KUKE MASOYA?
INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS???
KU MARMATSO
SABON SALON Namu NA DABAN NE, SABON TAKUN NAMU MAI KAYATARWA NE MAI FADAKARWA MAI ILIMANTARWA MAI GIGITARWA ABANGARAN SOYAYYA, ZAKU KOYI SALO DABAN DABAN DA ILIMI TA BANGARE DA DAMA, SOYAYYAH MAI GIGITA ZUCIYA MAI SAKA NUTSUWA....
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B
INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.
1- *KAUNA CE*
NA UMM ASGHAR
2- *RUKUQI*
NA FEEDHOM
3- *WANI SO*
NA ZEE YABOUR
4- *SO DA ALAKA*
NA UMMI AISHA
5- *MUGUN GANI*
NA SADIYA NASIR DAN
6- *ABDUL_HAMEED*
NA NANA DISO
7- *MUKULLIN ZUCIYA*
NA MAMAN KHADY
DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA
(1000) DUBU DAYA KACAL
KAI KA KAI....!