Sashe 76
Tukuicin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da mm ya isa auyen charanci arfe sha biyu na rana, mashin ya hau aka arasa shiga dashi can cikin auye don bada motarsa ya zo ba ta kasuwa ya shigo, tun daga wajen garin ya fara ganin sauye sauyen da auyen ya samu har zuwa bakin shigowa ciki, tsaida mai mashin in ya yi tare da sauka ya nufi wajen da har ya mutu bazai ta a manta shi ba, gaba ka an da wata bishiya daya riski mahaifiyarsa a wajen kafin ta rasu, wasu zafafan hawaye suka fara sauka a idanuwansa tuno yanda abubuwa suka faru a waccan ranar a kuma shekarun baya, kuka ya ri a yi sosai ha e da nemarwa mahaifiyarsa gafara da agaban idanuwansa ta mutu kafin ya mi e ya koma ya haye mashin in su nufi cikin auyen, tun da suka shiga ya fara hango yanda waccan ranar mutane ke gudu, manya da yara, mata da maza da kuma tsofaffi, ganin jiri na shirin ibarsa yasa yayi saurin dafe kai tare da runtse idanuwansa, anan ma gungun arayin ya hango yanda suka ri a tunkaro su a waccan ranar da sauri ya bu e idanuwa yana mai karanto duka addu'o'in daya sani a bakinsa sannan ya samu natsuwarsa ta dawo masa, kai tsaye gidansu yace mai mashin in ya nufa inda yayi ta yimasa kwatance, basu wani sha wahala ba don kusa yake da masallacin dake auyen suka iso, gidan na nan yanda yake na asa kamar yanda suka barshi, amma masallaci da sauran gidajen dake kusa dashi duk an canja gine-ginen su, ya ciro ari biyar ya mi awa mai mashin in yana arewa wajen kallo, canji ya mi o masa ari uku da hamsin ya ce ya auka duka ya bar masa, mutumen nata godiya, Har zai tafi mm ya dakatar dashi ha e da nuna gidan su da hannu ya ce, "Bawan ALLAH masu gidan nan nake tambaya" sai da mutumen ya walalo idanuwa kafin yace, "Wannan gidan, masu shi kake tambaya?" "Eh" "Tab, to nidai tun tashi na ban ta a ganin wani mahalu i a cikin sa ba, abunda kawai bazan manta ba shine, ance asalin gidan na yayan limamin masallacin nan ne, wanda arayi suka shigo a shekarun baya suka yiwa yankan rago" da sauri mm ya runtse idanuwa jin yanda kalmar ta daki zuciyarsa da yanda ya ga ma haifin nasa kwance cikin jini lokacin, yana jin mutumen ya ci gaba da cewa, "Banda wannan labarin bansan komai ba akan wannan gidan, kuma na tabbata babu masu shi yanzu inba aljanu ba" "To don ALLAH ina ne gidan limamin?" "Gashi can inda kaga bishiyar can, ba wani nisa ne da akwai ba balle na kaika" "To shikenan na gode" mm ya fa a tare da mi a masa hannu suka gaisa sannan ya nufi gidan, kasancewar arfe aya na rana ya kusan yi da kuma sauyawar lokaci saboda damana yasa ko daya isa ofar gidan ya tadda wani dattijo na arwala, sallama yayi masa ha e da mi a masa hannu suka gaisa bayan ya gama yana are masa kallo, tabbas bazai manta wannan fuskar ba, ko waye shi ya tabbata yana da ala a da mahaifinsa don yana arami yakan yawan ganesa a tare dashi, an samari yi magana lokaci na urewa masallaci nake son zuwa" tamkar wanda ya farka daga mafarki yayi firgigit ha e dayin ar gyaran murya ya ce, "Ammm, dama limamin masallacin nan nake nema shine aka nuno mun gidan nan akace nan ne gidan sa" "To..to..to ALLAH sarki, ai nine, Amma kafin nan auki ruwa ka gasu nan a buta kayi arwala sai mufara yin Sallah tukuna, daga ina halama an saurayi?" "Katsina baba" ya bashi amsa yana arin gano kamanninsa daya sani, "Ahh..kasha hanya, sannu dazu" "Nagode Baba" "Idan ka gama arwalar ka shigo ayi sallah sai mu zauna idan na dawo ko" "Eh." Ya bashi amsa ata aice tare da aukar bitar daya nuna masa ya fara arwala yana kallon yanda dattijon ke tokara sandar sa a hankali har ya isa masallacin, dama suna tsaye ladan yayi kiran Sallah, don haka dattijon na isa ya tada i ama aka tada sallah, da sauri ya arasa arwalar ya shiga masallacin aka daidaita sahu tare dashi.... _DON ALLAH DA GIRMANSA INA BARAN ADDU'O'IN KU GA MAHAIFINA DAKE CIKA SHEKARU UKU YAU DA RASUWA DAGA BAKUNAN KU MASU ALBARKA, UBANGIJI ALLAH YA RAHAMSHESA DA DUKKANIN MUSULMI DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA *ALLAH KA JI AN IYAYENMU [8/17, 7:45 PM] AR FARA KYAKKYAWA : _Page 45_ *TUKUICIN SO* *NA* *BILLY S FARI* *HASKE WRITTER'S ASS.. *Free Book* ********* *GODIYA MAI TARIN YAWA AGAREKU MASOYANA, NA GA ZALLAR KARAMCI DA TARIN AUNA DAGA WAJEN KU BISA ADDU'O'IN KU GA MAHAIFINA, NA GODE NA GODE SOSAI ALLAH YA SAKA MAKU DA MAFI OLOLUWAR ALKHAIRI YA KUMA JI AN NAKU IYAYEN WU AN DA SUKA RASU, WU AN DA BASU RASU BA KUMA ALLAH YA TSAWAITA MAKU RAYUWARSU CIKIN AMINCINSA YA TARAMU DUKA A ALJANNAH FIRDAUSI RANAR GOBE IYAMA, ONE LUV* ______________________________ Bayan sun kammala Sallah mutane duk sun gama fita dattijon ya juyo ya hango mm zaune ya aya hannayensa yana addu'a hawaye na saukar masa a fuska, da alama sai a sahu na ukku ya samu yin sallahr, an tsagaitawa ya yi har saida ya gama addu'ar sannan ya mi e tsaye ha e da jawo sandar sa ya nufo inda yake, mi ewa tsaye yayi shima yana arasowa ya mi a masa hannu sukayi musabiha sannan ya gaishesa cikin girmamawa, Hannunsa dattijon ya ja suka fita cikin masallacin zuwa gidan sa ya walawa ar autarsa Maryama kira ya ce ta kawo masu tabarma da ruwan sha anan soro anyi ba Bayan sun zauna ya bari har sai daya sha ruwa ya sauke ar ajiyar zuciyar gajiya dake tattare dashi sannan ya dubesa ha e cewa, "Bawan ALLAH ka ce daga katsina kake amma kuma baka yi mani bayanin ko kai waye ba da kuma abun daya kawo ka?" "Haka ne baffa" ya fa a tare da lan washe afafuwan sa yana fuskantar dattijon fuska da fuska tamkar mai shirin aukar karatu sannan ya ci gaba da cewa, "Da farko dai sunana Muhammad Muhriz, mahaifina kuma ana kiransa da malam Muhammad, manomine a wannan garin kuma yana sana'ar saida dabino da ashuwaki, na zo wannan garin ne neman dangin iyayena bayan ku utar da nayi a shekaru goma sha takwas da suka wuce sanadiyar shigowar da arayi sukayi a wannan auye suka kashemun mahaifi da mahaifiyata, guduwar da nayi ta ceton raina dana anwata mai suna Razina har wani bawan ALLAH ya taimake mu shine silar zamana Katsina, kuma shine dalilin daya sa na ce maka daga katsina nake" tun kafin ya rufe baki dattijon da hawaye suka cikawa idanuwa ya shiga walawa mutanen dake cikin gidan kira, "indo, Atika, Talatu Mariya...kuzo kuga abunda nake fa a maku koda yaushe, kuzo ga jinin an uwana Muhammadu ya dawo gareni, kuzo ku gasgata mafarkin da ako yaushe nake fa a maku inayi, ALLAH akbar ALLAH kai ne mai iko, kuma kai ne mai yin yanda ka so aduk lokacin da kake so" ya are zancen yana kuka ha e dayin sujudush shukar, mm kuwa a hankali ya runtse idanuwa wasu hawayen farinciki na saukar masa, tabbas yayi kuskuren rashin neman dangin iyayensa tuntuni, da wata il izuwa yanzu farincikinsa ya lunku fiye da yanda yake ji, Dattijon kuwa yana agowa daga sujada mm yaji ya rungumo sa ajikin sa yana fa "Taya akayi ka manta baffan ka haka Muhammad, taya ka kasa tunowa dani bacin kullum tare kake da mahaifin ka shi kuma tare yake dani" hannaye mm yasa shima ya rungume sa ha e da cewa, "Kayi ha uri baffa Ali, kallo aya nayi maka na tuna zuwan da mukeyi a wajenka ni da mahaifina, wayon ri e ko wane irin matsayi ne kake dashi awajensa kawai na kasa tunowa" "Za kace haka tunda kana can cikin birni hankali kwance, tashin hankalin daka barmu aciki kuwa ya kasa sa ka iya waiwayo mu" "Ba haka bane Abba, tunanina ne bai kawo hakan ba sai yanzu, amma daidai da rana aya auyen nan da duk mutanen dake cikinsa basu ta a fita a raina ba saboda nasan duka an uwana ne" "Haka ne, ALLAH yayi maka albarka, to ina ar uwar taka take ne?" "Bari nayi har sai na fara zuwa na gano an uwanmu tukuna daga baya sai na kawota ita" ago kai Baffa Ali yayi yana kallon an uwan nasa mata dake tsaitsaye fuskokin su auke da farinciki, ya ce "Indo kinga abunda nake fa a maki ko?, jikina na bani cewa duk inda jinin an uwana Muhammadu suke suna raye da yardar ALLAH, to gashi ALLAH ya bayyana mani akan da kansa" wacce ya kira da indo na matsar walla, ta ce "Na gani malam, ALLAH gagara misali ne huwar Rahmanu a lamurransa" mm ya an rissinar da kai asa ya shiga gaishesu aya bayan aya, murmushi indo tayi bayan sun amsa tare da matsowa ta shafa kansa tana cewa, "ALLAH mai iko sannu Muhammadu yanzu kai ne ka girma ka koma haka?" Daga shi har baffan murmushi sukayi kafin Baffa Alin ya sake juyawa gefen da sauran matan ke tsaye sun zubowa mm idanuwa suna kallon ikon ALLAH daya sake maido masu da an uwansu , ya ce "Mariya kin tuna jiyan nan nake fa a maki cewa nayi mafarkin ina tafiya nayi tuntu e, har zan fa uwa sai ga wani saurayi yayi saurin taro ni na fa a a jikinsa, ina agowa naga fuskarsa sak irin ta yana marigayi Muhammadu?, To kinga fassarar mafalkina, ashe da shi har anwar tasa suna raye ALLAH ya ku utar dasu kamar yanda itama mahaifiyar su ta ku uta" Wata irin razana mm yayi ha e da fisgo kai yana kallon Baffan nasa jin abunda ya fa a, cikin rawar baki da karyewar murya ya shiga fa "Um..m..mah...ummah nada rai bata mutu ba?" Ya are zancen cike da mamaki jikinsa na wani tsima tare da matsuwar jin amsar da Baffa zai sake basa, "Sosai Muhammadu, mahaifiyar ka bata mutu ba a wancan lokacin, yanzu dai ne ba muda tabbacin tana