Sashe 84
Tukuicin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wow I like her" dariya Mu'azzam yayi ha e da kallon sa ya ce, "Kama fidda bakinka malan, in ba haka ba ka ji kunya don indai Shahida ce to an ha u da an dace, itama in gwana ce ta bugawa ga jarida wajen surutu" "ALLAH?" "Hmmm, ai yanzun nan ne zata baka kunya in kafiye za ewa tsakaninsu, shiyasa nake ro on ALLAH yasa kar yaran nan idan sun girma su biyo ta da an banzar surutu, musamman ma Haisam da babu ruwansa" dariya mm ya kwashe da ita ganin yanda Shahida ta kwa e fuska ta madubi tana ballawa Mu'azzam harara jin abunda ya fa a ha e da cewa, "Tab..aikuwa kasan barewa baza tayi gudu an ta yayi rarrafe ba, ai kaima in ba abarka a baya ba indai wajen surutu ne" "Inaaa...ai ko ka an ban kamo afarta ba, parrot ma daya ganta sai da yayi saluting nata har kake wani ha a ni da ita" ya are zancen cikin zolaya yana yarenta ta madubi ha e da kashe mata ido, auke kai tayi tayi kamar bata ganesa ba shi kuwa mm ya ce, "Yanzu dai tsakanin ku ne ba ruwana a fiddani ciki, Madam sorry pls" Da haka suka arasa gida mai gadi ya bu e masu gate ya shige da motar ya yi parking, suna fitowa mm yayi saurin zagayowa ya mi a wa Momy dake arin fitowa hannu ta ri osa ha e da cewa, "Sannu Momy, kin gaji ko?" "Bari bari Muhriz, jin jiki na nake yi tamkar an bani kashi, kai gaskiya kuna ari ni irin wannan doguwar tafiya ba sonta nake yi ba" "Kai Momy, ni dake son arshen shekarar nan na kaiki hajji, idan kin dawo kuma mutafi umura tare" ya are zancen yana dariya ganin yanda take takawa a hankali ri e da hannunsa saboda yanda afafuwan keyi mata tsami, "Indai hajji ce zan daure naje, amma umura na yafe bazan iya ba", ta are zancen da dukkanin gaskiya dake fitowa daga asan zuciyar ta, Sai da suka fara watso ruwa suka ranka sallolin dake kansu sannan suka zauna cin abinci, duk da ba irin abincin Hausawa bane sun ci sosai don ba laifi yayi masu da i, hakan kuwa ba aramin farantawa Shahida rai yayi ba saboda tana son mutum mai sakin jiki da kuma rashin nuna mata yama, wanda mafiya lokutta hausawan mu haka suke ga ire iren yare da basu sani ba, Bayan sun kammala mm ya kalli Mu'azzam dake latsar waya ya ce, "Wai ina yaran nawa suke ne?" "Oh!, wai Haisam da aisa?, shi yana wajen lesson ita kuma Inaga bacci takeyi" "No wander, shiyasa banji ilbasar su ba tun da muka iso" "Ai kuwa, haddai aisa uwar rigima, da yanzu ka ji kukan ta ya fi a irga" Kallon agogon dake aure a tsintsiyar hannunsa mm ya yi ha e da cewa, "Think lokacin Sallah ya yi fa" "Oh, haka ne fa, tashi muje daga nan sai mu biya mu auko Haisam" "Wai dama ba anan cikin gida ake lesson in ba?" "Eh acan gidan uncle in Madam ne ake yimasu shida annen ta" Daga haka mm bai sake cewa komai ba ya yi gaba shi kuma ya bisa a baya bayan ya walawa Shahida kira dake can zaune tana kwasar fira ita da Razina Momy na aka baki itama jefi jefi ya ce ta an ha a masu abu marar nauyi kafin su dawo sannan ya fice, sai da ta koma ta sanarwa dasu Momy lokacin sallar magrib yayi sannan ta wuce akin ta itama, kasancewar su Momy nada arwalla sai kawai suka tashi suka yi sallar su sannan suka fito falo suka zauna, daidai lokacin aisa da bata wuce shekaru uku ba ta taso bacci tana murzar idanuwa, tana kawowa falon ta saki idanuwa tana kallon ba in fuskar dake ci, hannu Janan ta mi a mata ha e da cewa, "Come.." kafin ta rufe baki ta ja baya ha e da walawa Shahida dake zaune tana addu'a kira, "Mahmah" Shahida ta fito da sauri don ta zata wani abun ne sai kawai taga aisa ta uya a bayan ta tana nuna mata inda su Janan ke zaune, ajiyar zuciya tayi tare da jawo ta ta nufo wajensu da ita tana fa "Come aisa, ki gaishe ku kin ji ta" Dariya Razina tayi ha e da cewa, "Ba haka zaki ce ba, ki gaishu su, kin ji ko" "Ok , to ki gaisheta kin ji ko" "Gaishe su zaki ce" ta sake gyara mata tana dariya, cike da osawa koyon yanda zata fa in ta ce, "Oh my God, aisa greet them, they are your momys" ta are zancen tare da orata akan jikin Momy, da sauri ta zille tana ma e kafa a ha e da cewa "No momm.. she's an old woman, i don't want her to be my mom" Dariya duk suka saka cike da jin kunya shahida taji tamkar ta nitse a asa, hannu ta aga da niyar dukan ta Momy ta ce, "Noo...allow her mana, she's a small girl abi" kallonta Razina tayi har lokacin bata dena dariya ba kafin tace, "So, what up me, do you like me?" "Yeah i like you" ta fa a ha e da zuwa jikinta ta fa a, dariya Momy tayi ha e da kallon Shahida ta ce, "You see!, this are the kind of children we have now, they already know their parents since before they where born, thank God i hv my own by my side, ku ri e naku in ri e nawa" "A'ah Momy kar kice haka, kika sani ko aisa ce zata kaiki Saudiya" "Ta makaro ai yarona ya riga daya rigata, taje can na yafe ta biyawa iyayen ta" yanda Momy ke tsokanar aisa in da wasa ana dariya har tana ri afar ta tana janyewa ba aramin burge Shahida yayi ba, sai taji ina ma ace anan take zaune tare dasu, da family in nata sunfi kowa zama cikin farin ciki akoda yaushe. ewa tayi ta shiga kitchen ta barsu nan falo zaune bayan ta kunna masu tv, an farfeaun kayan ciki daya sha vegitables ta shiga ha a masu kamar yanda maigidan nata ya ce tayi, bayan ta arasa ta shiga ciki tayo wanka ta saka atamfarta mai kyau itama ta fito falon ta zauna ri e da an kwalin a hannu tana arin aurawa amma ta kasa, ajiye aisa Razina tayi dake jikinta akan kujera ha e da mi a hannu tana cewa Shahida, "lemme help you aunty" ba musu ta mi a mata an kwalin ta yimata auri mai kyau ha e da fikkar da jelar gashin nata a gefe sannan ta an ja an kwalin kadan a baya yanda goshin zai an fita tana fa "Wow! aunty you look more beautiful" "I know my sister, shiyasa ina son kayanta nan naku" "Not kayanta nan naku, kayan nan naku" "Ok , kayan nan naku" Shahida tafa a tana dariya, suna zaune su mm suka dawo tare da Haisam da shekarunsa zasu kai biyar zuwa shidda haka, cike da natsuwa ya araso cikin falon ya fara gaida mom in sa sannan ya gaida su Momy da Razina yana binsu da kallo, "Haisam, do you know them" Mu'azzam dake ri e da makullin mota yana arin zaunawa kusa da Shahida ya fa a yana kallonsa, "No dad" ya bashi amsa tare da ago kai ya kalli mm sannan ya sake maida kallonsa ga Razina dake zaune, ya ce "But dad she's looking a like with uncle Muhriz" "Yes, sibling in sa ce, wannan kuma mom in su" ya bashi amsa da Hausa don sosai yake son su iya yaren nasa, murmushi Haisam yayi yana kallon Momy tare da sake gaisheta ta mi a masa hannu ta ce yaje kusa da ita ya zauna, ba musu kuwa ya je ya zauna ta shiga tambayarsa ya karatu, bayan ya amsa masa ta ago kai tana kallon mm ha e da cewa, "To da alama shi wannan maigidan nawa yana auren, su o'oh dai ne ba yarda" mm na dariya ya ce, "To Momy banda abunki wake yarda da kishiya in ba dole ba, ai da gaskiyar aisa ara tayi ta kanta ko little in uncle" ya are zancen tare da lakutar chick in ta yana yimata wasa, "To ai shikenan, sai taje can ta arasa" Mu'azzam kuwa tuni ya shafa'a da kallon Razina dake auke da aisa, sai yaga har wata kama takeyi da ita musamman da yaji wani yanayi akanta cikin zuciyar sa, kallon da yakeyi mata ya sata tsarguwa ta mi e tare da ajiye aisa ta nufi kitchen inda taga Shahida tayi, saida ta shige sannan ya kauda kansa yana murmushi ha e da kallon mm ya ce, "Friend na gani fa ina so?" Harara mm ya balla masa ha e da cewa, "Bakada aiki gaskiya, to an rigaka" "Are you serious?" "Yes upcouse" mm ya bashi amsa tare da ficewa falon don kar ya allo tmasa ruwa, a can wajen wani an corridor ya nuf a dake auke da kujeru ya zauna tare da ciro wayar sa ya rubuta dadda an message tare da fatar nasara a jarabawa ya turawa Janan da mtn line in sa da bazai nuna inda yake ba tunda shi every where you go ne, yana gama turawa Mu'azzam ya iso wajen ri e da bowl guda biyu da ferfesun kayan cikin da Shahida ta gama ha a masu ya mi a masa aya sannan ya nemi kujerar dake kusa dashi ya zauna shima, suna ci suna an ta a hira inda nan ya tabbatarwa da mm shida da gaske yakeyi yana son Razina, ba tare da mm ya oye masa komai ba ya sanar dashi ala ar dake tsakaninta da Jabir wacce har ankai ga maganar aure, ya ara masa da cewa yanzu haka ma dalilin shigowarsa tare dasu lefenta da nasa zasu ha awa, ya kuma bashi ha uri sosai don ko ba don haka ba baya tunanin zai iya amincewa ya auri Razina duk da ya cancanci fiye da haka a wurinsa saboda karamci da mutuncin sa, ba don komai ba sai bazai jurewa yayi nesa da ita ba har hakan,