← Book details Tukuicin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 120

Sashe 4

Tukuicin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Meyasa bakuce yataimaka maku ba kuka barshi ya ajiyeku"
"Madam, Ina tsoron kada ya cutar damu nida qanwata, shiyasa yana yin parking na b'alla marfin motar nagudo"
"No boyyyy...bakyau haka da kayi, wanda ya taimakeku acikin daji har kuka zo nan baiyi maku komai ba bazaya cutar daku ba, infact kayi kuskure wataqil ma zuciyarsa me kyau ce zai taimaka maku daka tsaya"
"Madam! kitaimaka mana zanyi maki duk aikin da kike so narantse"
"Shikenan, tunda kayarda dani zan taimakeku kafin hankali ya kwanta kaji ko, ya sunanka"
"Muhammad Muhriz, qanwata kuma Razina" ya qarasa fad'a cike da farinciki tare da ajiye Razina qasa yana qoqarin karb'a qatuwar kular dake hannunta, dariya tayi da saida haqoranta suka baiyana had'e da cewa,
"Noo.. kabarshi kaji ko?, d'auki qanwarka kaga dare ya somayi kada taje tahau kan titi, bara na taro napep sai muje gida, nasan yarona ya dawo yana can yana jira"
Tana rufe baki napep na tsayawa tace, "Yawwa thank God, kagama mun huta, kuzo ku shiga"
Gefe ya ajiye Razina ya kama mata suka shigar da kayan cikin napep suka had'e kujeru da benci n da take d'ora abincin akai suka rufe da qaton buhu (tanhol) suka saka duwatsu suka daddanne sannan ya d'auki Razina suka shiga mai napep ya ja sukabar wajen tana lakutar chicks d'in Razina data kama ta maqalqale Muhriz saboda quiya tamkar wacce za'a raba dashi,
Kyakkyawan gidane madaidaici da bazaka tab'a cewa wacce ke cikinsa sana'ar abinci takeyi ba saboda har d'an madaidaicin gate ne d'auke dashi, suna tsayawa aguje yaronta da kad'an Muhriz zai girmesa ya rugo yana yimata oyoyo tare da rungumeta, jawosa tayi ajiki tana shafa kansa,
"Oyoyo my one and only son, how was the school"
"Fine mom" ya fad'a yana sake shigewa jikinta tare da bin Muhriz da Razina da kallo,
"Mom where do you find this beautifuls?" Ya tambaya tare da d'ago kai yana kallon momynsa, dariya tayi had'e da ciro d'ari uku a jikkarta ta miqawa mai napep d'in daya gama sauke kayan,
"Muriz come in side" don haka take kiran sunan nasa, wannan karon dai bai fahimci me take cewa ba shiyasa har ta kusa shigewa baibi bayanta ba har saida yaron nata daya bisu da kallo yace,
"Kashiga ciki tace" shi kuma yafara qoqarin kwasar kayan kamar yanda ya saba akoda yaushe ba tare daya sake cewa komai ba, ajiye Razina Muhriz yai ya taimaka masa suka d'auki kayan tare suka shiga dasu ciki Razina na biye dasu abaya.

Baki Muhriz ya saki yana qarewa gidan kallo saboda kyansa duk da bawai wani tsaruwa sosai yayi ba amma daidai gwargwado rufin asiri babu abunda zaka nema aciki karasa sai abunda ba'a rasa ba,
Saida suka gama kwashe kayan kaf lokacin harta watso ruwa ta dawo falo ta zauna tana qirgar kud'ad'en data samu na cinakin da tayi yau tana so ta fitar da riba da uwa ta bawa wacce ke tayata aiki taje ta siyo sauran abubuwan da babu na abincin gobe,
"Momy!

Who are those people pls" yaron ya sake tambayarta akaro na biyu, ajiye kud'in tayi tare da kallon gefen da yake tace,
"Ha'a!

Jabeer, what's wrong with you, bazaka bari na fara hutawa bane?

Go and bring my food kaji ko"
"Yes Momy, am Sorry" ya fad'a kamar zaiyi kuka yana tangalar kai sannan yawuce kitchen, yayinda shi kuwa Muhriz yayi zaune qasan kujera yana fama da Razina data haye saman kujerar tana tsalle tsalle data sauko,
"Kabarta Muriz, kazo ka shiga ciki Jabir zai gwada maka toilet kayi arwala kuje kuyi SALLAH"
Daidai lokacin Jabir yakawo m
ata abinci ya ajiye agabanta yana kumbura fuska irin na shagwab'ab'b'in yaran nan dake samun kulawar uwa d'ari bisa d'ari, murmushi tayi ba tare data bi takansa ba tace,
"Thank you darling, je ka kaisa toilet yayo arwala kaima kayi kuje masallaci kuyi sallah"
Razina na ganin ya tashi sun shiga wani d'aki ta sauko kan kujerar tabi bayansa tana kuka, har madam zata kai spoon d'in abinci abakinta ta ajiye taje ta d'aukota,
"Sorry Razi..bari su dawo wajen sallah ko" taqare maganar tana kaimata spoon d'in abincin abaki, qin karb'a tayi sai qoqarin zillewa takeyi daga jikinta tana kallon qofar d'akin da suka shiga, basu jima ba da shiga ba sai gashi yafito da sauri jikinsa jiqe da ruwa alamun yayo arwalar ya nufo wajen da sauri yana goge hannayensa ga riga zai karb'eta don jin kukan nata yakeyi har cikin qoqon ransa,
"Kaje mana kayi Sallah, ko zaka fasa ne don tana kuka?, Jeka mana zatayi shiru.."
Madam bata rufe baki ba Razina ta kwatsa wani irin kukan ganin ya juya zaibar wajen, runtse idanuwansa yayi tare da bin bayan Jabir daya fito da sauri suka wuce masallaci, ita kuma Razina madam ta shiga rarrashinta, da taga taqiyin shiru sai kawai taje ta kunna mata tv ta saka mata catoon, da farko qin ko kallon wajen tayi har saida taji sautin qarar maganar catoon d'in da madam ta qara murya, a hankali ta juyo tana kallo, kan kace me tayi shiru sai dai ajiyar zuciya, Saida madam taga hankalinta ya d'auku sosai sannan ta ajiyeta, bata koma bi takan abincinta ba sedai tawuce d'akinta itama tayo arwala ta d'auko carpet d'in sallar ta ajiye kusa ga Razina ta kabbarta itama tayi sallar,
Ba qaramin dad'i yaji ba lokacin da suka dawo ya riski qanwar tasa tayi shiru har tana kallo tana tafi da hannuwa ga kuma madam agefenta tana sallah, sai yaji wata irin qaunar matar marar misaltuwa ta dirar masa azuciya.

Da daddare bayan sunci abinci sun gama madam ta zauna ta shiga tambayar Muhriz labarinsa dana iyayensa da 'yan uwansa, bai b'oye mata komai ba yasanar da ita har zuwa kan yanda 'yan bindiga suka shiga qauyen nasu yau suka karkashe mutane da yanda ya riski gawar iyayen nasu waje daban daban, yaqare tare da fashewa da kuka mai tab'a zuciya, ba madam kad'ai ba hatta yaronta jabir kuka yakeyi, sun matuqar tausayawa Muhriz shida 'yar uwarsa Razina tare da alwashin d'aukarsu 'yan uwan da zasu zame masu jigo suma su zame masu jigo na rayuwa,
Duk da qarancin shekarun Muhriz hakan be hana momyn Jabir zaunawa ta bashi labarin rayuwarta tun daga farkon asalinta dana iyayenta ba har zuwa lokacin data had'u da mahaifin Jabir, Wanda shine silar faruwar qaddarar dake kanta, asalinta Krista ce 'yar asalin enugu, mahaifin Jabir Jamal shiya musuluntar da ita sanadiyar soyayyar dake tsakaninsu ya kuma aureta yazo da ita anan garin katsina mahaifarsa, ko kad'an iyayensa basuji dad'in aurenta da yayi ba amma da yake babu yanda zasuyi tunda yanada halinsa dole suka haqura, bayan aurensu da shekara uku ALLAH yayi masa rasuwa, lokacin Jabir nada shekara biyu aduniya, nan fa 'yan uwan mahaifin Jabir suka tasota gaba da hantara da tsangwama ita da yaronta, wannan dalilin yasata guduwa takoma wajen iyayenta, da yake suma riqaqqin kafuraine masu mugun riqo sai sukace lalle inbata dawoma addininsu ba to tabbas babuta babu su, da taqi amincewa da haka sai suka koreta suma, babu yanda ta iya dole ta dawo nan katsina agidan mijinta, kasancewar mafiya yawansu masu arziqine yasa babu wanda ya damu da tadata daga gidan musamman ganin tanada d'a sai dai suka ja mata kunne akan matuqar tana son su ta zauna lafiya agarin tofa babusu babu ta, kada ta sake ta nuna ta sansu, dama can ita ba yarensu bace ba kuma addininsu ba, d'an uwansu ne yayi karanbanin kawota cikinsu kuma tunda yarasu shikenan babu wata sauran alaqa ko sanayya tsakankaninsu, tayi kuka sosai tayi baqincikin faruwar hakan amma da yake kyakkyawan Imani tayi saita amshi qaddararta da hannu biyu kuma ta tashi tsaye wajen neman na kanta da kuma kula da d'anta da tarbiyarsa, don tasan duk da tarin arziqin da suke dashi bazasu tab'a iya taimakawa yaronta ba daidai dana kwana d'aya, mahaifin Jabir nada wani mashin roba roba, wannan mashin d'in shi yazamo rufin asirinta tun daga lokacin har zuwa yanzu, don kuwa kud'in data siyar dashine ta fara sana'ar abinci dasu kuma sai ALLAH yasa mata albarka aciki, Sam babu ruwanta da kowa inba mutunci ya had'aku da ita ba sannan bata tab'a zuwa roqo wajen kowa ba haka kuma daidai da rana d'aya bata tab'a bari yaronta ya alaqantu da sana'arta ba balle har ta hanasa cikar burin data d'ora akansa na zamowa mai dogaro da kansa shima, tunda ya shekara uku aduniya ta sakashi makaranta both ta boko data arabi, kullum zataje wajen sana'arta shi kuma ta turasa makaranta, gwargwado tayi tsaye tsayin daka wajen bashi tarbiya iya qarfinta tare da nuna masa tsantsar soyayyarsa dake cikin ranta, wacce bako shakka tah'adu biyu ne hadda wacce takeyiwa mahaifinsa,
Duk da tarin gargadin da 'yan uwan mahaifin Jabir sukayi mata akan zuwa wajensu hakan bai hana lokacin daya shekara goma ba ta d'aukesa ta zazzagaya wajensu dashi, saidai bata tab'a sheda masa cewasune dangin mahaifinsa ba gudun kada ya tashi da tsanarsu azuciya saboda ire-iren wulaqancin da sukeyi mata aduk lokacin da suka je wajensu, duk da kasancewar Jabir baisan matsayinsu awajensu ba sai yaji sam baya sonsu ya tsanesu, a tunaninsa suna walaqntasu ne saboda sunada kud'i da tarin arziqi.
Chapter 4 · 0% Book details