Sashe 2
Tukuicin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaro idanuwa Jabir dake tsaye yana kallonsa yayi had'e da dukan kafad'arsa cikin jin haushi da takaicinsa ya ce,
"Wai meye haka kakeyi Muhriz?, Janan ce fa ba wata ba?, Look!
alqur'an ko katashi muje mu kwashe kayan can ko nayi tafiyata kaji na fad'a maka, don wannan iskancin daka d'au hanya ni bazan juri kallonsa ba"
"ALLAH Janan ce Jabir?"
"A'a ba ita bace kai ne"
"Oh my God!, Kasan me kuwa?"
"Bana son ji malan, kawai katashi mutafi kaji ko, anya ma kaine kuwa?
Kaga yanda ka wani qura mata idanuwa sai kace wani sabon maye?, Sai kace ba Muhriz d'in dana sani ba mai shegen nuqufarci da miskilanci ga 'yan mata!"
"Bari kawai Jabir, wlh nima ji na nakeyi tamkar bani bane yau, ji nake tamkar an sauyani daga asalin MM d'in daka sani akan Janan, wani irin yanayi na dinga ji da ban tab'a jiba akan wata 'ya mace lokacin data matso kusa dani na fizgata, gaba d'aya yanda kurar qarfe haka na dinga ji wani abu na fizgata zuwa gareta, shin me hakan ke nufi Jabir?" Jabir daya saki baki yana kallonsa cike da mamaki ya ce,
"Hakan na nufin tabbas kasamu tab'in hankali Muhriz, wannan kad'ewar da tayi maka yasa kasamu sauyin tunani da manta kowaye kai da matsayin da kake dashi a makarantar nan, shin ko ka manta kai bakowa bane sai mai tallan dabino da batasan asalinka ba?, Ita kuma 'yar masu kud'ice dake ji da kanta ko ka manta alwashin daka d'auka?"
"Ban manta ba Jabir, amma koma meye naji son Janan a zuciyata"
"Tab!
To ina shawartar ka da kayi gaggawar anfani da d'an sauran hankalin daya rage maka kafin ya ida gushewa ka tashi mubar wajen nan, kamanta da ita domin kuwa duk kanwar jaa ce babu kafi balle na d'ara, kana kallon idanuwanta zakasan biri zaiyi kama da mutum, in kuwa kace ba haka ba to Zan sakar maka gatari, amma kasani ita d'in bata dace da mafarkinka ba, ni kaga tafiyata kafin d'alibbai sufito sufara fahimtar alqiblarmu, amma dai kayi tunani akai"
Jabir ya qarasa fad'ar hakan yana nuna gefen kansa da yatsa,
"Sam baka fahimta ba Jabir, a gaskiya bana Janan tazama cikin bara gurbin dana tsana, kuma ni zuciyata tariga data kamu da sonta daga kallo d'aya"
Cak Jabir ya tsaya daga tafiyar da yakeyi kafin can ya juyo cike da mamaki yace,
"Me kace MM?, Mai maita banji kaba sosai, kardai ace zargin da zuciyata keyi kake son tabbatarmun?
Noooo...am not supporting that, Janan bata dace dakai ba, idan zaka farka ka farka kawai kazo mukwashe wudancan kayan ko kuma natafi nabarsu a markanesu akan titin can kamar yanda aka tashi markaneka"
Miqewa MM yayi cike da kuzari ya kakkab'e jikinsa tare da nufo wajen Jabir yad'an daki gefen kafad'arsa yana dariya,
"Comoon...sonta nakeyi fa nace ko tun yanzu zaka soma takun saqa da uwar d'akin taka ne?"
"Wa?...
ALLAH ka tsari gatari da sarar masai, ai ko kai baka isa kazamo uban gidana ba balle ita, kawai ina tsoratar maka shan duka ne tunda kai raggo ne, amma tunda kace kana iya had'a gatari bari na sakar maka b'ota, idan gyad'a taji wuta da kanta zatayi d'wad'o, kad'ai san ita ko 'yar gidan waye da kuma abunda mahaifinta zai iya yimaka idan kaje masa a irin wannan siffar"
Seda ya dafa kafad'ar Jabir had'e da d'an sosa gefen kunnensa tukuna ya ce,
"Eh, ai cewa nayi ina sonta bawai nace zan fad'i mata ina sonta ba ko?, Ina son na auna halin Janan dana sauran mata tunda har zuciyata ta zab'eta, ban damu da kowaye mahaifinta ba da kuma mezai iya yimun, kawai nagartarta da qarfin mutuntakarta nake buqata, matuqar nasamesu awajenta a wannan yanayin data sanni, tofa shikenan haqata ta cimma ruwa"
"Shikenan, munga bugun lamba, bara musa idanuwa muga yanda film d'in zai kaya, badai girin girin ba tayi mai"
'Daure fuska MM yayi tare da bud'e sauran ruwan dake cikin gorar ruwan ya watsa masa a fuska yana fad'in,
"Kaifa d'an iska ne Jabir, bakinka baya fad'ar abu mai kyau, in sha ALLAH wannan zatayi mai har kuzo kuriqa lasa"
Jabir dake dariya ya ce "ALLAH!"
"Zaka gani ne"
"To ai shikenan, nidai don ALLAH da girmansa kab'oye wannan son azuciyarka kuma kayiwa bakinka takunkumi wajen aikata kuskuren fad'arsa awajenta kamar yanda tsala-tsalan 'yan matan dake bibiyarka keyi har sai kaga kamun bakin ludayin daga wajenta, inba haka ba kuwa, tofa ka fad'a ruwan dafa kanka da kanka"
"Angama matsoracin wofi, ka kwantar da hankalinka ai dole zanyi yanda kace tunda nasan ko waye mahaifinta duk da dai alamu sun nuna ita d'in ba halinsu d'aya ba"
"Aifa, ni nasan tunda karoga ka saka alaqar zuci tsakaninku babu yanda za'ayi ka iya fahimtar duk wani aibinta yanzu, don haka ga filinan ga mai doki"
"Ashe ko zaku sha sukuwa malan Jabir" ya amsa masa a miskilance yana murmushi tamkar bashi bane suka gama shaqiyanci dashi yanzu,
Da haka suka je suka tattara dabinon da kwakwar suka kwashe waje d'aya suka saka cikin buhu, Jabir yakira aka sake kawo masu wasu suka koma gefe inda suka saba zama sukaci gaba da sana'arsu kafin d'alibbai sufara fitowa daga wajen lectures.
_*WAYE MUHAMMAD MUHRIZ MAIDABINO?*_
*ALLAH KAJIQAN IYAYENMU
[8/17, 7:39 PM]
AR FARA KYAKKYAWA
: _Page 2_
*TUKUICIN SO*
*NA*
*BILLY S FARI*
*HASKE WRITTER'S ASS..
_Wattpad@Billyfari9https://www.wattpad.com/1224710693?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=BTK2Vk0LL5HyZ7f8z6t5hJUXU2zgmsDfqOwA%2FHYKAXZqR35cPk3tmBsZcsQgSabPg%2F2ma3NiPJiyOw%2F8vbI%2FiCkTNduJzX1kysyIKbnFxScFE5Gu%2BWEUvIGcsAyRE3my_
*M* uhammad Muhriz, kyakkawan matashine kuma saurayi maiji da kansa da bazai haura shekaru 32 ba aduniya, hamshaqin mai kud'ine d'an kasuwa kuma d'an boko da yayi fice acikin garin na katsina, inda yafi bada qarfi ga kasuwanci gida da wajen qasar nan, iyayensa sun rasu tun yanada shekara goma sha biyar aduniya shi da qanwarsa Razina alokacin ita kuma tanada shekaru biyu kacal, sun rasu sanadiyar fashin da b'arayi suka kaimasu awani qauye da ake kira charanchi acan cikin jahar katsina, inda suka karkashe duka mazajen dake qauyen da kuma wasu matan da suka saka taurin kai wajen yunqurin tafiya da sukayi dasu, wanda alokacin mahaifiyar su Muhriz da Razina na mai suna Bilkisu na cikinsu, yayinda shi kuma mahaifinsa suka kashesa bayan d'auki ba dad'in da sukayi dashi wajen ceton rayuwarsa data iyalinsa da yayi, shi kansa Muhriz saida suka tafi dashi amma ALLAH
yabashi ikon guduwa ya dawo ba tare da sun ganesa ba, koda yadawo gida ya tadda qanwarsa Razina a tsakar gidansu zaune cikin rana tanata faman kuka, da sauri yaje ya d'aukota had'e da fad'awa cikin d'akin mahaifinsa, inda ya taddasa kwance cikin jini anyi masa yankan rago, saurin saka tafin hannunsa yayi ya kwantar da kan Razina dake faman kuka a saman kafad'arsa ya durqushe agaban gawar ta mahaifin nasa ya saka wani irin kuka mai cike da ban tausayi wanda bayada mai rarrashinsa alokacin aduniya, babu babban tashin hankalinsa irin yanda kukan Razina ke ratsa kwakwalwarsa had'e da huda masa zuciya, yayi kuka irin kukan dake tabbatar da rashin gata da maraici da kuma hauhawar nauyi ga wanda keyinsa, yayi mintuna talatin awajen yana abu d'aya kafin yamiqe rungume da Razina data kasayin shiru har yanzu tamkar wacce tasan masifa da quncin da suka fad'a na rayuwa a yanzu, qarar bindigar daya jiyoce tasashi saurin fitowa daga gidan aguje cikin firgici da tashin hankali, yayinda itama ta sake fashewa da wani kukan,
Ba tare daya san inda zai nufa ba yakama hanya domin neman ceton rayuwarsa da kuma ta qanwarsa, yana kaiwa bakin qofar fita qauyen yayi tuntub'e da wata gawa ya kife ya fad'i qasa dashi har Razina, yunqurawar da yayi yamiqe idanuwansa suka sauka kan gawar, tsananin tashin hankalin da yake ciki ko kad'an baiyi tasiri ba wajen mantawa da fuskar mahaifiyarsu, ko shakka babu ita d'in ce, shed'arsa ce tafara kaida komo tana neman kucce masa saboda firgicin daya sake shiga na ganin gawar jigo kuma ginshiqin rayuwarsu akaro na biyu agabansa, cikin sheshshekar kuka ya samu damar furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihirrajiun da qarfi ya fad'a ajikin gawar ba tare daya damu da mutanen dake fitowa cikin qauyen aguje suna wucewa ba wasu har suna takinsu, rarrafowa Razina tayi wajen itama ta haye gawar mahaifiyar tasu gaba d'aya tana kuka ganin d'an uwan nata awajen, tamkar dai yanda suka kashe mahaifinshi itama sun kasheta tahanyar dab'a mata wuqa aciki, amma da yake rai mai alfarma ne bata ida qarasa mutuwa ba tana jin sautin kukan
daya tabbatar mata na yaranta ne ta farfad'o tare da jan wata irin shed'a dake nuni da ran be ida fita ba da sauri ya d'aga daga jikinta yana fad'in,
"Inna kada ki mutu, ki tashi Inna ga Razina na kuka, don ALLAH kada kimutu inna kibarmu kamar yanda baffanmu ya mutu ya barmu" yaqare zancen tare da jawo Razina daketa tsala kuka ya kara mata a fuska, riqo hannunsa tayi dake fuskarsa yana qoqarin goge hawaye ta sake zagaye jikin Razina dashi ma'ana ta d'ora saman wanda ya rungume Razina, cikin qarfin hali ta d'ago hannu tasa afuskarsa ta goge masa hawayen dake kwance akai tace,
"Ku gudu sannan ka kula da qanwarka Muhriz..." Kafin tarufe baki hannunta dake saman fuskarsa ya fad'i qasa alamun rai yayi halinsa, nan take Muhriz yaji tamkar ana rura masa wata irin wuta acikin jinin dake yawo a jikinsa, duk wani tsoro, tashin hankali da kuma fargaba sai yaji ya gushe masa, gaba d'aya yaji zuciyarsa ta bushe ta yanda zai iya fuskantar kowane irin qalubalen rayuwa a halin yanzu, hannu yasa ya shafe idanuwan mahaifiyarsu da suka kakkafe tare da d'aukar Razina dake kuka yasa hannu ya goge mata hawaye yana fad'in.