Sashe 3
Tukuicin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ya Isa haka Razina, kidena kuka ya zame mana dole mu fuskanci qaddararmu, a halin yanzu mune zamu tunkareta bazamu koma bari ta riskemu ba" Yana gama fad'ar hakan ya nufi hanyar komawa cikin qauyen babu tsoro ko misqala zarratin a zuciyarsa, acewarsa zai rayu acikinsa koda shi kad'aine da qanwarsa babu inda zasu je,
Yana kaiwa a tsakiyar gari yaji muryar mahaifiyarsa nadawo masa akunnuwa, "ku gudu Muhriz sannan ka kula da qanwarka..."
kallon Razina data fara bacci yayi sannan ya maida kallonsa ga gungun b'arayin dake tunkarosu zasu ficewa daga cikin garin suna ihu da shewa suna qarawa, sai kawai ya tsinci kansa da rugawa ya fad'a can wani dajin badon ya tsorata ba sai don kawai yacika wasiyar mahaifiyarsa akan qanwarsa, amma badon wannan ba a yanda yake jin zuciyarsa zai iyayin fito na fito dasu saidai su kashesa. (Hmmm Muhriz kenan, ai tunda manyanka da jami'an tsaro, gwamnati suka kasa da lamarin wud'an nan b'arayin kaima bazaka iya ba sedai kawai akai qararsu ga ALLAH shine zai iya yimana maganinsu, amma sam qarfin zuciya ko na jiki ko makamai bazai iya da lamurransu ba sai qarfin addua kawai)
Gudu yayi sosai da bai tsinci kansa ako ina ba sai tsakiyar titi, tsabar gajiya baya iya yin komai gashi riqe da Razina wacce ga dukkan alamu babu fitar lumfashi ajikinta, da sauri wani mai motar haya ya fito daga qauyen qanqara daya tashi kadesu ya faka gefen titi, kasancewar marece yayi babu motoci da yawa yasa har ya d'aukikkesu daga kan titin babu abunda ya samesu, tambayar Muhriz yakeyi lafiya daga ina suke amma ya kasa bashi amsa sai nuna masa Razina yakeyi dake riqe a hannunsa gam, cikin tsoro mutumen ya dubi gefe da gefen titi da kuma hanyar daya hango sun fito yaga ba kowa ya d'aukesu su duka ya saka cikin motar sannan yaja sukabar wajen, dama garin katsina yayi sai kawai ya nufi can dasu, hannu Muhriz ya miqa ya jawo 'yar jarkar swan daya hango acan gefen driven da ruwa, mutumen be hanasa ba ya bud'e gorar ya tuttud'awa Razina a fuska da jiki, tafi mintuna biyu kafin can yaga taja shed'arta da qarfe ta maido had'e da fashewa da kuka alamun suma ne tayi ta farfad'o, murmushin qarfin hali yayi hawaye na zubo masa sannan ya d'auketa ya bata ruwan tasha sosai sannan ya qarasa shanye sauran shima had'e da fad'awa jikin kujerar motar yana fidda lumfashi d'aya bayan d'aya, duk wannan abun da Muhriz keyi drivern na kallonsa ta gefen idanuwa amma bai ce dashi komai ba har saida sukayi nisa sosai sannan yayi gyaran murya had'e da juyowa yana kallonsa yace dashi me yake faruwa da sune ya gansa cikin wannan halin kuma d'auke da 'yar qanqanuwar yarinya?, Banda kallonsa babu abunda Muhriz keyi har suka iso cikin garin katsina ba tare daya ce masa komai ba balle yasa ran zai samu ya bashi amsar tambayar da yayi masa, waje ya samu yayi parking agefe sannan ya juyo da niyar sake yimasa wata tambayar akaro na biyu sai kawai yaga ya bud'e marfin motar ya fice aguje d'auke da qanwar tasa, sosai abun ya bawa mutumen mamaki da sauri ya bud'e marfin motarsa amma sai kawai yaja motarsa yayi gaba, dama yana tunanin ina zai kaisu?
Gida ko wajen hukumar 'yan sanda tunda yayi tambayarsa meya faru dasu yaqi magana, gashi ga dukkan alamu wani tashin hankali suka yoma gudu don alamu sun nuna haka.
PLS *COMMENT*
*SHARE*
*LIKE*
*ALLAH KAJIQAN IYAYENMU
[8/17, 7:39 PM]
AR FARA KYAKKYAWA
: _Page 3_
*TUKUICIN SO*
*NA*
*BILLY S FARI*
*HASKE WRITTER'S ASS..
*Free Book*
Wattpad@Billysfari9 https://www.wattpad.com/1224710693?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=BTK2Vk0LL5HyZ7f8z6t5hJUXU2zgmsDfqOwA%2FHYKAXZqR35cPk3tmBsZcsQgSabPg%2F2ma3NiPJiyOw%2F8vbI%2FiCkTNduJzX1kysyIKbnFxScFE5Gu%2BWEUvIGcsAyRE3my_
*G* udu yakeyi sosai d'auke da Razina ba tare da yasan dalilinsa nayin hakan ba har saida yakai bakin wani shago inda wata mata ke saida abinci, cikin muryar dake nuna tsantsar gajiya da yunwar dake tare dashi yace, "Don Allah hajia ki taimakamun da abinci na bawa qanwata" juyowa matar dake miqawa wani saurayin abincin dake cikin takeaway ansa cikin baqar leda daya siya tayi had'e da cewa,
"Kawo kudi.." da yake ba bahausa bace amma taji hausa sosai, goge zufan dake tsiyayo masa afuska yayi tare da guntayen hawayen da suka zubo a idanuwansa sannan yace,
"Banida kud'i, kitaimaka mani don ALLAH..." Bai qarasa rufe baki ba wani saurayi da take qoqarin miqawa abinci yana miqo mata kud'i yasa hannu ya turasa gefe suka fad'i qasa Yana fad'in,
"Kai gafara can, ku bazaku tashi kuje ku nemi na kanku ba iyayenku duk sunbi sun kashe maku zuciya da bara da roqo..." Bai rufe baki ba shima matar ta karb'e abincinta daya siya tamiqa masa yanzu had'e da turesa shima sannan ta watsa masa kud'insa data karb'a a fuska taje ta duqa kusa da Muhriz dake qoqarin d'ago Razina dake kuka yana kakkab'e mata jiki ta miqa masa,
"Sorry, kiyi hakuri kinji?
Ina Mama naki take?" tana shafa kansa tare da goge masa gefen fuska, cike da rashin damuwa da halin da yake ciki ya karb'e abincin ya bud'e, lafiyayyar shinkafa da miya ne hadda naman kaza da salad ya ture naman agefe ya shiga yamutse abincin yana d'iba yana bawa Razina abaki ba tare daya damu da bawa matar amsar tambayar da tayi masa ba balle har ya godewa abunda tayi masu, ganin haka yasa tamiqe tsaye tana jifar saurayin da yayi tsaye bud'e da baki da harara, shafa kansa yayi tare da cewa "sorry madam" Yana sake miqo mata kud'in don tabashi abincin, kamar jiransa takeyi ta balbalesa da masifa ta inda take shiga ba nan take fita ba har saida mutane suka taru wajen, fad'a takeyi masa sosai akan abunda yayi tare da illar yin hakan wanda sai a sannan hankalin mutanen ya koma gasu Muhriz dake qasa zauna yana Ida qarasa sauran abincin da Razina ta rage, don kuwa taci sosai saboda ba qaramar yunwa take jiba, ga abincin saye dama shima bawani afkine dashi ba, kallo d'aya zaka yimasu kafahimci suna buqatar taimako saboda yanda suke awani hargitse, nan mutane suka taso masa suma da matar ta fad'a masu abunda ke faruwa suna fad'in be kyauta ba, daga qarshe kuma ta buga kai ga qasa tace bazata sayar masa da abincinta ba koda shikadai be customer daya rage mata aduniya, yayi magiyar duniya amma ta hanasa dole ya haqura yabar wajen cike da nadamar abunda yayi kafin sauran mutanen dake wajen suma sufara watsewa,
Ledar ruwa qwaya d'aya ta d'auko ta miqawa Muhriz ganin sun gama cin abincin yasa hannu biyu ya karb'a tare dayi mata godiya murmushi ta sakar masa tana yaba kyawon da ALLAH yayi masa shida 'yar uwarsa, har lokacin fuskarta cunkushe ba walwala saboda abunda saurayin nan yayi masu, babu abunda ta tsana aduniya irin taga ana walaqanta mabuqaci musamman yara duk da irin tarin tuhuma da laifin iyayensu da take gani idan ta ganesu cikin wannan yanayin, shiyasa a kullum batada buri irin taga ta gina yaronta qwaya d'aya da ALLAH ya bata aduniya ta kuma tsaya masa yasamu ingantacciyar rayuwar da bazai lalace mata ba, tana wannan tunanin Muhriz ya d'auki qanwarsa suka koma can gefe yana yimata wasa tana dariya, dama shi yaro matsalarsa lokacin da yake cikin damuwa amma data kau zaka gansa tamkar ma baisan meya faru ba ko halin da ake ciki, to haka ta kasance ga Razina sab'anin shi Muhriz da babu abunda ke zuciyarsa a yanzu kamar ina suka nufa idan dare yayi?
Ina zasu je?
Shine abunda kawai keyi masa kaida kawo a qwaqwalwa da kuma zuciya,
Har aka kira sallar magrib suna awajen, su basu tafi ba su basu tsaya waje d'aya ba, in yayi nan da ita aguje tana dariya yabita can da gudu sunata wasarsu, can dubara ta fad'o masa ganin matar tafara har had'a kayanta alamun ta tashi, da sauri ya kamo Razina data ruga tayi bakin titi ya d'aukota ya nufo wajen matar.
"Madam" ya fad'a kamar yanda yaji wancan saurayin ya fad'a d'azu, d'an juyo da kanta tayi jin sautin muryarsa kafin ta juyo da jikinta duka gaba d'aya tana d'an sakin fuskarta daga yanda take d'azu,
"What little boy?" Kasancewar acan qauyensu ya fara zuwa makaranta don har yakai aji d'aya na matakin secondary yasa ya fahimci me take cewa, dama can yana d'an ji kad'an kad'an mayarwar ce dai bazai iya ba,
"Don ALLAH kitaimakeni ni da qanwata, bamuda kowa nan garin an kashe mana iyaye"
Wani kallo tayi masa mai d'auke da alamomin tambaya barkatai tana nazartar cikin idanuwansa kafin tace,
"Daga ina kika zo"
"A can qauyen charanci" shiru tayi kamar mai wani nazari saiga sautin qarar redio daga wani shago dake kusa da nata na tashin labarai cewa 'yan bindiga sunkai hare hare a yankin qauyukkan dake cikin jahar da suka had'a da charanci, qanqara da kuma kakumi, inda sukayi garkuwa da qananan yara da mata kuma suka karkashe mutane masu yawan gaske, cikin damuwa ta sake tambayarsa jin abunda ke faruwa,
"To waye ya kawoku nan little boy"
"Wani drivern mota ne ya taimaka mana lokacin da muka fito daga qauyenmu"
"To ina drivern yanzu?