Sashe 85
Tukuicin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
haka kuma yana jin nauyin Shahida don ta auke sa da mutunci kuma tana girmamawa da mutunta sa, saboda haka ba anwarsa ba ko wata ya ji abokin nasa zai auro mata to sai inda arfin sa ya are wajen hanasa aikata hakan balle ace shi da kansa zai auki anwarsa ya aurar da ita ga mijin ta, Duk da Mu'azzam yaji ba da i ya fahimci abokin nasa sosai tare da yimata fatan alkhairi, ya kuma yi al awarin binne wannan zancen acikin zuciyar sa har abada, bayan kwana biyu mm ya bawa Momy ku e masu matu ar yawa tare da MasterCard in sa da zasuyi sayayyar kayan lefen kafin ya dawo don yau zai wuce Dubai, ya kuma ro i Mu'azzam da yaba Shahida dama ta rakasu a siyo duk abunda ya kamata kafin ya dawo nan da kwanaki uku, don washe garin ranar daya dawo zasu koma Nigeria, sai da suka fara zuwa tare suka siyo akwatunan da za'a saka kayan ya za awa Janan best colours in daya san tana so sannan ya wuce, da daddare Mu'azzam ya sake sa suka shirya suka fita tare ya kaisu campaning wani abokinsa na cosmetic suka fara siyo kayan shafe shafe da turarukka da sauran abubuwan da suka shafi angaren, wanda Momy bata san yanda akayi ba saidai taga sun dawo gida ba tare da ta biya kudin ba, suna isa gida kuma motar campaning na isa da kayayyakin da suka siyo, data yi masa zancen ku in sai ya ce ta barsu ya riga daya biya komai tayi ta saka masa albarka, haka ya ri a fita dasu kullum tare da Shahida ana sissiyo abubuwan har aka gama, wanda kusan kaso talatin bisa ari cikin ku in kayan duk shine ya biya, ko da mm ya dawo ya yi matu ar mamakin ganin yawan kayayyakin da aka siya, don a tsammanin sa da yar idan ku in daya bayar zasu isa shiyasa ya ha awa Momy da MasterCard in sa, sai gashi yaga ko ku in daya bata a hannu basu ida are wa ba balle ayi tunanin ciro wasu cikin account in sa, wani irin nauyi ne ya kamasa lokacin da Momy ta fa a masa cewa gaba aya cosmetic in da aka siyo da turarukka Mu'azzam ya biya ku in haka ma akwai wasu abubuwa da dama aciki da shine ya biya ku en su, shiru yayi yana mamakin karamci irin nasa wanda ba tun yau ya saba yima shi ba, arin samunsa yayi masa godiya yayi amma aduk lokacin daya bu e baki zai yi magana sai hanasa, bai samu damar yin hakan ba sai washe gari da suka rakkosu zuwa airport zasu wuce, ya mi a masa hannu sukayi musabaha ha e da ri e hannun nasa sosai ya ce, "Thank you so much friend, indeed..." Mu'azzam yayi saurin dakatar dashi ta hanyar cewa, "Enough Muhriz, what a friends mean, kai dai sai mun iso buki in sha ALLAH" "Ba damuwa, kai ne mutum na farko kuwa da zan fara sanarwa" "Da dai yafi maka, don wannan karon duk ka gwadamin wariyar launin fata tofa zamu gartaya dakai" "Hakan bazai faru ba in sha ALLAH" "To yayi, ka gaida Madam Janan, kafa a mata cewa i solute her da tayi arin fitar mana dakai a jerin tazurai, don ni har nazata bakada lafiya sai mun garzaya dakai asibiti" ya are maganar cike da sha iyanci yana dariya, dariyar shima mm yayi tare da bashi hannu suka tafe ya ce, "Ka shirya kuwa a cikin wata tara cif zan tabbatar maka da cewa ni in lafiyayyen ne, kai badon jinjiri an wata bakwai ba lafiyayyen bane to da nace acikin wata bakwai zan baku babynku a hannun ku don na tabbatar maku da cewa lafiya ta garau" ya fa a yana wani jinjina jikinsa suka sake tafewa suna dariya, Shahida kuwa har da wallanta don ba aramar sha uwa sukayi da Razina ba, acikin an kwanaki biyar in nan da sukayi ta koya mata abubuwa da yawa da suka shafi makeup irin wacce akayi anan Nigeria da kalolin aurin an kwali da dai sauran su, haka itama Razina ta koyi kalolin yanda ake sarrafa abinci irin na kasar shina da kalolin abincin da muke dasu anan gida kuma suyi da i sosai, infact dukkanin su sun sha u da juna ga aisa itama sai faman kuka takeyi ganin Razina zata tafi, har ta an yi nisa sai kuma ta juyo da gudu tana share hawaye ta kar asa dake hannun Shahida tana faman zillo ta auke ta, kiss tayi mata a kiss ha e da cewa, "Zanyi kewarki my little, stop carrying kinji ko" ta sa hannu tana goge mata hawaye, daidai lokacin Mu'azzam ya araso wajen ya mi a mata hannu ya kar aisa tare da cewa, "To amarya maza jeki ki tafi ke suke jira, ashe ba ni ka ai zanyi kewar anwar nan tawa ba har da family nawa, how i wish Zaki ci gaba da kasancewa a tare damu har abada" sinne kai tayi asa tare da shafa kan Haisam daya rungume afafuwanta, ba tare da ta ce komai ba ta juya tana goge hawaye tabar wajen, cikin aga murya Mu'azzam ya ce, "Ki gaidai angonki Jabir da yayi mani rigage, kice nace shudin mai sa a ne kuma ina taya shi murna" ya are zancen tare da rungumo Shahida a jikinsa ya sakar mata kiss a forhead, Mm dake can tsaye a bakin jirgi ya zuba hannayensa a cikin aljihu yana hangosu yayi murmushi tare da neman tsari akan duk abunda zaisa ya zamo silar rushewar farin cikin abokin nasa da kuma matarsa, Razina na shiga shima mm ya shiga aka rufe ofar don dama su ka ai ake jira, da sauri ya ara sa can wajen tu in ya samu har abokan tu in nasa Erik da James sun fara daidaita komai shi ka ai suke jira a tashi, cikin mintuna ya gama saita na angaren sa shima sannan jirgin ya fara tafiya a hankali kafin daga bisani kuma ya tashi sama, Mu'azzam na ganin sun tashi ya ara janyo Shahida ajikin ya yiwa aisa kiss a kunci sannan ya juya suka nufi wajen motar su suka wuce gida. ***. ***. ***. angaren Janan kuwa kwanaki shidda suka rage masu su kammala jarabawa, kallo aya zaka yimata ka fahimci ba ka an ta bawa karatun muhimmanci ba saboda cikakken lokacin kanta ma bata da shi yanzu, sallah da kuma wanka kadai ke tada ita idan tana karatu amma hatta abincin wani lokaci tana ci tana karatu ne, duk da tarin soyayyar da take yiwa mm ta danne ta maida hankali wajen karatun ta sosai saboda shima ya fa a mata cewa zai rage damunta a waya saboda ta samu isasshen lokacin da zata maida hankali ga karatun ta, shiyasa duk kwanakin nan da yayi tafiya ba tare daya samu kiranta akai akai ba sai dai message bata wani damu ba tunda dama yariga daya fa a mata, Yau ma kusan zaune ta kwana tana karatu don exam biyu suke da ita gobe, aya practical ce da rana zasu yi misalin arfe sha biyu, ayar kuma sai zuwa arfe hu u zasu rubuta ta, kasancewar bata son tayi latti yasa arfe sha aya na bugawa ta auki motar ta ta wuce school gabanta na fa uwa, gashi duk jikin nata baya yimata da i amma sai ta ta'alla a abun da rashin samun isasshen baccin da bata yi bane daren jiya, Tana fita ko awa ba'a yi ba motocin ambassador Hussain Salim kusan waya bakwai suka iso gidan nasu, dama tuni Abban yasan da zancen zuwan nasu na kawo kayon auren Janan kamar yanda ya tsara ya kuma yi order duka abunda zasu ci su sha a hotel don kar ma kowa yasan da zancen har sai sun iso, suna isowa ya kira hotel in ya ce akawo masa order in da yayi sannan ya fita wajen tarbon su, manyan mata ne hamsha an masu ji da nera ko wace taci ta oshi, kana yi masu kallo aya zaka san hutu da jin da i ya zauna ajikinsu su bakwai, sai ambassador Hussain Salim da kansa da kuma Asgar.