← Book details Tukuicin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 120

Sashe 71

Tukuicin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ko daya dawo gida baibi takan kowa ba ya shige
akin su ya nemi gado ya haye, kafin kace me tuni bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi,
angaren Janan kuwa bata koma gidan ba sai bayan sallar isha, tafe take cikin mota tana waya da masoyin nata har ta
araso gida tayi parking ta fito ciki tare da mi
a hannu ta
auki jikkarta sannan tasa makulli ta rufe ta nufi cikin gidan, tana kaiwa tsakiyar falo taji muryar mahaifin nata ya ce,
"A ina kika fito?" Cikin kaishi murayar dake nuna mai ita babu walwala a tattare dashi, mm ba tare data kashe wayar ba ta jefata a jikka ha
e da kallon mahaifin nata ta ce,
"Abba barka da dawowa, yaushe ka dawo ne" a tsawace ya ce,
"Answer my question from where are you?"
"Daga gidan Hajiya kaka" ta bashi amsa tana tare da sunkuyar da kanta
asa,
"Me kika je yi acan" cike da mamaki ta
ago kai ta kallesa jin tambayar data sake fitowa daga bakinsa kafin tace,
"Na je gaida ta ne"
"Kint je gaida ta ko kunje ha
uwa da wannan
an iskan yaron?"
Jin tayi shiru bata bashi amsa ba ya sashi ka
a kai yabar wajen ranshi na suya da sululi, kenan abunda su Jazz suka fa
a masa gaskiya ne, dole ya
auki
waran mataki cikin gaggawa kafin komai ya lalace masa,
Ita kuwa ajiyar zuciya ta sauke tare da
ago kai tana kallon gun daya bari sannan ta juya ta nufi upstairs
in, Nihal ta hango tsaye ta na
e hannayenta akan
irji tana kallon meke faruwa, da
an sauri sauri ta shiga hawa upstairs
in har takai inda take,
"Sannu Adda Nihal" ta fa
a ka
ai tare da
aga mata hannu ta shige
akinta, bayanta Nihal tabi tare da tsayawa bakin
ofa tana
are mata kallo, Janan data soma kwa
e kayan jikinta ta juyo ta kalleta ta
auke kai,
"Adda lafiya?"
"Lafiya lau Janan, ina kika je ne yau?"
"Gidan grandma"
"Shine baki fa
a mun ba muka je tare"
"Naga kina bacci ne, be side ba lallene kije ba kona fa
a maki, shiyasa banyi hakan ba"
"To ya akayi kika
aga wayata dana kira"
"Sorry ban lura ba ina can ina fira nida mm" takai zancen tare da excusing kanta ta nufi toilet don tawatsa ruwa,
"Wait Janan..."
"Please....am so tired Adda, bara na watso ruwa zan sauko
asa sai muyi magana"
"Ok" ta fa
a ha
e da juyawa tabar
akin cike da takaicin mm a ranta, gaba
aya yasa
ar uwarta sauya mata daga Janan
in data sani zuwa wata daban, badon shine farincikin ta
a da tasa anyi masa tsakani da ita, yayansa ko kan hanya ya ganta bazai kalleta ba,
Janan kuwa na fitowa wajen wanka ta ciro wayar ta daga cikin jikka takira mm, bugu
aya ya
aga don dama cike yake da tunanin meya faru ta dena magana
azu bacin kiran bai tsinke ba,
"Yalla
ai afuwan, na iso gida ne
azu Abba ke tambayata daga ina nake shine fa na tsaya bashi amsa ba tare dana kashe ba"
"Ok, ya dawo kenan?"
"Eh, na taddashi agida"
"Masha ALLAH, to yanzu meye labari?"
"Yana hannunka hubbin ruh"
Haka suka ci gaba da firarsu ta soyayya hankali kwance, dama tayi taking dinner
in ta a gidan grandma hakan yasa bata damu da sauka
asan ba, haka Nihal tayita zuba idanuwan ganinta har ta gaji bata sauko ba kamar yanda ta ce
in, sosai abun ya
onawa Nihal rai amma duk da haka saita danne saboda tana son Janan tadena yimata shariyar data tsiri yimata yanzu,
Saida ta watso ruwa ta saka kayanta na bacci sannan ta kashe wutar
akinta ta jawo
ofar ta nufi
akin Janan, har lokacin suna la
e da juna ita da mm suna waya, tana kallonta ta shigo ta haye kan gadon nata ta kwanta taaare da jan duvet ta rufa dashi fuskarta na kallon p.o.p
in saman
akin, kasancewar Nihal ta saba'in hakan wani lokacin ya sa bata bi ta kanta ba taci gaba da wayarta, saida taga anyi wasu mintuna talatin basu
ara wayar ba sannan ta ce,
"Janany sister magana nake son yi dake"
"Ok bani Adda bani mint
una biyar" karaf taji mm ya kar
e da,
"A'a, jeki kuyi maganar ku saida safe, nima na gaji bacci nake ji" ya fa
i hakan saboda yaji sautin muryar Nihal lokacin da take magana, ko bacin haka shima yanada bu
atar kwantawa ya huta don gobe sakko zasuyi zuwa
asar dubai, yasan ko idan bai kwanta dawuri ba tofa bazai tashi dawuri ba, badon Janan taso ba ta ce,
"Shikenan saida safe"
"Ok bye, ki kula mani da kanki"
"Zanyi hakan, kaima kayi mafarkina"
"Love you, nightttt.."
"Love you too hubbin ruh" ta fa
a cike da nisha
i sannan ta katse kiran,
"Sorry Adda, gani meke faruwa ne?" Ta juyo tare da
ora kanta a saman kafa
ar ta, "hmm Janan kenan!, Meyasa kika sauya mun kwana biyun nan?"
"Kece kika fara sauyamun Adda, shiyasa na biki ayanda kike so"
"To danayi maki me?"
"Abubuwa da dama mana"
"Kar kiyi
arya domin baki saba yimun ba, asali ma batayi maki kyau"
"Haka ne Adda, fisabilillahi yanda kike reacting akan mm bayayi mun da
i gaskiya, haka ma Aunty zee, kiyi rayuwarki a yanda kike so bazani hanaki ba, amma maganar gaskiya son kai da wula
anci duka basa da da
i, Aunty zee mahaifiya take agaremu ko muso ko kar mu so, wajibi ne agaremu mubata girmanta da ALLAH ya bata koda ace mun girmeta, balle gaba
aya tayi
a damu, yanda kike kalamai marasa da
i da rashin girmamawa agunta shiyasa nakeyi maki haka saboda kiji idan akwai da
i kuma..."
"Pls ya isa haka, naji wannan sai me kuma?"
"Bana son kina fa
a e maganganu akan wanda nake fata kuma nake mafarkin ya zamo mijina, gaskiya hakan baya yimun da
i shiyasa nafita shirginki"
"Ina akan wannan na baki ha
uri ko?, Kuma wai me kika
okesa ne da zaki nemi ba
anta mun akansa, kenan haka zai rabamu idan kika auresa?, haka zaisa ki gujeni bayan kinsan duk duniya banida wata wacce ta fiki?, Wlh ALLAH hakan ya fara sakani tsoron ki auresa don na tabbata rabamu zaiyi" ta
are zancen tare da saka kuka bil ha
i har cikin zuciyar ta,
an matsowa Janan tayi kusa da ita tare da cewa, "am so sorry, kiyi ha
uri in Sha ALLAH na dena, sannan kidena tunanin mm zai rabani dake, wlh bazai ta
a yin hakan ba na tabbata, ki gyara kurakuranki ni kuma nayi maki al
awarin canzawa daga sauyin da nayi"
"Kin tabbata?"
"Sosai kuwa, kefa second mom
ina ce, taya zanyi maki al
awarin
arya" murmushi tayi tare da rungumota ta ce,
"Ina matu
ar sonki Janany sister don ALLAH kidena biyewa masu son rabani dake kin ji
ar uwata?,
ar dariya Janan tayi kafin tace, "babu fa mai iya rabani dake na fa
a maki, don haka kidena wannan tunanin, nima ina son ki sosai"
Nan fa suka shiga wata sabuwar fira cike da son junan su kafin bacci mai matu
ar da
i yayi awon gaba dasu, mm kuwa yana kwantawa wayarsa ta shiga ruri, da har bazai
auka ba sai kuma ya mi
a hannu ya
auki wayar daya saka a caji yana tunanin ko Janan ce, ganin lamba ya sashi sakin tsaki tare da kashe wayar gaba
aya bayan ta katse sannan ya koma ya kwanta,
Turo baki Amira dake kwance tayi bayan ta sake kiran wayar a karo na biyu ance kashe take, gidan tura sa
o ta shiga tare da rubuta masa message kamar haka, _Mm wlh Inaga baka san meye cutar so ba, amma ina ri
on ALLAH ya saka maka ita, musamman tawa, tayanda bazaka ta
a samun sukunin da kwanciyar hankali ba har sai kaji muryata sau takwas a rana, kaga fuskata sau bakwai a sati, sannan ka
uduri mallakata lokaci
aya, ina son ka, ina son ka ya Muhriz na_ ta tura alamar kiss
da kuma heart
sannan ta tura masa tare da rungume wayar, a haka itama bacci mai nauyi ya zo ya yi awon gaba da ita.
Chapter 71 · 0% Book details