← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 139

Sashe 98

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

🐎ZEEE MAKAWA🐎
✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
7⃣7⃣
B Y
🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,

Assalamu Alaikum yan uwa musulumai,
Dan Allah a tsakanin marubuta da makaranta yakamata asamu kyakyawan facin ta,
Bawai challenge's ya shigo ciki ba, idan har marubuci tayi wani abin da yadan kauce wa addini ko tarbiyan mu yakamata akirata in prevent aimata gyara ,
Babu wanda yawuce gyara aduniya, tundai na fannin addin mu,
Yima marubuci cin fuska a bainin jama,a baida amfani wlh,
Wanan rubutun da kuja ga munayi abune mukaddari daga Allah, akwai masu so soyi amma Allah bai basu ikon yi ba,
Bakaramin wahala ke cikin rubutun novel ba yan uwa,
Yakamata duk yadda marubuciya tai novel din ta a gode mata, indan har da gyara akira mutun a gefe not in public aimai gyara,
Pls mukuma marubutan Allah yakara bamu hakkuri a tsakanin mu mukara daurewa da makarantar , duk abinda kayi ba aima korafi akai ba, wanan abin baida ma,ana ne ,,,,,
Idan nafadi ba daidai ba ina mai rokon gafaran ku yan uwana,👏👏👏👏

Kitchen din shiru yake babu kowa acikin shi sakamakon kashe na,urar da zata sada ma kitchen din da ruwa,
Hakan yasa ma,aikatan fita waje don ganin ko may ye matsallar ,
Maman Umar abin ya bata mamaki kasancewa ko a daren jiya itace tayi aikin karshe a kitchen din kuma ruwan yana zuwa normal,
A hankali ta fito daga dakinta tana tafiya cikin sanda har ta shiga kitchen din,
Saida ta leka ta tabbatar da ba kowa a waje lokacin ta ciro wani dan koya daga cikin gefen breast din ta ta jefa a cikin flower sinasir da maman Umar ta kwaba ,
Tafito da sauri tana dan waige waige, bayanta,
Tana shiga dakin ta tashige bayi ta wanke hannuwan ta tsab, takoma saman godon ta kamar wacce bata tashi daga barci ba,
Bayan angyara matsalar ruwan maman Umar ta dawo taci gaba da aikin ta,
Tanagamawa ta jera komai a carpet saura kuma masu ci a table aka kai masu nasu, saman tebur,,
Saida kowa kusan ya hallara a falon wurin karin kumallon safe,
Kusan nice ta karshen zama a falon saidai ba a saman kujera na nufa ba,
Wurin Ummi na nufa don a saman carpet, take zama ,
A hankali na dan durkusa gami da kara gaida Ummi karo na biyu,
Saida na sawa plate dina komai da nake sha,awa, nadan tsiyaya ruwan sha, a cup na aje a gefe na,
Nai bissimillah nadauka zankai wa bakina,
Aziza dake zaune daga gefen mu ta kura min ido, Allah Allah take yi in kai a bakina,
Daidai lokacin da zan kai a bakina sai wayana dake gefe yadauki ruri
Mayar da sanasir din nayi cikin plate na, nai saurin daukar wayan , diba massage din,
Ganin nobar Amal, da nayi yasa ni saurin ta shi kusa da Ummi ,
Kada kici abincin nan fadima ,
Kuma in kin karanta kada ki dago kai ki debe ni pls,
Gashi dai nagama karantawa amma sai na kasa daga kaina sama,
Wani irin mugun tsoro ne yakamani saboda nasan cewa Amal bata maganan banza
Maimaikon in juya sai na mike kawai daga, gurin da niyar tashi ,
Muryan Ummi ce na ji tace min fadima da wo mana kici abincin cikin sanyin murya nake ce mata,
Ummi zan dauko ma salimat takarda ne a daki, yanzu zan dawo, sai kuma wani dabara yafado min nace ma ummi bari ma dai intafi da abincin daki na kawai sai inci a can,
Wani wawan ajiyar zuciya Aziza tayi,jinda tayi cewa zantafi dakina in ci,
Mutun biyu ne Allah yanufa suci sanasir din, dayake suna da rabon wahala,,
Da Salim sai Ummi duk yadda Amal taso ta hana Ummu ci acikin hikima hakan baiyi, ba,
Ciwon ciki ne mai karfi ya turnike su sai ,
Tun ana abu wasa wasa har takai ga anyi rushing din su asibiti,
Nan likita yai masu dan bayani akan cewa akwai abinda sukaci Allah nai yatai make su sun kawo su asibiti da wuri,
Yace amma inda mace mai cikine taci gaskiya da abin yafi nan worse,
Jin hakan yasa hankali kowa tashi kowa da abinda yake tunane acikin zuciyar shi gamay da abinda likita yace,
Kwanan su biyu , a asibitin aka sallamo su zuwa gida,
Har a lokacin Amal batace min komai gamay da text din da tayo min ba,
Hakan dai danaga irin wahalar da su ummi suka sha yasani shan jinin jiki na sosai,
Sai yakasan ce duk gidan hankali na a tashe yake so sai,
Gurin Salimat na tafi da kukana nafada mata duk yadda mu kayi da Amal,
Itama dai shawara tabani sosai akan yadda zan zauna da kowa agidan
Tace min akwai abinda Amal take zargi a gamay da ni,
Hakan yasa tunda ga wanan ranan Salimat ce ke kawo min abinci a boye ko kuma intafi gidan ta ince a can,
Yau bazan tafi school ba don haka na koma nadan kwanta don in huta,
A can cikin barci na rika jin kamar ana tabani sama sama,
Sai kuma na dinga jin kamar ana kiran suna na a hankali,
Cikin karfin hali na bude idanu na a hankali, tayadda ba kowa zai iya gane cewa na bude ido na ba,
Aziza ce tsaye da wani abu kamar jan kyale a hannun ta,
Can kasan gadona naga ta duka ta aje kyalen a hankali kuma ta taso ,
Ta kama hanyar kofar dakin fita zuwa waje,
Ido kawai nabita dashi a hankali har ta kure min
Bakina duk adduan da na sani na tsari saida nayi shi a lokacin wani ba ni ko karasa shi nake daukar wani,
Sai da na tabatar ta wuce tundazu sai na sauko da bissimillah tare da naiman tsari ga Allah ,
Ta gefe gudan nabi ban yarda na bi ta inda nagantaba tsaye,
Bayi na fada da wayana nakira Salimat na sheda mata abinda nagani,
Ba,adauki wani lokaci ba ta shigo gidan da shirinta,
Ita da Amal ne suka dauke wanan jan kyalen suka samo wani jan kyale na rigar Amal irinshi suka aje mata agurin,
Mamaki duk ya kashe mu, Salimat ce tafara magana daga cikin mu,
Tace wai may yasa wanan matar batada imanine haka,
Mundade muna shawara a tsakanin mu so sai,
A ranan ga dare ya raba amma sam babu alamar barci a ido na,
Duk da nasan cewa sun fitar da mugun abin a dakina
Tunane nayi ko may yasa sheriff yin tafiya tun ranan da yadawo batare da yadauki ma aziza wani mataki ba ,
Ajiyar zuciya na saukar cikin tausayawa kaina ina tuna nen wanan sabon rayuwa da na tsinci kaina a cikin sa,
Gaba sai bugawa yakeyi saboda alamar gitawa da naga anayi ta dan hasken da ke hasko min ta jikin window daki na,
Na rintse idona ina ci gaba da addua acikin raina,
Saboda na sadakar da raina cewa nawaya kare kawai a wanan ranan,
Can kuma sai naji shiru nadaina jin motsin komai kuma naga a daina wanan gittawan da ake ta min,
Duk da nasan cewa na rufe dakina yau da makulli, amma hakan bai hanani jin tsoro ba,
A haka barci barawo yazo yadan yi awon gaba dani,
Sai da asuba nafarka cikin dan firgita don ji nayi kamar za a shigo min ,
Saida na kwanatar da hankalina sannan na gane cewa ai ba komai har yanzu,
Saida na tabbatar da cewa gari ya waye kuma tabbasa kowa yadan fara fitowa waje
Natashi naje nai wanka nafito kenan ina shiri naji alamar ana buga min kofan daki da karfi kamar za,a tsaga shi biyu,
Na nufi kofan pa gigice nabude a hankali, hannu na guda yana rike da dan towel din da nake tsane jiki na da shi,,
Ga mamakina Aziza ce tsaye tana ganin na bude daki naga tai wani irin shock na nuna alamar mamaki,
Kallonta nakeyi sosai babu kaukautawa,na zuba mata ido, nima,
Ganin da nayi cewa , kallon nata bana girma da arziki bane,
Kallon tababiya naimata na kallo ta wani irin shekeke,
Na juyawa nayi da zumar in koma cikin dakina,
Sai naji ta turo kofar ita ma da karfi kamar zata bangaje ni,
Turus na tsaya gami da rasa na yi hannuna, yana rawa, ina kallon ta don inga abida zatayi,
Cikin tsayin wani lokaci shiru ya biyo baya sai dai na kula da ita kamar tana kokarin kallona tana na,zarin wani abu,
Nadai daure da nagaji da kallon kallon da mukeyi na ce mata lafiya dai ko hjy,
Cikin dakewa ta ce min da akayi may fa,
Cikin rawar murya nace mata, naga kamar kina bukatar wani abune a nan,
Ta buga min wata uwar harara ta kuta saida gabana yai mugun faduwa da ga ni irin yadda tai min,,
Tawani irin juya da karfi kamar mai fada da iska tawuce,
Nanta bar ni tsaye da mamakinta,
Gakuma wani irin tsoro da firgicinta da ya kamani
Don nasan cewa a yadda taimin yanzunan zata iya aiwatar da komai akaina,
Inda tawuce tabarni nan nake tsugune amma tsabar fargaba abinda take shirin yi min yasa ni zarya a corridor
Ina ta tunanen mai yasa Aziza take farautana haka saboda kawai na auri mijin ta ne ko ko may,
Da sauri namike na isa inda wayana yake jone a caji na ciro cikin sauri na kira layin ,
Sheriff tsayin wani lokaci naji shiru, sai can daga bisani naji computer tana gaya min wayar a kashe take,,
A rude na nemi layin Amal, itama hakan ne ta kashe wayar ta,
Sai dabaran kiran Salimat yazo min,
Ina samun ta ta dauka,nan na shiga, fada ma Salimat cewa tazo ba lafiya,
Hankalina a tashe nake maganar , hakan yasa tace min gata tafe,
Kafintazo saita bugowa maman Umar waya tasheda mata cewa tazo dakina da sauri ta diba mata halin da nake ciki,
Maman Umar tasamay ni na dan rakube a bakin gado ina kuka,
Ban boyewa maman Umar komai ba tun abinda Aziza tai min safiyan jiya,
Har zuwa cikin dare dakuma yadda mukayi yanzu da ita,
Salimat tafado dakin a rude nafada mata duk yadda na kwana a dakin da kuma abinda mukayi da ita yanzu
Saida ta nisa sosai can tace min shawar guda zan baki fadima,
Tace min ina passport dina nafada mata cewa yana nan,
Ita ta shirya min duk yadda komai zai kasance gare ni,
Tasa maman Umar ta kwaso min duk wani abin bukatana adakin dakuma wasu kudi masu yawa da naita boyon su da dadewa,
Salimat ta kwashe kayan zuwa gidan ta batare da sanin kowa ba,
Ta yadda ko CCTV ba za a gane cewa kaya ta dauka ba,
Duk wani motsin da za a yi a wanan yini a tsorace muke nida su salimat da maman umar don ko ruwan gidan nadaina sha yanzu,
Azizako sai fita takeyi tana dawo tare da wata yar doguwar takari fara wace tayi bleaching duk ta kode,
Ranan dole tare muka kwana da maman Umar adaki daya,
Washegari tun da safe nai shirin zuwa makaranta, saboda kasancewar itace ranan da zan rubuta jerabawar karshe,
Ina kallon Ummi cikin tausayawa saboda har yanzu jikinta baida wani karfi sosai,
Amal tana ta jana da hira saidai sama sama naje dan ansa mata,
Can dai tace min wai may yasamay ni ne yau taga duk bani cikin hayacina sosai,
Nadan kakaro murmushin dole nace haba Amal yaune fa zan gama exam dina aiko kinga dole in dan damu,
Dazamu tafi naba maman umar takarda nace taba sheriff idan yadawo kasan ,
Ina gama exam ko min ti biyu bamu karaba muka dauki shatan taxi nida salimat sai jedda,
Ina rugumay da Aisha wace mamata ta ce min in wuce da ita duk inda zani tabar min ita,
Batare da bata lokaci ba akai muna screening duk na ka gu inga mun shiga jirgi
Ina jin anfara kiran yan jirgin mu sai kuma kuma al,amarin ya juye min duk naji ba dadi, a raina,
Saboda nasan cewa Ummi bazata ji dadin abinda nayi ba,
To amma yaya zanyi dole ne in tserar da rayuwana ,
Karfe tara na dare jirgin mu yatashi daga jidda zuwa Nigeria,,,,,,
Chapter 98 · 0% Book details