Sashe 111
Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shigar safiya su kaiwa garin kano su biyu ne a tafiyar tasu Khalid bai samu biyo su ba, kamar yadda yaso, sai Al, mustapha da ke tare da Sheriff din shi akoda yau she, Tafiyan su ta zanto tamkar kamar ta official ne, don jirgin ba wai wasu passenger ya kwaso ba masu yawa, Daga Riyadh Abuja jirgin ya sauka, bayan duk wani bincike da ya dace ai masu angabatar Motocin company su Ahmad ne har guda hudu Suka zo don taron su inda aka lodawa hilux kaya masu yawa a bayan ta, Sai a lokacin doctor kamal yaga irin kayan da Ahmad ya jibgo don tafiyan, Cikin mamaki ya juya inda Ahmad din ke tsaye yana kokarin bude kofar mota, Bayan sun zauna ne Doctor yace wanan uban kayan fa da ka dauko, Murnushi yayi lokacin yana kokarin ciro wata yar karamar system din shi new model don binciken wani karfe, Yace wa Doctor duk kayan fadima ce Doctor, Cikin yar zarar idon mamaki yake kallon shi, Shiko cikin ko in kula yace yes Da da farko ba,a gaban iiyayen ta, na nemi auren ta ba duk wani abin da yakamata ai wa fadima ban mata ba, Wancan lokaci kasani kai aure ne kawai na wani manufa, But yanzu ko ta riga ta zama wani sashe na jiki fiye da yadda nake tsamani, Shiyasa zan tafi mata da wanan kayan a matsayin lefen ta, a gurin iyayen ta na aini fi, Don su ma in basu hakkin su tare da hakkuri, da duk wani kuskure da aka tafka alokacin na rashin bidan yardan su, Murmushi doctor yai mai don gane hikimar yin hakan Yana son Ahmad wurin bawa kowa hakkin shi komai kan,kanta abu Yace wanan kuma fa gaskiya ne Ahmad, hakan nada wani fa,ida so sai, Musan man ga mutanen mu hausawa da suka maida kayan lefe kamar wani sunna babba, Zakaga koda yaro baida halin su kamar dole sai ya nemo su ya kai gidan yarinya, Wasu ma don jahilci har rainawa sukeyi, agaban yan uwan yaro,,, Sannu a hannkali motocin ke tafiya a bissa titin cikin garin Abuja,, Saidai yar go,slow da suka samu a hanyar don gurin yadan cike da abin hawa, Doctor kamal sai yaba garin Abuja yake yi, ga irin girman da takara acikin yan shekarun nan, A zuciyar shi yana fadin cewa a gaskiya gwainatocin Nigeria suna iya keep karin su dosai wurin inganta rayuwar al,uman su, Babu gwaunatin da zata hau mulki da baita wanin abin ci gabar al,uma ba akasar Duk wacce ta hau sai tayi iya kokarinta ga jama,ar ta, Suna tafe suna hirar su, Ahmad na fada mai cewa shima yana son yabar kasar saudiya yadawo kasarsa da zama, Saida har yanzu gwaunatin saudiya sun ko sake shi , Koda yaushe kokari kara mai ci gaba sukeyi a gurin aikin shi. Ta yadda ba zaiyi tuna nen dawowa kasar shi ba, saboda amfanar da sukeyi dashi, Maitama suka ga an rubuta baro, baro a titin shiga layin uguwar, Agaban wani kyakyawan gida suka tsaya, inda mai gadin kofar gidan ya wagale get motacin suka shige ciki gaba dayan su Gidan Ahmad na maitama, ke nan, wanda bai ko tare a cikin sa ba, Sabone shiya gina abin shi tun lokacin da yafara aiki a kasar yai tunanen yin wannan ginan don gaba, Don ita Nafisa tana zaune A so Rock, a gidan shi da company su na nan Nigeria ta gina mai , Don haka a can maitama ya yanke shawar sauke doctor, Saboda Doctor ya huta yasa su zuwa maitama direct, Doctor kamal yayi mamaki kwarai da wanan katafaren gidan da Ahmad yagida a kasar shi ta haihuwa, Saidai mamakin nasa ba wani mai tsawo bane saboda sanin da yai,wa Ahmad din , Akan irin kudin da yake samu a kowani wata, daga guraren aikin shi da kuma masana,artan su ta Abu Abdallah, dake Dubai, Dan ma Ahmad din ya kasance mutum mai son taimakawa addinin sa , Yana yawan taimakawa kasa shen musulumai baka ken fata da tallafi, da kaso nai tsoka daga cikin dukiyar shi akoda yaushe,,,, Sun samu Bashir ya aiwatar da komai da yakamata don taron baki a gidan, Saida ya tabbatar da cewa, doctor yasamu natsuwa daga gajiyar da suka kwaso ne,, Sai yai mai sallama da niyar wucewa gidan shi da nafisa take zaune a ciki, Al, mustapha ya bar mai, don kauda shiru agidan shima kuma mustapha din agajiye yake a lokacin, Sam nafisa bata da masaniyar cewa Ahmad zai zo yau saboda ta san cewa yafi shigowa karshen wata, duk da bawai ko wani wata bane yake samun shigowa Nigeria din,, Duk da rashin shigowar shi time to time bai sa tadamu da rashin zuwan na shi ba, Ita dai gurin ta ta zauna a matsayin matar shi a rayuwar ta don gani take yi kamar babu sauran namijin da yakai Ahmad din ta komai yanzu, Don haka tasa wa ran ta yin hakkuri da zama dashi ko ta yayane, zata iya jurewa da shi din, Don haka babu wani tanadin da tai mai na shirin zuwan nashi Kamar yadda ya kamata duk wata, mace ta tarbi mijin ta a duk lokacin da zai ziyar ce ta,,,,, Nafisat ta canza halinta so sai yanzu ba kamar da ba , duk wani shaye shaye ta daina shi yanzu, Zaune take a cikin tanga may,may falon ta tana waya yar aikin ta na gefe guda ta na dan goge gogen kayan cikin falon, Duk da safiya ne yanzu, bai hana nafisa ta tsara kwaliyar ta ba tankar wace mijinta ke a gari, zaune,,, Da sallamar shi ya shigo cikin falon nasu, duk da gidan shi ne, amma shi akidar shi ce yashigo da sallama, Ganin da taimai girshi sai da gabanta ya fadi, cikin nuna yar faduwar gaba tace Ahmad , A yar razane ta mike tsaye daga zaunen da take, Tana mai sannu da zuwa cikin mamaki, Inda take yadan nufa yadan sunbaci tsakiyar goshinta kamar yadda larabawa kewa matan su ko diyan su, Kaine tafe babu ko sanarwa, batare da ya dakata ba ko ya dan tsaya ya wuce kai tsaye zuwa hawan stairs , Binshi tayi da kallo tace a zuciyar badai, miskilanci ba Ahmad, Itama saman ta haura tabi bayan shi, Koda ta shiga dakin ta samay shi yana cire botton din rigar shi, Zuwa tayi don taimaka mai cikin kissa irin ta yan duniyar mata, Duk da yagane nufin ta hankalinshi bai wani daga ba ga duk wani kisi,sinanar da take ai,watar wa, Kara tanbayar shi tayi ko lafiya ya shigo batare da fada mata ba, zai shigo ba Jaye taye daga gaban shi kadan, ya nufi hanyar bayi, Daidai kofar shiga toilet yace mata, batafiyan ki nayo ba shi yasa ban sanar da ke ina hanya ba, yashige bayi abinshi,, Ta yar murmushi kamar ta mugunta tace aiko nice mai tafiyar ba aiki ba, Bayan yafito ne ya shirya ta kara shigowa dakin cikin kwalliyar da yafi nadazu, kyau, Abin breakfast ta gabatar mai duk da ya danci wani a abu acan gidan da suka fara sauka da doctor Hakan bai hanashi karban tayin da tai mai ba na abincin don ya fitar mata da hakkin ta, Kasa stair ya sauko don ya ci abincin, yafara cin abincin da ta sa aka shirya mai a saman dinnig, a hankali saboda sam bai jin cin komai a halin yanzu, Kunun cookeroth yadan kurba, kadan sai wayar shi tai kara alamar kira, Bashir ne a layin inda Sheriff ke sheda mai cewa ai ya iso ko tun dazu kuma yana gidan nafisat, Aiki ne yataso maku haka ba shiri kashigo a gagauce, Nafisat ta kara tambayar shi a karo na biyu, Kai tsaye yace mata a,a aikin kaina ne wanan karon, Mata, ta ce nabiyu , shiyasa kika gan ni a wanan lokacin, Duk da maganar yadan daki zuciyar ta amma sai ta daure don kawai alkawarin da ta daukar wa iyayen ta, Tai dan murmushi tace Aziza ce sai ka biyo ta har nan wacce ba wani zama takeyi ba a kasar da har zai sa ka biyo ta, Daidai lokacin da yake mikewa tsaye yace Aziza kuma, Ai Aziza ba sai na biyo ta har Nigeria ba tunda ba,a nan take zama ba, Kafin wanin su yai wani magana ne Bashir ya shigo falon cikin sallamar shi, Dan rugumay juna sukayi bayan misa bi,ar da sukayi, Bayan gaisuwa da kuma tambayar sauran jama,a Sai suka zauna a lokacin Ahmad ke cewa Bashir to ya mutumin da zai gwada muna hanyar garin ya shirya tafiyan ko, Sai a lokacin nafisa da ke tsaye ta sandare cikin mamakin maganar da Ahmad ya fada mata, tun dazu, Tadan gyara zaman ta don jin zancen takeyi kamar ta almara har yanzu, Bashir yace a gaskiya ba karamin kokari yarinyar nan tayi ba, da ta kamo hanya ita kadai tun daga saudiya har wanan gari da akace yana da nisa sosai, Ahmad yadan yi, ajiyar zuciya ,cikin muryan tausayi,yace ba komai ke kara tayar min da hankali ba kamar cikin da ke ajikinta, Bashir, Banason ace min wani abu yasamu cikin nan don duk wani hope nawa a yanzu bai wuce kawai inga ance min an haifi abinda ke cikin cikin nan ba, Ido waje Nafisa ta kara kallon shi , Ta mai,maita a zuciyar ta tace ciki fa, Wace matar tashi keda ciki wacce ban sani ba, Kai wanan dai kila matar wani ne can suke zance, Shiko bai ko san cewa tanayi ba ma, Don haka cigaba ya yi kawai da zancen shi, batare da yako kula da wani zaran ido da nafisat keyi ba, Bashir ne yadan kulada halinda take ciki a lokacin don haka ce mata yayi, Kina mamaki ne ke ma ko Nafisa, a ce mace ta baro saudiya da ciki zuwa nan kasar aiba gaskiya bane koma dai may ne ai zata bari har ta haihu ai ko, Nafisa tai karfin halin bashi ansa tace watakila wani abin ne yabata mata rai har yasa ta tafiya mai nisa haka,, Ahmad yace ma bashir cikin murmushi You know she is still young, Bawai wata babba ba ce, barazanar Aziza ce yasa ta firgicewa a lokacin,