← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 139

Sashe 72

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

Washegari muka wayi gari da babban bakuwa, Aziza ce tazo daga Dubai don ita yanzu can tafi zama, da tana zuwa Nigeria kaida kai amma yanzu ta daina,
Zuwan ta yasa nadan saki jikina kadan wai ni ina gudun tagane abin da yafaru ni da mijinta,.
Sai har yanzu ban iya hada idona sam da sheriff saboda wani irin mugun kunyar shi da nauyin shi nake ji sosai walahi
Da ina da dama dana koma madina in karasa hutuna acan don zaifi min
Shiko ina lura da shi da munda hada ido ko nai wani dan motsi sai yadan wani lunshi idon shi,
Don hakane ma na koma daki abina ban kara fitowa ba,
Photo da Amal ta turo mai ne ya dauka yake nunawa Aziza yana mata bayani akan photo,
Saida ta kalli photo tsab sai wani tunane da tadade tanayi ba mafita yafado mata a rai
Cikin wani irin yanayi ta dan gyara zaman ta don taji dadin yin nazari akai

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
6⃣6⃣
*BY*
🐎 *ZAINAB *IDRIS**MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP 🐎

Almost true life story,,,,
Chapter 72 · 0% Book details