← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 139

Sashe 79

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jirgin safiya muka biyo zuwa saudiya a,Riyadh muka sauka sai muka karasa garin makka kafin ayi sallah azuhur duk muna cikin garin makkah,
Dakina na wuce don indan huta saidai kuma zuciya na fam yake da zunlumi da tunanen abinda ke gabana,
Gashi kuma maganar siri ne ba bu damar in fada ma wani,
Duk da basan ko ya maganar dashen ciki yake ba nasan cewa abune mai girma,
Saidai inda nake jin saukin al,amarin shine kawai in ance indan yafara girma za,a cire ne amayar mata da abinta a cikin cikin ta
Wanan abin zan yi shine kawai don sheriff din mu mutun mai mutunci da sanin yakamata,
Koma maye ai dolene in sadakar da rayuwa na agare shi don in,taimaka mai kamar yadda shima din yataimaki rayuwa na ta fan,ni daban daban,
Tunda muka dawo daga wanan tafiyan Amal tagane cewa ina cikin damuwa, sosai tunda ba haka tasan nake ba,
Tunda ta tambaye ni nace mata ba komai tun lokacin tasan cewa bazata gane komai ba kawai ido tasa min,,,
Ita ko Aziza ba abinda ya damay sai farinciki kawai takeyi da an,nashuwar ta,
Aziza taima sheriff bayani cewa likitan ta yace nanda dn wani lokaci yanason ta koma tare dashi don zai dan gwada wani fasaha akasu tayadda ciki zai zauna mata,
Cikkn rashin yarda da maganar ta yace Aziza na fada maki cewa bani bukatar wanan plan din naki pls,
Nabarwa Allah al,amari na idan Allah yatashi bani haihuwa basai natafi wata uwar duniya ne ma har inda nake zaibani
Kisani cewa rabon mutun bai wuce shi, idan kikayi imani da tawakkali sai ubangiji maji rokon bawan shine sai ya karba muna addu,an mu,,,
Kuka tasa mai , maitsuma rai yadda yakasa daurewa har yabar mata dakin
Yafito waje,
Ga mamakin shi sai ga alamar innuwar mutun a cikin duhun daren,
A hankali yanufi gurin da ganin kowaye wajen zaune,,, fadima ce zaune cikin wanan duhun ta hada kafa da gwaiwa da alamar akwai abinda ke damun ta,
A hankali ya furta sunan ta cikin mamaki,
Sai na dago kaina nimadai din cikin mamakin may yafito da shi cikin wanan lokacin haka,
Tambaya yawatso min a gagauce, lafiya, may kikeyi haka anan cikin wanan lokacin,
Bakomai na iya furtawa, cikin dan karamin,sautin,
Gefen guda yasamu yadan zauna gab da inda nake,
Yadan kura min ido na dan wani lokaci,,
Can yace fadima har yanzu kina akan tunanen yan uwanki ne da suka tafi, kokuwa da akwai wani abinda ke damun ki ne azuciyan ki,,
Maimakon inyi magana sai kawai nadan girgiza mai kai alamar a,a,.
Kamar mai rada ya ce fadima baki da wanda yafini duk cikin fadin kasar nan,
Amma ace kina cikin wani hali nadamuwa wanda har zai hanaki sukuni da samun barcin
Duk ki fada min to waye kike da shi bayan ni da zaki fadamawa,
Ban kara cewa komai ba kawai dai sai nai shiru saboda nasan cewa duk tsananin tambaya bazan taba fada mai komay ke damuna ba,
Saboda alkawarin da na dauka na boye wanan babban sirin ga kowa,
Sai bayan raina, ba mai jin cewa ai nice nataimakawa sheriff,
Shima dai din shirun yayi har takai kamar babu kowa agurin saboda shirun da ya ratsa gurin,
Duk sai yaji ba dadi acikkn zuciyar shi, saboda yasan cewa lalai akwai abinda ke damun wanan yarinyar sai zurfin ciki irin nata bai bari ta fadi, komadai may ye zai kokari yasa mata ido sosai ,a,al,amuranta
Wata ajiyar zuciya ya sauke da karfi gamida fesar da wata iska irin ta dan relief din nan,
Yakara daga ido ya kalle ta sai wani irin tausayinta ya kamashi yasan cewa tana kokari dole ta shiga cikin irin wanan yanayin,
Narashin kowa nata kusa da ita hatta wace takawo ta kasar ta wuce tabarta,
A,hankali ya dan matso gab da inda nake zaune dan kalleni cikin tausayi,
Ya sa hannun shi yakamo hannu na yadan matse cikin nashi,
A raunane yace min kiyi hakkuri fadima da zanran kin gama karatun ki nida kaina zai kai har gaban iyayenki insha Allah,
Yakara matse hannu na acikin nashi yace min tashi kije ki kwanta ki dan huta zan san abinda zan yi ,
Kala ban ce ba na mike da niyar in wuce saidai kuma hannu na na rike a cikin nashi,
Shima dai din tasowa yayi a hankali ya zo gab dani yadan matse ni a kirji shi tayadda har ina iya jin yadda zuciyar shi ke bugawa,
Cikin sauri nayi kokarin kwace kaina daga jikin nashi, amma ina yarike ni gam,
Saida yai ra,ayim kanshi nasamu yasake ni
Tunda yasaakeni ban ko kara waigawa ba nai ciki da sauri, ina maida nunfashina ahankali,
Nadade barci bai dauke ni ba tu nen sabon salon da sheriff ya bullo min da shi nason ko yaushe ya hada jikina da nashi nakeyi,

Hakana nakwana cikin wanan damuwar gari nawaye nasamu maman Umar wace yanzu take min kamar yar uwata jini,
Data saura min cikin fadin saudiya saiko salimat da ke tare dani,
Ban inya boye mata komai ba tana wankin kayan su umar a laundry saida ta matse kayan takuma gama jin bayani na
Saita zauna a dayan kujeran da nake zaune gefe ta dan kamo hannu na ta kalli kwayar idona tace min
Fadima kin dai fi kowa sanin cewa sheriff ba mutumin banza bane balle mu tuhumay shi
Don idan sani ne na dokokin Allah ke ma kinsan cewa yasan komai fiye da sanin mu,
Don haka wani zargi bai ko taso ba a tsakanin ku,
Tace kawai ni abinda na fahinta yana maki hakane don daukar ki dayayi kanar yar kaunar shi,
Kinko ga dole ne ki dinga gani irin haka ,saboda haka kada ko kisa wani zargi a tsakanin ku dashi,,,.
Wanan maganar na maman Umar yasa nadan ji sanyi araina nafitar da duk wani zargin sabon canjin da nagani ga sheriff din,
Hutun mu ya kusa karewa ga kuma shirin tafiyan da Aziza keyi dani zuwa gurin dashen cikin da za ai min na aje mata baby ta da zanyi,
Nasan cewa dole Ina kallo Amal da salim za su wuce madina don cigaba da karatun mu wanda daga wanan hutun insha Allah mun gama karatun mu ke nan,
Saura kamar sati biyu mu koma wurin doctor aziza a kasar indiya su Amal suka koma madina
Wanda sam sheriff baiso ace sun tafi sun barni ba saboda da yasan cewa yanzune zamu karatun mu na karshe,
Amal sun wuce da kwana biyu Hindu ta bugowa Aziza waya cewa su hadu Nigeria saboda wasu kaya da sukayo oda akasar chaina ance jirgi ya nutse dawa su don haka dole ne suje su ganewa idon su abinda ke faruwa,
Bada son ranta tabar kasar saudiya zuwa Nigeria da niyar bazata dade ba saboda tafiyan da zamuyi,,,
Tun da marancen ranan nake jin jikina bana jin dadin shi sam ga kuma gidan duk kusan kowa ya watse gidan yai min girma,
Don hakane saina dan koma dakina na kwanta daniyar kila indan nasamu barci na tashi zandan ji damar jikin nawa,
Mun muna mafarkin danayi yssa na farka inata zufa a goshina, duk da na farka daga barcin ina iya tuna mafarkin
Maciji nagani a cikin daki na yavkokarin shige min ajikina,
Naje in gudu sai kuma na kara gani gida ya nufoni gadan gadan ya shige min a jiki,
Innalillahi kawai nake iya furtawa a bakina ban iya koda daga hannu na don jiki na duk naji ba karfi,
Daidai lokacin naji takon kafar sheriff zuwa dakina,
Don nasan cewa in bashi ba wanda ya isa yatako har inda nake,
Da sallama ya shigo dakin saidai a kwance yagan ni da alamar ba lafiya tare dani ,
Da sauri yakaraso inda nake kwance ya na tambayar ko may yasamay ni ,
Baki na bude da niyar in mai magana sai naji ban iyawa,
Sai hawaye da suka dan biyo kumci na
Tabayana yakeyi arude baki da lafiya ne na kada mai kai almar ,a,a
Sai ya lura cewa na dafe kaina
Yakoma da sauri yadoko man magani yabani,na samu nasha
A hankali ya hawo gadon yadan rugumoni ajikin shi yana min addu,a sai nayi wani irin ajiyar zuciya ,
Na lunshe idona ina ji ina shakar kamshin turaen shi tun ina danjin karan A C har barci yadaukeni
Tundaga lokacin ban kara sanin inda nake ba,
Dasafe koda natashi sai kawai nakamajin jikina ba karfi ko ina nawa ciwo yake mun,
Na koma ko tashi da kyat nake iyawa don nauyin da nakeji ajikina,
Acikin wanan halin har azizata dawo tasa may ni a hakan ,
Saboda son ranta duk da taga banda lafiya saida ta tafi da ni wanan tafiyar hakana,
Sau kin abin tare da sheriff muka tafi yana ta faman nan nan da ni,
Ranan da mukaje washe gari duk muna office din likita da su inda lita naga yakaini su wani daki su biyu,
Bayan sunfitone aziza tace ma liktia ya dibani banda lafiya,
Saita ja sheriffs da hira akan harkan maikatar su,
Ina shiga likita yace in kwanta awin farko naji yace in tashi da sauri gabana ya fadi,
Sainaji yace min infita kawai basai yadibani ba zai dai bani magani,
Shiko sheriff tunda na shiga hankalinshi na gurin mu yanayi yana kallon hanyar office din doctor saigani nafito,
Tana gani na fito ta mike tsaye,,,,,,,,,,
🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
6⃣9⃣
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story
Chapter 79 · 0% Book details